Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • Yaya Ake Rubuta da Fassara Littattafanmu?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
    • DARASI NA 23

      Yaya Ake Rubuta da Fassara Littattafanmu?

      Wani da ke aiki a Sashen Rubuce-Rubuce, a Amirka

      Sashen Rubuce-Rubuce, a Amirka

      Rukunin mafassara a Koriya ta Kudu

      Koriya ta Kudu

      Wani mutumi ɗan Armeniya yana riƙe da littafin da Shaidun Jehobah suka fassara

      Armeniya

      Wata yarinya ’yar Burundi tana riƙe da littafin da Shaidun Jehobah suka fassara

      Burundi

      Wata mata a ƙasar Sri Lanka tana riƙe da mujallun da Shaidun Jehobah suka fassara

      Sri Lanka

      Muna buga littattafai a harsuna wajen 750, kuma muna ƙoƙartawa mu yi wa’azin “bishara” ga ‘kowane irin mutum da ƙabila da harshe da al’umma.’ (Ru’ya ta Yohanna 14:6) Ta yaya muke cim ma wannan gagarumin aikin? Muna yin hakan ne da taimakon wasu marubuta da ke faɗin duniya da kuma rukunin mafassara masu ƙwazo kuma Shaidun Jehobah ne dukansu.

      Ana rubutun ne ainihi a Turanci. Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ce take kula da Sashen Rubuce-Rubuce da ke hedkwatarmu. Wannan sashen ne ke kula da aikin marubutan da ke hedkwata da kuma wasu ofisoshin reshe. Marubutan da muke da su a wurare dabam-dabam ne ya sa muke rubuta batutuwan da suka shafi mutane daga al’adu dabam-dabam, don mutane a ko’ina su so karanta littattafanmu.

      Ana aika rubutun ga mafassara. Bayan an tabbatar da cewa abin da aka rubuta daidai ne, kuma an ba da izinin buga shi, sai a aika rubutun ta hanyar na’urar kwamfuta zuwa mafassara da ke faɗin duniya don su fassara ta, kuma su tabbatar da cewa fassarar ta yi daidai. Suna ƙoƙartawa su yi amfani da “kalmomin gaskiya” waɗanda za su bayyana ainihin abin da aka ce a Turanci zuwa harshensu.—Mai-Wa’azi 12:10.

      Na’urorin kwamfuta suna hanzarta aikin. Na’urar kwamfuta ba za ta yi aikin masu rubutu da mafassara ba. Amma, aikinsu zai fi sauri idan suka yi amfani da kwamfuta da kuma littattafan binciken da ke cikinta. Shaidun Jehobah sun tsara abin ake kira Multilanguage Electronic Publishing System (MEPS). Wannan fasaha ce da take iya ɗaukan rubutu a harsuna dabam-dabam tare da hotunan da ke cikinsu, sa’an nan ta haɗa su tare don a buga su.

      Me ya sa muke irin wannan yunƙurin, har ma a harsunan da ’yan dubbai ne kawai suke yin su? Muna yin hakan ne domin nufin Jehobah shi ne, “dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.”—1 Timotawus 2:3, 4.

      • Yaya ake rubuta littattafanmu?

      • Me ya sa muke fassara littattafanmu zuwa harsuna da yawa?

  • Yaya Muke Samun Kuɗin Gudanar da Ayyukanmu a Faɗin Duniya?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
    • DARASI NA 24

      Yaya Muke Samun Kuɗin Gudanar da Ayyukanmu a Faɗin Duniya?

      Wani yana ba da gudummawa da son rai
      Shaidun Jehobah suna yin wa’azi

      Nepal

      Waɗanda suka ba da kansu da yardar rai don taimaka a gina Majami’ar Mulki a Togo

      Togo

      Waɗanda suka ba da kansu da yardar rai suna hidima a ofishin reshe da ke Birtaniya

      Birtaniya

      A kowace shekara, ƙungiyarmu tana buga miliyoyin Littafi Mai Tsarki tare da littattafai, tana rarraba su ba tare da gaya wa mutane su biya kaza ba. Muna gina Majami’un Mulki da ofisoshin reshe kuma muna kula da su. Muna tallafa wa dubban masu hidima a Bethel da kuma masu wa’azi a ƙasashen waje, kuma muna kai kayan agaji sa’ad da bala’i ya auku. Saboda haka, kana iya tambaya, ‘Ta yaya ake samun kuɗaɗen yin waɗannan ayyukan?’

      Ba ma gaya wa mutane su ba da ushiri kuma ba ma yawo da faranti don karɓan baiko. Ko da yake muna kashe kuɗi sosai wajen gudanar da wa’azin da muke yi, ba ma roƙon kuɗi. Shekaru sama da ɗari da suka shige, fitowa ta biyu ta mujallar Hasumiyar Tsaro ta ce, mun gaskata cewa Jehobah ne yake tallafa wa aikinmu kuma ba za mu “taɓa roƙon mutane su ba mu tallafi ba.” Kuma ba mu taɓa yin hakan ba!—Matta 10:8.

      Ana tallafa wa aikinmu ne ta wajen ba da gudummawa da son rai. Mutane da yawa suna son yadda muke koyar da Littafi Mai Tsarki kuma suna bayar da gudummawa saboda hakan. Shaidun Jehobah suna amfani da lokacinsu da ƙuzari da kuɗinsu da sauransu, wajen yin nufin Allah a faɗin duniya, kuma suna yin hakan ne da farin ciki. (1 Labarbaru 29:9) Akwai akwatuna a Majami’ar Mulki da kuma wuraren manyan taronmu inda waɗanda suke son su ba da gudummawa suke iya saka gudummawarsu. Ƙari ga haka, ana iya ba da gudummawa ta dandalinmu na jw.org/ha. A yawancin lokaci, muna samun gudummawar kuɗin nan ne daga mutanen da ba su da abin hannu. Mutanen nan suna kama ne da gwauruwa talaka wadda Yesu ya yaba wa. Duk da cewa talaka ce, ta ba da gudummawa da zuciya ɗaya. (Luka 21:1-4) Saboda haka, kowane mutum zai iya yin “ajiya” domin ya ba da gudummawa ‘bisa yadda ya yi niyya a zuciyarsa.’—1 Korintiyawa 16:2; 2 Korintiyawa 9:7.

      Muna da tabbaci cewa Jehobah zai ci gaba da motsa mutanen da suke son su ‘girmama shi da wadatarsu,’ su tallafa wa aikin wa’azin Mulki domin nufinsa ya cika.—Misalai 3:9.

      • Mene ne ya bambanta ƙungiyarmu da sauran addinai?

      • Yaya ake amfani da gudummawar da mutane suka bayar da son rai?

  • Me Ya Sa Ake Gina Majami’un Mulki Kuma Yaya Ake Yin Ginin?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
    • DARASI NA 25

      Me Ya Sa Ake Gina Majami’un Mulki Kuma Yaya Ake Yin Ginin?

      Waɗanda suka ba da kansu da yardar rai don gina Majami’un Mulki a Bolivia

      Bolivia

      Wani Majami’ar Mulki a Nijeriya kafin a sake gina shi
      Wani Majami’ar Mulki a Nijeriya bayan an sake gina shi

      Nijeriya, kafin a gina da sa’ad da aka gina

      Wani filin gina Majami’ar Mulki a ƙasar Tahiti

      Tahiti

      Kamar yadda sunan nan Majami’ar Mulki ya nuna, ainihin cibiyar abin da ake koyarwa a wurin daga Littafi Mai Tsarki, shi ne, Mulkin Allah, kuma shi ne ainihin abin da Yesu ya koyar a duniya.—Luka 8:1.

      Cibiyoyi ne inda ake bauta ta gaskiya a yanki. Shaidun Jehobah suna tsara aikin da suke yi na wa’azi a Majami’ar Mulki da ke yankinsu. (Matta 24:14) Girma da fasalin Majami’un Mulki sukan bambanta, amma gini ne madaidaici inda ikilisiya guda ko sama da haka suke yin taro. Saboda ƙaruwar da ake samu na ikilisiyoyi da masu shela, a cikin ’yan shekarun nan, mun gina dubban sababbin Majami’un Mulki (wajen guda biyar a kowace rana). Ta yaya ake cim ma hakan?—Matta 19:26.

      An gina su ne da gudummawar da mutane suka ba da don gina Majami’un Mulki. Ana tura gudummawar nan ta kuɗi zuwa ofishin reshe don ya ba ikilisiyoyin da suke son su gina ko su gyara Majami’ar Mulki.

      Masu ginin suna yin sa ne da son rai ba tare da an biya su ko sisi ba kuma mutane ne daga wurare dabam-dabam. A ƙasashe da yawa, akwai Rukunin Masu Gina Majami’ar Mulki. Wannan rukunin na magina tare da ’yan’uwan da suke taimaka musu suna zuwa ikilisiyoyi dabam-dabam a birane da ƙauyuka a ƙasar da suke hidima, don su taimaka wa ikilisiyoyi wajen gina sababbin Majami’un Mulki. A wasu ƙasashe, an zaɓi Shaidun da suka ƙware don su riƙa duba ayyukan gina da kuma gyara Majami’un Mulki da ke yankin da aka ba su. Ko da yake ƙwararrun magina daga yankin suna ba da kansu, yawancin masu aikin ’yan ikilisiyar da ake yi wa ginin ne. Ruhun Jehobah da kuma ƙoƙarin da mutanensa suke yi da zuciya ɗaya ne ya sa hakan ya yiwu.—Zabura 127:1; Kolosiyawa 3:23.

      • Me ya sa ake kiran wuraren da muke ibada Majami’ar Mulki?

      • Yaya ake gina Majami’un Mulki a faɗin duniya?

Littattafan Hausa (1987-2026)
Fita
Shiga Ciki
  • Hausa
  • Raba
  • Wadda ka fi so
  • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
  • Ka'idojin Amfani
  • Tsarin Tsare Sirri
  • Saitin Tsare Sirri
  • JW.ORG
  • Shiga Ciki
Raba