Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • Fushi Ya Jawo Kisan Kai
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
    • Kayinu ya yi fushi sa’ad da Habila ya mika hadaya ga Jehobah

      DARASI NA 4

      Kayinu Ya Kashe Habila

      Adamu da Hauwa’u sun haifi yara da yawa bayan da aka kore su daga lambun Adnin. Kayinu ne yaronsu na farko, kuma shi manomi ne. Na biyun kuma mai suna Habila, yana kiwon dabbobi.

      Wata rana sai Kayinu da Habila suka yi wa Jehobah hadaya. Ka san abin da hadaya take nufi? Wata irin kyauta ce da ake ba Allah. Jehobah ya karɓi hadayar Habila amma bai karɓi na Kayinu ba. Sai Kayinu ya yi fushi sosai. Jehobah ya ja kunnen Kayinu kuma ya gaya masa cewa idan bai bar fushin nan ba, zai yi wani abin da ba kyau. Amma Kayinu bai ji ba.

      Maimakon haka, ya gaya wa Habila: ‘Ka zo mu je gona tare.’ Da suka je gonar kuma Kayinu ya ga ba kowa a wurin, sai ya kashe ƙaninsa Habila. Mene ne Jehobah ya yi? Jehobah ya hukunta Kayinu, kuma ya kore shi zuwa wani wuri mai nisa. Bai yarda Kayinu ya sake dawowa wurin ’yan’uwansa ba.

      Kayinu ya zo wurin Habila a gona

      Wane darasi ne za mu iya koya daga wannan labarin? Za mu iya yin fushi idan ba a yi mana abubuwan da muke so ba. Idan mun ga cewa mun soma yin fushi ko kuma idan wasu sun ga muna fushi kuma suka gaya mana mu daina, zai yi kyau mu daina fushin don kada mu yi laifi.

      Da yake Habila ya ƙaunaci Jehobah kuma ya yi abin da yake da kyau, Jehobah ba zai taɓa mantawa da shi ba. Allah zai tayar da Habila a lokacin da aka mayar da duniya aljanna.

      ‘Ka je ku shirya da ɗan’uwanka, sa’an nan ka zo ka miƙa hadayarka.’​—Matta 5:24

      Tambayoyi: Su waye ne yara biyu da Adamu da Hauwa’u suka fara haifa? Me ya sa Kayinu ya kashe ɗan’uwansa?

      Farawa 4:​1-12; Ibraniyawa 11:4; 1 Yohanna 3:​11, 12

  • Jirgin Nuhu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
    • Nuhu da iyalinsa sun gina jirgi

      DARASI NA 5

      Jirgin Nuhu

      A kwana a tashi, sai mutane suka soma yawa a duniya. Amma yawancinsu ba sa yin abu mai kyau. Har da wasu mala’iku ma da ke sama. Sun sauko daga sama zuwa duniya. Ka san dalilin da ya sa suka yi hakan? Domin su sami jiki irin na mutane kuma su auri mata.

      Matan da mala’ikun suka aura sun haifi yara. Waɗannan yaran sun yi girma sosai kuma suka zama mugaye. Jehobah bai bari su ci gaba da yin mugunta ba. Ya ce zai halaka su da ambaliyar ruwa.

      Nuhu da iyalinsa sun gina jirgi kuma suna shirya abinci

      Amma akwai wani mutum da ba ya mugunta. Yana ƙaunar Jehobah sosai. Sunansa Nuhu. Shi da matarsa suna da yara uku. Sunayensu Shem da Ham da Japheth kuma dukansu sun yi aure. Jehobah ya gaya wa Nuhu cewa ya gina babban jirgin ruwa da ke kama da akwati da za su zauna a ciki don kada su mutu. Jehobah ya kuma gaya wa Nuhu cewa ya shigar da dabbobi da yawa cikin jirgin don kada su mutu.

      Nan da nan sai Nuhu ya soma gina jirgin. Sun yi shekara hamsin kafin su gama aikin. Sun gina jirgin yadda Jehobah ya gaya musu. A lokacin, Nuhu ya gaya wa mutanen cewa Jehobah zai halaka su da ruwa idan ba su daina yin mugunta ba. Amma ba su ji ba.

      Sa’ad da lokaci ya kai, sai Nuhu da iyalinsa suka shiga cikin jirgin. Bari mu ji abin da ya faru bayan haka.

      “Kamar yadda aka yi a zamanin Nuhu, haka dawowar Ɗan Mutum za ta zama.”​—Matta 24:​37, Littafi Mai Tsarki

      Tambayoyi: Me ya sa Jehobah ya ce zai halaka mugaye da ambaliyar ruwa? Mene ne Jehobah ya ce Nuhu ya yi?

      Farawa 6:​1-22; Matta 24:​37-41; 2 Bitrus 2:5; Yahuda 6

Littattafan Hausa (1987-2025)
Fita
Shiga Ciki
  • Hausa
  • Raba
  • Wadda ka fi so
  • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
  • Ka'idojin Amfani
  • Tsarin Tsare Sirri
  • Saitin Tsare Sirri
  • JW.ORG
  • Shiga Ciki
Raba