WAƘA TA 112
Jehobah Allah Ne Na Salama
Hoto
(Filibiyawa 4:9)
1. Jehobah, Allahnmu,
Allah na salama ne.
Muna so mu kasance da
Halayen da kake so.
Kai ka ba mu gata
Mu zama aminanka,
Domin mun ba da gaskiya
Ga ƙaunataccen Ɗanka.
2. Kana amfani da
Ruhunka da Kalmarka
Don ka kāre mutanenka
A cikin duniyar nan.
Kafin lokacin da
Za a daina yin yaƙi.
Bari ruhunka mai tsarki
Ya sa mu yi salama.
3. Kana da al’umma
A sama da duniya.
Ka shirya mu da ruhunka
Don mu shaida Mulkinka.
Mulkin da ka shirya
Zai share duk wahala.
Masu tawali’u kuma
Za su more salama.
(Ka kuma duba Zab. 4:8; Filib. 4:6, 7; 1 Tas. 5:23.)