Abubuwan Da Ke Kawo Farin Ciki A Iyali
Ku Koya wa Yaranku Tarbiyya
Loida,a wata mahaifiya a ƙasar Mexico, ta ce: “Ana ba da kwaroron roba a makaranta, saboda haka matasa suna tsammanin cewa yin jima’i ba laifi ne ba idan suka yi amfani da kwaroron roba.”
Nobu, wata mahaifiya a ƙasar Japan, ta ce: “Na tambayi ɗana abin da zai yi idan shi da budurwarsa suna tare su kaɗai. Amsarsa ita ce, ‘Ban sani ba.’”
SA’AD da ɗanku ko ɗiyarku take jariri, kun gyara gidanku yadda yaranku ba za su shiga haɗari ba? Wataƙila kun rufe wayoyin lantarki, kun ɓoye abubuwa masu kaifi, kuma kun kāre gefen matakalu, kun yi dukan waɗannan abubuwan ne don ku kāre ɗanku.
Da ma a ce kāre ɗanku matashi yana da sauƙi kamar haka! Yanzu damuwarku ta ƙaru, kuna tunanin: ‘Wa ya sani ko ɗana yana kallon hotunan batsa?’ ‘Ɗiyata tana aika hotunan batsa ta hanyar wayar selula, wato, hotunan inda take tsirara?’ Kuma wata tambaya mai sa fargaba ita ce, ‘Ɗana matashi ya soma sha’awar jima’i ne?’
Sa Ido ba Shi Ne Maganin Ba
Wasu iyaye suna sa wa yaransu ido daga safiya har dare don su san duk wani abin da suke yi. Daga baya, iyaye da yawa suna gane cewa irin wannan sa idon da suke yi yana ƙara sa yaronsu ya ƙware wajen ɓoye abin da yake yi.
A bayyane yake cewa sa ido ba zai magance matsalar ba. Jehobah Allah da kansa ba ya amfani da wannan dabarar don ya sa halittunsa su yi masa biyayya, ku ma iyaye bai kamata ku yi hakan ba. (Kubawar Shari’a 30:19) Saboda haka, ta yaya za ku iya taimaka wa yaranku matasa su yanke shawara mai kyau game da tarbiyya?—Misalai 27:11.
Mataki mafi muhimmanci shi ne ku riƙa tattaunawa da yaranku a kowane lokaci kuma ku soma tun suna ƙanana.b (Misalai 22:6) Bayan haka, sa’ad da suka shiga ƙuruciya, ku ci gaba da tattaunawa. A matsayin iyaye, daga bakinku ne ya kamata yaranku matasa su fara jin duk wani tabbataccen bayani. “Mutane da yawa suna tunanin cewa mun fi son mu tattauna da abokanmu game da jima’i, amma hakan ba gaskiya ba ne. Muna farin ciki sosai sa’ad da muka sami irin wannan bayanin daga iyayenmu. Mun san cewa ba za su ruɗe mu ba,” in ji Alicia, wata yarinya daga Biritaniya.
Abin da ya Sa Tarbiyya Take da Kyau
Yayin da suke girma, yara suna bukatar su san fiye da yadda ake ɗaukan ciki da haihuwa, suna bukatar ja-gora. Ya kamata ‘hankulansu ya kasance wasassu don raba nagarta da mugunta.’ (Ibraniyawa 5:14) A taƙaice, suna bukatar su kasance da imani mai ƙarfi a kan batun yin jima’i a hanyar da ta dace kuma su riƙe wannan imanin gam. Ta yaya za ku iya koya wa ɗanku matashi tarbiyya mai kyau?
Ku soma bincika taku tarbiyyar. Alal misali, wataƙila kun gaskata sosai cewa fasikanci, wato, jima’i tsakanin namiji da macen da ba su auri juna ba, zunubi ne. (1 Tasalonikawa 4:3) Wataƙila, yaranku sun san matsayinku a kan wannan batun; suna ma iya yin ƙaulin ayoyin Littafi Mai Tsarki da suke goyon bayan imaninku. Idan aka tambaye su, suna iya amsa cewa yin zina zunubi ne.
Amma suna bukatar fiye da haka. Littafin nan Sex Smart ya lura cewa wasu matasa suna iya cewa sun amince da imanin iyayensu game da jima’i. Littafin ya ce: “Ba su da gaba gaɗin kafa nasu ra’ayin. Amma sa’ad da suka faɗa wani yanayin da ba sa tsammani kuma nan da nan suka fuskanci matsalar ‘sanin halin da ya cancanta da wanda bai cancanta ba,’ sukan rikice gaba ɗaya.” Ainihin dalilin da ya sa kasancewa da tarbiyya yake da muhimmanci ke nan. Ta yaya za ku taimaka wa ɗanku matashi ya koye su?
Ku bayyana musu tarbiyyarku dalla-dalla. Kun yarda cewa waɗanda suka auri juna ne kawai ya kamata su yi jima’i? Sai ku gaya wa ɗanku matashi, ku bayyana masa dalla-dalla kuma a kai a kai. In ji littafin nan Beyond the Big Talk, bincike ya nuna cewa “a iyalan da iyaye suka gaya wa yaransu matasa dalla-dalla cewa ba su amince matasa su yi jima’i ba, a yawancin lokatai akwai alamun cewa yaran za su yi jinkirin soma jima’i.”
Hakika, kamar yadda aka ambata ɗazu, faɗin tarbiyyar da kuke so ba tabbaci ba ne cewa ɗanku ko ɗiyarku za ta yi amfani da su a rayuwarta. Amma, bayyana irin tarbiyyar da kuke son iyalinku ta kasance da ita dalla-dalla zai tanadar da ginshiƙin da yaranku za su gina nasu ɗabi’un a kai. Kuma bincike ya nuna cewa matasa da yawa suna bin tarbiyyar iyayensu daga baya ko da sun ƙi nuna hakan sa’ad da suke girma.
KU GWADA WANNAN: Ku yi amfani da labarin wani abin da ya faru don ku soma tattaunawa kuma ku bayyana musu tarbiyyarku. Alal misali, idan aka ba da rahoton yin jima’i ƙarfi da yaji da wata, kuna iya cewa: “Ina mugun ƙyamar yadda wasu maza suke ƙoƙarin cin zarafin mata. A ina ne kake tsammanin cewa suka koyi waɗannan halayen?”
Kada ku ɓoye musu komi game da jima’i. Gargaɗi yana da muhimmanci. (1 Korintiyawa 6:18; Yaƙub 1:14, 15) Amma, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa jima’i ainihin kyauta ce daga Allah, ba tarkon Shaiɗan ba. (Misalai 5:18, 19; Waƙar Waƙoƙi 1:2) Gaya wa yaranku matasa game da haɗarurrukan kaɗai zai iya sa su kasance da ra’ayin da bai dace ba wanda ya saɓa wa abin da Nassi ya ce game da batun. “Iyayena sun fi mai da hankali a kan haɗarin yin lalata, kuma hakan ya sa na kasance da ra’ayin da bai dace ba game da jima’i,” in ji Corrina, wata matashiya a Faransa.
Ku tabbata cewa ba ku ɓoye wa yaranku komi game da jima’i ba. Wata mahaifiya mai suna Nadia a ƙasar Mexico ta ce: “Abin da nake ƙoƙarin gaya wa yarana matasa a kowane lokaci shi ne cewa jima’i kyakkyawan abu ne kuma Jehobah ya ba ’yan Adam ne don su ji daɗinsa. Amma ya kamata a ji daɗinsa ne kawai a cikin aure. Zai iya sa mu farin ciki ko baƙin ciki, hakan ya dangana ne da yadda muka yi amfani da shi.”
KU GWADA WANNAN: Sa’ad da kuka sake tattauna da ɗanku matashi a nan gaba game da jima’i, ku kammala tattaunawar a hanya mai kyau. Kada ku ji tsoron nuna musu cewa jima’i wata kyauta ce mai tamani daga Allah wadda za su more a nan gaba sa’ad da suka yi aure. Ku tabbatar wa ɗanku matashi cewa zai iya manne wa mizanan Allah har wannan lokacin.
Ku taimaka wa ɗanku matashi ya yi tunani sosai a kan sakamakon. Don su tsai da shawarwari masu kyau a rayuwarsu, matasa suna bukatar sanin yadda za su bincika zaɓin da ke gabansu kuma su yi tunani sosai a kan amfani da illar kowane zaɓi. Kada ku yi tunanin cewa sanin da suke da shi na abin da ya dace da wanda bai dace ba ya isa kawai. “Idan na tuna kurakuren da na yi sa’ad da nake matashiya,” in ji Emma, wata Kirista a ƙasar Ostareliya, “zan iya cewa sanin mizanan Allah kawai ba ya nufin cewa ka amince da su. Yana da muhimmanci mutum ya fahimci amfanin waɗannan mizanan da kuma sakamakon karya su.”
Littafi Mai Tsarki zai iya taimakawa, domin dokoki da yawa da ke cikinsa sun nanata sakamakon yin zunubi. Alal misali, Misalai 5:8, 9 ta aririci samari su guji fasikanci “domin kada ka bada girmanka ga waɗansu.” Kamar yadda ayoyin nan suka nuna, yin zina zai shafi halinmu, zai hana mu zama cikakku a hidimarmu ga Jehobah, kuma zai zubar da mutuncinmu. Kuma hakan zai hana wanda ya yi zina ya ko ta ja hankalin duk wani ko wata da ke son ta yi aure kuma take da halaye masu kyau. Yin tunani a kan haɗarurruka na zahiri, na motsin rai, da kuma na ruhaniya da rashin biyayya ga dokokin Allah ke jawowa zai iya ƙarfafa ɗanku matashi ya ƙudurta yin rayuwar da ta jitu da dokokin.c
KU GWADA WANNAN: Ku yi amfani da kwatanci don ku taimaka wa ɗanku matashi ya ga amfanin bin mizanan Allah. Alal misali, kuna iya cewa: “Wutar murhu tana da kyau; gobara a daji ba ta da kyau. Mene ne bambancin su, kuma ta yaya amsarka ta yi daidai da iyakar da Allah ya kafa game da jima’i?” Ku yi amfani da bayanin da ke Misalai 5:3-14 don ku taimaka wa ɗanku matashi ya fahimci mugun sakamakon da ke tattare da zina.
Takao, wani matashi ɗan shekara 18 a ƙasar Japan, ya ce: “Na san cewa ina bukatar in yi abin da ke da kyau, amma ina yin gwagwarmaya a kullum da sha’awoyin jiki.” Matasan da suke jin haka su san cewa ba su kaɗai ne ke fuskantar hakan ba. Manzo Bulus wanda Kirista ne mai aminci sosai ya ce: “Ni da na ke nufi in aika nagarta, ga mugunta gareni.”—Romawa 7:21.
Yana da kyau matasa su san cewa yin irin wannan gwagwarmayar ba laifi ba ne. Hakan zai iya motsa su su tsai da shawara a kan irin halin da ya kamata su kasance da shi. Zai kuma iya taimaka musu su yi tunani a kan wannan tambayar, ‘Ina so in zama mamallakin rayuwana kuma mutane su san cewa ina da hali mai kyau da aminci, ko kuwa ina son a san ni a matsayin mai yin abin da kowa ke yi, wato, wanda yake barin sha’awoyinsa su sha kansa?’ Kasancewa da tarbiyya mai kyau zai taimaki ɗanku matashi ya amsa wannan tambayar cikin hikima.
[Hasiya]
a An canja wasu sunaye a wannan talifi.
b Don samun shawara game da yadda za ku iya soma tattaunawa da yaranku game da jima’i da yadda za ku san abin da ya kamata ku tattauna da su daidai da shekarunsu, ku duba Hasumiyar Tsaro, Janairu-Maris, 2011, shafi na 12 zuwa 14.
c Don ƙarin bayani, ka duba talifin nan “Young People Ask. . . Will Sex Improve Our Relationship?” a cikin Awake! na Afrilu 2010 na Turanci, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
KU TAMBAYI KANKU . . .
▪ Waɗanne tabbaci ne nake da su cewa ɗana matashi yana da tarbiyya mai kyau?
▪ Sa’ad da nake tattaunawa da ɗana matashi game da jima’i, ina kwatanta jima’i ne ainihi kamar kyauta daga Allah ko kuwa tarkon Shaiɗan?
[Akwati da ke shafi na 20]
Littafi Mai Tsarki Ja-gora ne Mai Kyau Tun Daɗewa har Zuwa Yau
“Umurnin da ke cikin Littafi Mai Tsarki game da jima’i ya kasance ja-gora mai kyau tun daɗewa har zuwa yau. A wannan zamanin da matasa da yawa suke girbe mugun sakamako na motsin rai na abubuwan da ke gaba: yin lalata tun suna yara, cikin shege, ƙanjamau da wasu cututtuka da ake samu ta hanyar jima’i, shawarar da ke cikin Nassosi wadda ta ce jima’i ya kasance tsakanin masu aure ne kaɗai . . . tana da muhimmanci sosai, shi ne kaɗai ‘jima’i marasa haɗari,’ kuma mai amfani.”—Parenting Teens With Love and Logic.