-
Rahab Ta Boye ʼYan Leken AsiriDarussa daga Littafi Mai Tsarki
-
-
DARASI NA 30
Rahab Ta Ɓoye ʼYan Leƙen Asiri
Sa’ad da wasu Isra’ilawa suka je leƙen asiri a birnin Yariko, sun sauka a gidan Rahab. Sai sarkin Yariko ya ji abin da ya faru kuma ya tura sojoji gidan Rahab. Da ganin haka, sai Rahab ta ɓoye mutanen biyu a rufin gidanta kuma ta ce wa sojojin su bi wata hanya. Ta ce wa ʼyan leƙen asirin: ‘Zan taimake ku domin na san cewa Jehobah yana goyon bayanku kuma za ku halaka birnin nan. Don Allah, ku yi mini alkawari cewa ba za ku halaka ni da kuma dangina ba.ʼ
ʼYan leƙen asirin suka ce wa Rahab: ‘Mun yi alkawari cewa ba za mu halaka duk wani mutumin da ke cikin gidanki ba. Ki ɗaure jar igiya a wundon gidanki kuma babu abin da zai sami danginki.’
Rahab ta ɗaure igiyar a wundon ɗakinta kuma ta sa mutanen suka sauka da igiyar. Sai suka je suka ɓoye a cikin duwatsu har tsawon kwana uku kafin suka koma gida. Bayan haka, Isra’ilawa suka tsallake Kogin Urdun kuma suka soma shirin halaka biranen. Birnin Yariko ne suka fara halakawa. Jehobah ya gaya musu cewa su zagaya birnin sau ɗaya kowace rana, har kwanaki shida. Amma a kwana na bakwai, sun zagaya sau bakwai. Sai firistocin suka busa ƙafoninsu kuma sojojin suka yi ihu sosai. Sai katangar birnin ta rushe. Amma gidan Rahab da ke katangar birnin bai rushe ba. Rahab da danginta sun tsira domin ta dogara ga Jehobah.
“Haka yake kuma da . . . Rahab a lokacin da ta ɓoye ’yan leƙen asirin ƙasar nan, ta kuma taimake su sun tsira ta wata hanya dabam. Ba ta wurin ayyuka ne ta zama marar laifi ba?”—Yaƙub 2:25
-
-
Joshua da GibeyonawaDarussa daga Littafi Mai Tsarki
-
-
DARASI NA 31
Joshua da Gibeyonawa
Labarin abin da ya same Yariko ya bazu a duk cikin ƙasar Kan’ana. Sarakunan sun haɗa baki domin su yaƙi Isra’ilawa. Amma sai Gibeyonawan suka kawo wata dabara dabam. Sun sanya tsofaffin kaya kuma suka je wurin Joshua, suka ce masa: ‘Daga wata ƙasa mai nisa muka fito. Mun ji labarin Jehobah da kuma dukan abubuwan da ya yi muku a ƙasar Masar da Mowab. Za mu zama bayinku idan kun yi mana alkawari cewa ba za ku kashe mu ba.’
Joshua ya yarda da su kuma ya ce ba zai kashe su ba. Amma bayan kwana uku, sai ya ji cewa ƙarya suka yi masa da suka ce wai daga ƙasa mai nisa suka fito. Su ’yan ƙasar Kan’ana ne. Sai Joshua ya tambaye su: ‘Me ya sa kuka yi mana ƙarya?’ Sai suka ce: ‘Mun ji tsoro ne! Mun san cewa Jehobah Allahnku yana tare da ku. Don Allah kar ku kashe mu.’ Joshua bai kashe su ba.
Kafin ka sani, sai sarakuna biyar daga ƙasar Kan’ana tare da sojojinsu suka ce za su kashe Gibeyonawa. Joshua da sojojinsa ba su yi barci ba a daren don sun tafi su ceci Gibeyonawan. Sai suka fara faɗa washegari da sassafe, kuma Kan’aniyawan suka soma guduwa. Amma duk inda suka je, Jehobah yana ta harbinsu da ƙanƙara. Sai Joshua ya roƙi Jehobah ya sa rana ta tsaya cak. Me ya sa zai yi irin wannan roƙon tun da yake ba a taɓa ganin rana ta tsaya cak ba? Ya yi hakan ne don ya nuna cewa ya dogara ga Jehobah sosai. Kuma rana ta tsaya cak har sai da Isra’ilawa suka ci sarakuna da kuma sojojin Kan’aniyawa da yaƙi.
“Abin da duk za ku faɗa, ya tsaya kan ‘I’ ko ‘A’a’ kawai. In dai ya zarce haka, daga Mugun ya fito.”—Matta 5:3, Littafi Mai Tsarki
-