WAƘA TA 42
Addu’ar Bawan Allah
Hoto
(Afisawa 6:18)
1. Mafi Iko, Jehobah Allahnmu.
Ka tsarkake sunanka mafi girma.
Kana aikata duk nufinka,
Muna jiran albarkar Mulkinka.
Muna jira ya zo don
Mu sami albarkarsa.
2. Allah muna godiya don ranmu.
Ka ba mu abubuwa masu kyau.
Ka ba mu rai da kuma haske,
Ka ba mu hikima da basira.
Muna maka godiya
Kuma muna yabon ka.
3. A duniya muna shan wahala.
Amma muna dogara a gare ka,
Allah Ubanmu muna roƙo.
Ka ba mu ƙarfin da za mu jimre
Kuma mu yi nufinka.
Mu riƙe amincinmu.
(Ka duba Zab. 36:9; 50:14; Yoh. 16:33; Yaƙ. 1:5.)