WAƘA TA 41
Allah Ka Ji Roƙona
Hoto
(Zabura 54)
1. Ya Ubana ka ji roƙona.
Kai ne Allah, kai zan bauta wa.
Babu wani Allah kamar ka.
(AMSHI)
Sarki Jehobah, ji roƙona.
2. Allah ina godiya sosai,
Ka ba ni rai, ka nuna hanya.
Ina murna domin ƙaunarka.
(AMSHI)
Sarki Jehobah, ji roƙona.
3. E, ina so in yi nufinka!
Ka taimake ni in yi hakan.
Ba ni ƙarfi domin in jimre.
(AMSHI)
Sarki Jehobah, ji roƙona.
(Ka kuma duba Fit. 22:27; Zab. 106:4; Yaƙ. 5:11.)