DARASI NA 28
Ka Riƙa Nuna Godiya don Abin da Jehobah da Yesu Suka Yi Maka
Yaya kake ji sa’ad da abokinka ya ba ka wata kyauta mai kyau? Babu shakka, kyautar tana sa ka farin ciki sosai kuma kana so ka nuna wa abokinka cewa kana son kyautar. Jehobah da Yesu sun ba mu kyauta mafi kyau da muka taɓa samu. Mene ne wannan kyautar, kuma ta yaya za mu nuna cewa muna godiya?
1. A wace hanya ce za mu nuna godiya don abin da Allah da Yesu suka yi mana?
Littafi Mai Tsarki ya ce ‘dukan wanda ya ba da gaskiya ga [Yesu]’ zai sami rai na har abada. (Yohanna 3:16) Mene ne ba da gaskiya yake nufi? Ba kawai yin imani da Yesu ba ne, amma muna bukatar mu nuna bangaskiya ta zaɓinmu da kuma ayyukanmu. (Yakub 2:17) Idan muka nuna bangaskiya ta ayyukanmu da kuma furucinmu, muna ƙarfafa dangantakarmu da Yesu da kuma Jehobah.—Karanta Yohanna 14:21.
2. Wane taro na musamman ne zai taimaka mana mu nuna godiya don abin da Jehobah da Yesu suka yi?
A daren da Yesu ya mutu, ya gaya wa mabiyansa wata hanya da za su riƙa nuna godiya don hadayar da ya yi. Ya gaya musu su riƙa yin wani taro na musamman da ake kira a Littafi Mai Tsarki “Jibin Ubangiji,” ko Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. (1 Korintiyawa 11:20) Yesu ya umurci manzanninsa da kuma Kiristoci a yau su riƙa tuna cewa ya ba da ransa domin mu. Yesu ya ce: “Ku dinga yin haka don tunawa da ni.” (Luka 22:19) A duk lokacin da ka halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, kana nuna cewa kana godiya don ƙaunar da Jehobah da kuma Yesu suka nuna mana.
KA YI BINCIKE SOSAI
Za mu koyi hanyoyin da za ka nuna godiya don ƙaunar da Jehobah da Yesu suka nuna mana. Za mu kuma ga abin da ya sa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu yake da muhimmanci sosai.
3. Mene ne za mu yi don mu nuna godiya?
A ce wani ya cece ka sa’ad da ruwa yake so ya ɗauke ka. Za ka manta da abin da mutumin ya yi maka ne? Ko za ka nemi damar gode masa?
Muna da damar samun rai na har abada domin Jehobah ya yi mana alheri. Ku karanta 1 Yohanna 4:8-10, sai ku tattauna tambayoyin nan:
Me ya sa hadayar Yesu kyauta ce ta musamman?
Yaya kake ji domin abin da Jehobah da Yesu suka yi maka?
Ta yaya za mu nuna godiya don abin da Jehobah da Yesu suka yi mana? Ku karanta 2 Korintiyawa 5:15 da 1 Yohanna 4:11; 5:3. Bayan kun karanta kowane nassi, sai ku tattauna tambayar nan:
Kamar yadda aka nuna a nassin, mene ne za mu yi don mu nuna godiya?
4. Ka yi koyi da Yesu
Yin koyi da Yesu ita ce wata hanya da za mu nuna godiyarmu. Ku karanta 1 Bitrus 2:21, sai ku tattauna tambayar nan:
A waɗanne hanyoyi ne za mu bi misalin Yesu?
Yesu yana son Kalmar Allah, ya yi wa’azi kuma ya taimaka wa mutane
5. Ka halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu
Don ka ga abin da ya faru a Taron Tunawa da Mutuwar Yesu na farko, ku karanta Luka 22:14, 19, 20. Sai ku tattauna tambayoyin nan:
Mene ne ya faru a Jibin Maraice na Ubangiji?
Mene ne gurasa da ruwan inabin suke wakilta?—Ka duba ayoyi na 19 da 20.
Yesu yana so almajiransa su riƙa taron sau ɗaya a shekara kuma a kwanan watan da ya rasu. Saboda haka, Shaidun Jehobah suna wannan taron a kowace shekara yadda Yesu ya ce a yi, don su tuna da mutuwarsa. Don ƙarin bayani game da wannan taro mai muhimmanci, ku kalli BIDIYON nan. Sai ku tattauna tambayar da ke gaba.
Mene ne ake yi a Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?
Gurasar tana wakiltar kamiltaccen jikin Yesu da ya ba da hadaya domin mu. Ruwan inabin kuma yana wakiltar jininsa
WASU SUN CE: “Na riga na karɓi Yesu a matsayin Ubangijina da Mai Cetona. Saboda haka, ba na bukatar kome kuma.”
Ta yaya za ka yi amfani da Yohanna 3:16 da Yakub 2:17 don ka nuna cewa akwai ƙarin abubuwan da ake bukatar a yi?
TAƘAITAWA
Muna nuna godiya don abin da Yesu ya yi mana ta wajen ba da gaskiya gare shi da kuma halartan Taron Tunawa da Mutuwarsa.
Bita
Mene ne ba da gaskiya ga Yesu yake nufi?
Ta yaya za ka nuna godiya domin abin da Jehobah da Yesu suka yi maka?
Me ya sa yake da muhimmanci mu halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?
KA BINCIKA
Ku kalli bidiyon nan don ku ga abin da tunawa da mutuwar Yesu zai ƙarfafa mu mu yi.
Ku karanta talifin nan don ku koyi yadda za ku kasance da tabbaci ga alkawuran Jehobah.
“Ka Kasance da Tabbaci a Kan Alkawuran da Jehobah Ya Yi” (Hasumiyar Tsaro, Oktoba 2016)
Ku karanta talifin nan don ku ga yadda koya game da hadayar Yesu ya inganta rayuwar wata mai suna Victoria Tong.
“Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Agusta, 2011)
Ku karanta talifin nan don ku san abin da ya sa mutane kaɗan ne suke cin gurasa da kuma shan ruwan inabi a Taron Tunawa da Mutuwar Yesu.