WAƘA TA 18
Muna Godiya Domin Mutuwar Yesu
Hoto
1. Allah Jehobah yau,
muna a gabanka,
Don ka nuna mana ƙaunar
da ba kamarta.
Ka aiko da Ɗanka Yesu
don mu rayu.
Babu wata sadaukarwar
da ta kai wannan.
(AMSHI)
Ya ba da ransa dominmu.
Ya yi hakan da jininsa.
Har abada
za mu riƙa yi maka godiya.
2. Yesu ya yi sadaukarwar
da son ransa.
Ya ba da ransa domin
yana ƙauna sosai.
Yanzu muna da bege don
ya cece mu.
Muna da begen yin rayuwa
har abada.
(AMSHI)
Ya ba da ransa dominmu.
Ya yi hakan da jininsa.
Har abada
za mu riƙa yi maka godiya.
(Ka kuma duba Ibran. 9:13, 14; 1 Bit. 1:18, 19.)