WAƘA TA 48
Mu Riƙa Bauta wa Jehobah Kullum
Hoto
(Mikah 6:8)
1. Za mu riƙa yin tafiya
Da Jehobah Maɗaukakinmu.
Allahnmu mai alheri ne
Yana sāka wa amininsa!
Jehobah ne ya jawo mu
Domin mu kusace shi.
Mun yi alkawari cewa
Za mu bauta wa Allahnmu.
2. Shaiɗan maƙiyin Jehobah
Yana tsananta wa dukanmu,
Domin Allah ya ƙayyade
Ranar da za ya halaka shi.
Jehobah zai taimake mu
Mu kusace shi sosai,
Domin mu riƙe aminci
Mu bi ja-gorancinsa ma.
3. Jehobah ya yi tanadi,
Tanadin ruhu da Kalmarsa
Da kuma ikilisiya
Da addu’o’in da muke yi.
In mun bauta wa Jehobah
Zai riƙa koyar da mu,
Zai sa mu riƙe aminci,
Kuma mu faranta ransa.
(Ka kuma duba Far. 5:24; 6:9; 1 Sar. 2:3, 4.)