Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w21 Fabrairu pp. 14-19
  • Yadda Za Mu Fahimci Shugabanci a Ikilisiya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Mu Fahimci Shugabanci a Ikilisiya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YAYA YA KAMATA MU ƊAUKI ’YAN’UWA MATA?
  • KOWANE ƊAN’UWA SHUGABAN KOWACE ’YAR’UWA CE?
  • IKON MAGIDANTA DA KUMA DATTAWA
  • KA RIƘA DARAJA YESU SHUGABAN IKILISIYA
  • “Almasihu Ne Shugaban Kowane” Namiji
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Ka Rika Karfafa ʼYan’uwa Mata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Kana Daraja Mata Yadda Jehobah Yake Yi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Rika Daraja Kowa a Ikilisiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
w21 Fabrairu pp. 14-19

TALIFIN NAZARI NA 7

Yadda Za Mu Fahimci Shugabanci a Ikilisiya

Almasihu ne “kan jama’ar masu bi, wato, jikinsa. Shi kansa kuma shi ne Mai Ceton jikin.”—AFIS. 5:23.

WAƘA TA 137 Mata Masu Aminci

ABIN DA ZA A TATTAUNAa

1. Wane dalili ne ya sa mutanen Jehobah suke da haɗin kai?

MUNA farin cikin kasancewa cikin mutanen Jehobah. Me ya sa muke zaman lafiya kuma muke da haɗin kai? Dalili ɗaya shi ne don dukanmu muna yin iya ƙoƙarinmu mu riƙa daraja tsarin shugabanci da Jehobah ya kafa. Idan muka fahimci wannan tsarin sosai, za mu daɗa kasancewa da haɗin kai.

2. Waɗanne tambayoyi ne za mu amsa a wannan talifin?

2 A wannan talifin, za mu tattauna waɗanda suke ja-goranci a ikilisiya. Za mu kuma ba da amsar tambayoyin nan: Wane aiki ne Jehobah ya ba ’yan’uwa mata? Shin kowane ɗan’uwa shugaban kowace ’yar’uwa ce? Dattawa suna da iko a kan ’yan’uwa kamar yadda magidanci yake da iko a kan matarsa da yaransa ne? Bari mu fara tattauna yadda ya kamata mu ɗauki ’yan’uwa mata.

YAYA YA KAMATA MU ƊAUKI ’YAN’UWA MATA?

3. Ta yaya za mu daɗa nuna godiya don abubuwan da ’yan’uwa mata suke yi?

3 Muna daraja ’yan’uwa mata da suke aiki tuƙuru don su kula da iyalinsu. Ban da haka, suna wa’azi da kuma taimaka wa ’yan’uwa a ikilisiya. Za mu daɗa daraja su idan muka yi tunanin yadda Jehobah da Yesu suke ɗaukan su. Ƙari ga haka, za mu amfana idan muka yi la’akari da yadda manzo Bulus ya bi da mata.

4. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah yana daraja maza da mata?

4 Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah yana daraja maza da mata. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a ƙarni na farko, Jehobah ya ba mata da maza ruhu mai tsarki don su yi abubuwa masu ban al’ajabi kamar yin magana a yaruka dabam-dabam. (A. M. 2:1-4, 15-18) Jehobah ya shafe mata da maza da ruhu mai tsarki kuma za su yi sarauta tare da Yesu. (Gal. 3:26-29) Mata da maza za su sami ladar yin rayuwa har abada a duniya. (R. Yar. 7:9, 10, 13-15) Ƙari ga haka, mata da maza ne aka ba umurnin yin wa’azi da kuma koyarwa. (Mat. 28:19, 20) Alal misali, littafin Ayyukan Manzanni ya ambata wata ’yar’uwa mai suna Biriskilla, wadda ita da mijinta Akila suka taimaka wa Afolos ya fahimci gaskiya, duk da cewa shi mutum ne mai ilimi sosai.—A. M. 18:24-26.

5. Kamar yadda Luka 10:38, 39, 42 suka nuna, mene ne ra’ayin Yesu game da mata?

5 Yesu ya girmama mata kuma ya daraja su. Farisiyawa sun rena mata, ba sa yin magana da su a cikin jama’a, kuma ba sa tattauna Kalmar Allah da su. Yesu bai bi al’adar Farisiyawa ba. Maimakon haka, ya tattauna Kalmar Allah da mata sa’ad da yake tattaunawa da sauran almajiransa.b (Karanta Luka 10:38, 39, 42.) Ban da haka, Yesu ya yi wa’azi tare da mata. (Luk. 8:1-3) Kuma ya ba su gatar gaya wa almajiransa cewa an ta da shi daga mutuwa.—Yoh. 20:16-18.

6. Ta yaya manzo Bulus ya nuna cewa yana daraja mata?

6 Manzo Bulus ya umurci Timoti ya riƙa girmama mata. Bulus ya gaya masa cewa ya riƙa bi da “tsofaffin mata kuma kamar mama, sa’an nan ’yan mata kuma kamar ’yan’uwa.” (1 Tim. 5:1, 2) Duk da cewa Bulus ya taimaka wa Timoti sosai don ya manyanta, ya ce mahaifiyar Timoti da kakarsa ce suka fara koya masa “Rubutattun Kalmomin Allah.” (2 Tim. 1:5; 3:14, 15) Bulus ya ambata sunayen ’yan’uwa mata sa’ad da yake aika saƙon gaisuwa a wasiƙarsa ga Romawa. Ya lura da ayyukan da waɗannan ’yan’uwa mata suka yi kuma ya gode musu.—Rom. 16:1-4, 6, 12; Filib. 4:3.

7. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

7 Kamar yadda aka nuna a talifin da ya gabata, Littafi Mai Tsarki bai nuna cewa ’yan’uwa maza sun fi mata daraja ba. ’Yan’uwa mata suna taimakawa a ikilisiya sosai, kuma dattawa suna bukatar taimakonsu don ’yan’uwa a ikilisiya su zauna lafiya kuma su kasance da haɗin kai. Amma muna bukatar mu amsa wasu tambayoyi. Alal misali: Me ya sa Jehobah ya bukaci mace ta ɗaure ɗankwali a wasu lokuta? Tun da yake maza ne ake naɗa dattawa da kuma bayi masu hidima, hakan yana nufin cewa kowane ɗan’uwa shugaban kowace ’yar’uwa ce?

KOWANE ƊAN’UWA SHUGABAN KOWACE ’YAR’UWA CE?

Yesu yana zaune a kan kursiyinsa a sama kuma walkiyar daukakar Jehobah tana haskaka shi. A karkashinsa akwai hotunan taron ikilisiya, wasu suna ibada ta iyali kuma wata ’yar’uwa tana nazari ita kadai. An maimaita hotunan a sakin layi na 8 da 11-14.

8. Kamar yadda Afisawa 5:23 ta nuna, kowane ɗan’uwa shugaban kowace ’yar’uwa ce? Ka bayyana.

8 Kowane ɗan’uwa shugaban kowace ’yar’uwa ce? A’a! Yesu ne shugabanmu duka. (Karanta Afisawa 5:23.) A cikin iyali, maigida ne yake da iko a kan matarsa. Ɗa da ya yi baftisma ba shi da iko a kan mahaifiyarsa. (Afis. 6:1, 2) A ikilisiya, ikon da dattawa suke da shi a kan ’yan’uwa yana da iyaka. (1 Tas. 5:12; Ibran. 13:17) ’Yan’uwa mata marar aure da ba sa zama da iyayensu, za su ci gaba da daraja iyayensu da kuma dattawa. Amma kamar ’yan’uwa maza a ikilisiya, Yesu ne kaɗai shugabansu.

Wata ’yar’uwa tana nazari ita kadai.

’Yan’uwa marasa aure da ba sa zama da iyayensu suna ƙarƙashin shugabancin Yesu (Ka duba sakin layi na 8)

9. Me ya sa ’yan’uwa mata suke bukatar su ɗaura ɗankwali a wasu lokuta?

9 Jehobah ya ba maza hakkin koyarwa da yin ja-goranci a ikilisiya, amma bai ba mata wannan hakkin ba. (1 Tim. 2:12) Me ya sa? Domin yana so ikilisiya ta kasance da tsari. Idan yanayi ya taso kuma aka bukaci ’yar’uwa ta yi aikin da ’yan’uwa maza ne suke yi, Jehobah ya bukaci ta ɗaura ɗankwali.c (1 Kor. 11:4-7) Jehobah ya faɗi hakan ba don yana rena mata ba, amma don su nuna suna daraja tsarin shugabancin da ya kafa. Yanzu bari mu amsa wannan tambayar: Wane irin iko ne magidanta da dattawa suke da shi?

A Wane Lokaci Ne ’Yar’uwa Take Bukatar Ta Ɗaura Ɗankwali?

Wata ’yar’uwa tana gudanar da taron fita wa’azi. Ta zauna kuma ta daura dankwali.

Don ’yar’uwa ta san yanayin da ya dace ta ɗaura ɗankwali, ya kamata ta amsa waɗannan tambayoyi uku:

  1. 1. Zan yi wa wani addu’a ne a gaban ɗan’uwan da ya yi baftisma? Zan koya wa wani Littafi Mai Tsarki ne a gaban ɗan’uwan da ya yi baftisma?—1 Kor. 11:4, 5.

  2. 2. Ko da ɗan’uwa da ya yi baftisma ba ya wurin, abin da nake so in yi aiki ne da ya kamata ɗan’uwa ya yi?—1 Tim. 2:11, 12; Ibran. 13:17.

  3. 3. Idan ina da aure, mijina yana wurin da nake so in yi addu’a da babbar murya ko kuma koya wa wani Littafi Mai Tsarki ne?—1 Kor. 11:3.

Idan amsar kowanne cikin tambayoyin nan e ce, to ’yar’uwar tana bukatar ta ɗaura ɗankwali. Idan amsar dukan tambayoyin a’a ce, ’yar’uwa ba ta bukatar ta ɗaura ɗankwali.e

IKON MAGIDANTA DA KUMA DATTAWA

10. A wasu lokuta, me zai iya sa dattijo ya kafa dokoki a ikilisiya?

10 Dattawa suna ƙaunar Yesu, kuma suna ƙaunar ‘tumakin’ da Jehobah da kuma Yesu suka ba su amana. (Yoh. 21:15-17) Dattijon da ya damu da ’yan’uwa a ikilisiya sosai, yana iya ganin kansa kamar mahaifi ga ’yan’uwan. Yana iya tunanin cewa, tun da magidanci yana da ikon kafa dokoki da za su kāre iyalinsa, dattijo ma yana iya kafa dokoki da za su kāre ’yan’uwa a ikilisiya. Ƙari ga haka, wasu ’yan’uwa suna iya ƙarfafa dattawa su yi hakan, ta wajen gaya musu su tsai da musu shawarwari. Amma dattawa da magidanta suna da iko iri ɗaya ne?

Wani dattijo yana yin jawabi a taro.

Dattawa suna kula da ’yan’uwa a ikilisiya kuma suna nuna musu cewa suna ƙaunar su. Jehobah ya ba su hakkin cire masu zunubi da suka ƙi tuba daga ikilisiya (Ka duba sakin layi na 11-12)

11. Wace alaƙa ce ke tsakanin ikon dattawa da na magidanta?

11 Bulus ya nuna cewa akwai wasu alaƙa tsakanin ikon dattawa da na magidanta. (1 Tim. 3:4, 5) Alal misali, Jehobah yana so mama da yara su yi wa maigida biyayya. (Kol. 3:20) Kuma yana so ’yan’uwa a ikilisiya su yi wa dattawa biyayya. Jehobah yana so magidanta da dattawa su tabbata cewa waɗanda suke ƙarƙashin ikonsu sun ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah. Kuma ya kamata su nuna musu cewa suna ƙaunar su. Kamar yadda magidanta nagari suke yi, dattawa suna taimaka wa waɗanda suke bukatar taimako a ikilisiya. (Yaƙ. 2:15-17) Ƙari ga haka, Jehobah yana so dattawa da magidanta su taimaka wa ’yan’uwa su bi ƙa’idodinsa. Amma ya gargaɗe su ‘kada su wuce abin da aka rubuta’ a Littafi Mai Tsarki.—1 Kor. 4:6.

Wani dan’uwa yana gudanar da ibada ta iyali.

Magidanta suna da ikon yi wa iyalinsu ja-goranci. Magidancin da ke ƙaunar matarsa zai tattauna da ita kafin ya tsai da shawara (Ka duba sakin layi na 13)

12-13. Kamar yadda Romawa 7:2 ta nuna, ta yaya ikon dattawa da magidanta ya bambanta?

12 Da akwai hanyoyi masu muhimmanci da ikon da dattawa suke da shi ya bambanta da na magidanta. Alal misali, Jehobah ya ba dattawa ikon yin shari’a kuma ya ce su cire masu zunubi da suka ƙi tuba daga ikilisiya.—1 Kor. 5:11-13.

13 Jehobah ya ba magidanta wasu ikon da bai ba dattawa ba. Jehobah ya gaya wa magidanta su kafa wa iyalinsu dokoki kuma su tabbata cewa sun bi dokokin. (Karanta Romawa 7:2.) Alal misali, magidanci yana da ikon gaya wa yaransa lokacin da za su riƙa dawowa gida daddare. Kuma yana da ikon horar da yaransa idan ba su bi dokar ba. (Afis. 6:1) Hakika, magidanci da ke ƙaunar matarsa zai tattauna da ita kafin ya kafa doka, domin su biyu “kamar mutum ɗaya” suke.d—Mat. 19:6.

KA RIƘA DARAJA YESU SHUGABAN IKILISIYA

Yesu yana zaune a kan kursiyinsa a sama kuma walkiyar daukakar Jehobah tana haskaka shi.

Yesu, da ke bin ja-gorancin Jehobah yana yi wa ikilisiya ja-goranci (Ka duba sakin layi na 14)

14. (a) Kamar yadda Markus 10:45 ta nuna, me ya sa ya dace da Jehobah ya naɗa Yesu shugaban ikilisiya? (b) Wane aiki ne Jehobah ya ba Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu? (Ka duba akwatin nan “Hakkin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu.”)

14 Jehobah ya yi amfani da hadayar Yesu don ya fashi kowa a ikilisiya, da kuma mutanen da suka ba da gaskiya ga Yesu. (Karanta Markus 10:45; A. M. 20:28; 1 Kor. 15:21, 22) Don haka, ya dace da Jehobah ya naɗa Yesu wanda ya ba da ransa hadaya a matsayin shugaban ikilisiya. Shi ya sa Yesu yake da ikon kafa dokokin da iyalai da kuma ’yan’uwa a ikilisiya za su bi. Kuma yana da ikon tabbata cewa ana bin dokokinsa. (Gal. 6:2) Amma ba kafa dokoki kawai Yesu yake yi ba, yana kula da mu kuma yana ƙaunar mu.—Afis. 5:29.

Hakkin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu

Mambobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu suna yin taro.

Membobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ba su da iko a kan bangaskiyar ’yan’uwansu. (2 Kor. 1:24) Sun san cewa Yesu shi ne shugaban ikilisiya kuma sun amince da furucinsa cewa: “Dukanku kuwa ’yan’uwa ne.” (Mat. 23:8) Suna ƙaunar ’yan’uwansu sosai kuma suna yin iya ƙoƙarinsu don su kula da su. Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu suna bin ja-gorancin Yesu don su tsara ayyukan Shaidun Jehobah a dukan duniya. Suna naɗa Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Shaidun Jehobah da kuma masu kula da da’ira. (Afis. 4:7-13) Masu kula da da’ira kuma suna naɗa dattawa a ikilisiya. (A. M. 14:23; Tit. 1:5) Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu suna yin iya ƙoƙarinsu don su ci gaba da tanada abubuwan da za su sa ’yan’uwa su kusaci Jehobah. Suna yin hakan ta wasiƙu da umurni da littattafai da shirye-shiryen JW da makarantu da taron ikilisiya da taron yanki da kuma taron da’ira. (A. M. 15:22-35) Membobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu suna ƙaunar ’yan’uwa sosai. Saboda haka, sa’ad da bala’i ya faru ko kuma wasu mawuyacin yanayi ya taso, suna tuntuɓar ofishinmu da ke wurin da gaggawa don su tabbata cewa ’yan’uwa sun sami taimako.f

15-16. Wane darasi ne ka koya daga furucin ’Yar’uwa Marley da Ɗan’uwa Benjamin?

15 ’Yan’uwa mata suna nuna cewa suna daraja Yesu ta wajen bin ja-gorancin mazan da ya naɗa su kula da su. ’Yan’uwa mata da yawa sun amince da abin da wata ’yar’uwa mai suna Marley da take zama a Amirka ta faɗa. Ta ce: “Hakkina a matsayin mata da kuma ’yar’uwa a ikilisiya yana da daraja a gare ni. Ina ƙoƙartawa sosai don in ci gaba da daraja ikon da Jehobah ya ba mijina da kuma dattawa. Mijina da kuma ’yan’uwa maza a ikilisiya sun sa hakan ya kasance mini da sauƙi, domin suna daraja ni kuma suna nuna godiya domin ayyukan da nake yi.”

16 ’Yan’uwa maza suna nuna cewa sun fahimci tsarin shugabanci ta wajen daraja ’yan’uwa mata da kuma girmama su. Wani ɗan’uwa mai suna Benjamin da ke zama a Ingila ya ce: “Na koyi abubuwa da yawa daga kalamin ’yan’uwa mata a taro da kuma shawarwarin da suka ba ni game da yadda zan riƙa wa’azi da kuma koyarwa da kyau. A ganina, aikin da suke yi yana da muhimmanci sosai.”

17. Me ya sa muke bukatar mu daraja tsarin shugabanci da Jehobah ya kafa?

17 Idan maza da mata da magidanta da dattawa suka fahimci da kuma daraja tsarin shugabanci da Jehobah ya kafa, za a yi zaman lafiya a ikilisiya. Kuma abu mafi muhimmanci, za mu ɗaukaka Jehobah, Ubanmu mai ƙauna.—Zab. 150:6.

MECE CE AMSARKA?

  • Yaya ya kamata mu ɗauki ’yan’uwa mata a ikilisiya?

  • Kowane ɗan’uwa shugaban kowace ’yar’uwa ce? Ka bayyana.

  • Ta yaya ikon magidanta da na dattawa ya bambanta?

WAƘA TA 123 Mu Riƙa Bin Ja-gorancin Jehobah

a Wane aiki ne Jehobah ya ba ’yan’uwa mata a ikilisiya? Shin kowane ɗan’uwa shugaban kowace ’yar’uwa ce? Dattawa da magidanta suna da iko iri ɗaya ne? A wannan talifin, za mu ga yadda Littafi Mai Tsarki ya amsa waɗannan tambayoyin.

b Ka duba sakin layi na 6 a talifin nan “Ka Riƙa Ƙarfafa ʼYan’uwa Mata,” da aka wallafa a Hasumiyar Tsaro ta Satumba 2020.

c Ka duba akwatin nan “A Wane Lokaci Ne ’Yar’uwa Take Bukatar Ta Ɗaura Ɗankwali?”

d Don sanin wanda yake da ikon zaɓan ikilisiyar da iyali za su riƙa halartan taro, ka duba talifin nan “Ka Riƙa Daraja Kowa a Ikilisiya,” a Hasumiyar Tsaro ta Agusta 2020, sakin layi na 17-19.

e Don samun ƙarin bayani game da wannan batun, ka duba littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah,” shafuffuka na 209-212.

f Don samun ƙarin bayani game da hakkin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2013, shafuffuka na 20-25.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba