Ta Yaya Za Mu Zama Masu Salama?
DA YAKE muna zama a duniyar da ke cike da matsaloli, wajibi ne mu yi iya ƙoƙarinmu don mu riƙa zaman lafiya da mutane. Duk da haka, ko da muna zaman lafiya, muna yawan fama don mu ci gaba da yin hakan. Mene ne Kalmar Allah ta ce za ta taimaka mana mu riƙa zaman lafiya da mutane? Kuma ta yaya za mu taimaka wa mutane su riƙa zaman lafiya?
ME ZAI TAIMAKA MANA MU ZAMA MASU ZAMAN LAFIYA?
Zama masu kwanciyar hankali zai taimaka mana mu zauna lafiya da mutane. Ƙari ga haka, muna bukatar mu ƙulla abokantaka da wasu. Kuma abin da ya fi muhimmanci shi ne ƙulla dangantaka na kud da kud da Allah. Ta yaya za mu yi hakan?
Yawan damuwa yana hana mutane da yawa samun kwanciyar rai
Muna nuna cewa mun dogara ga Jehobah kuma muna son mu ƙulla abokantaka da shi idan muna masa biyayya kuma muna bin ƙa’idodinsa. (Irm. 17:7, 8; Yaƙ. 2:22, 23) Jehobah zai kusace mu kuma ya sa mu kasance da kwanciyar rai. Littafin Ishaya 32:17 ya ce: “Amfanin yin abin da yake daidai, shi ne salama. Abin da yin adalci zai haifar, shi ne natsuwa da hutawa har abada.” Za mu sami kwanciyar hankali idan muna yi wa Jehobah biyayya da dukan zuciyarmu.—Isha. 48:18, 19.
Jehobah yana kuma yin amfani da ruhunsa mai tsarki don ya taimaka mana mu zauna lafiya da mutane.—A. M. 9:31.
RUHUN ALLAH YANA TAIMAKA MANA MU YI ZAMAN LAFIYA
Salama ce ’yar ruhu na uku da manzo Bulus ya ambata. (Gal. 5:22, 23) Tun da yake salama ’yar ruhun Allah ce, wajibi ne mu bi ja-gorancin ruhu mai tsarki don mu zauna lafiya da mutane. Za mu tattauna hanyoyi biyu da ruhun Allah zai iya taimaka mana mu yi zaman lafiya.
Na farko, karanta Kalmar Allah a kai a kai zai taimaka mana mu yi zaman lafiya da mutane. (Zab. 1:2, 3) Sa’ad da muke yin bimbini a kan abin da muka karanta a cikin Littafi Mai Tsarki, ruhun Allah yana taimaka mana mu fahimci ra’ayin Jehobah a kan al’amura da yawa. Alal misali, muna ganin abin da ke motsa Jehobah ya kasance da salama da kuma dalilin da ya sa salama take da muhimmanci a gare shi. Idan muka yi amfani da abin da muka koya daga Kalmar Allah, za mu zauna lafiya da mutane.—K. Mag. 3:1, 2.
Na biyu, wajibi ne mu nemi taimakon ruhu mai tsarki. (Luk. 11:13) Jehobah ya yi mana alkawari cewa idan muka nemi taimakonsa, ‘salama irin wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam, za ta kuma tsare zukatanmu da tunaninmu cikin Almasihu Yesu.’ (Filib. 4:6, 7) Idan muna addu’a a kai a kai kuma muka nemi taimakon ruhun Jehobah, zai sa mu kasance da kwanciyar hankali wanda yanayi ne da abokansa kaɗai suke morewa.—Rom. 15:13.
Ta yaya wasu suka bi wannan shawarar da ke cikin Nassi kuma suka yi canje-canjen da suka sa su kasance da salama da Jehobah da kwanciyar hankali kuma suka zauna lafiya da mutane?
YADDA SUKA SOMA ZAMAN LAFIYA
Akwai mutanen da kafin su soma bauta wa Jehobah, suna “saurin fushi.” Amma a yau, sun zama masu sauƙin kai da nasiha da haƙuri kuma suna son zaman lafiya.a (K. Mag. 29:22) Bari mu tattauna labarin masu shela biyu waɗanda kafin su zama Shaidu suna saurin fushi. Amma yanzu sun daina irin wannan halin.
Bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da kuma neman taimakon ruhun Allah za su taimaka mana mu sami kwanciyar hankali
Kafin wani mai suna David ya yi baftisma, bai da halin kirki. Yana yawan gaya wa mutane baƙar magana kuma yakan zagi ’yan’uwansa da kuma iyayensa. Amma da shigewar lokaci, sai David ya canja halinsa kuma ya soma zaman lafiya da mutane. Mene ne ya taimaka masa? Ya ce, “Na soma bin shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki, kuma hakan ya sa ni da ’yan’uwana muka soma daraja juna sosai.”
Yadda aka yi renon wata mai suna Rachel ya shafe ta sosai. Ta ce, “Har yanzu, ina fama da saurin fushi domin na yi girma a iyalin da kowa yake saurin fushi.” Mene ne ya taimaka mata ta riƙa zaman lafiya da mutane? Ta ce, “Nakan yi addu’a ga Jehobah a kai a kai kuma in nemi taimakonsa.”
Ban da David da Rachel, akwai wasu misalai da suka nuna cewa idan muka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma muka roƙi Allah ya ba mu ruhunsa mai tsarki, za mu sami kwanciyar hankali sosai. Hakika, duk da cewa muna rayuwa a duniyar da ke cike da matsaloli, za mu sami kwanciyar hankali da zai sa mu yi zaman lafiya da iyalinmu da kuma ’yan’uwa a ikilisiya. Ban da haka ma, Jehobah ya umurce mu ‘mu yi iyakar ƙoƙarinmu, in zai yiwu, mu yi zaman lafiya da kowa.’ (Rom. 12:18) Hakan zai yiwu kuwa? Kuma ta yaya za mu amfana idan muka yi zaman lafiya da mutane?
KA ZAUNA LAFIYA DA MUTANE
Wa’azin da muke yi game da Mulkin Allah yana taimaka wa mutane su kasance da salama. (Isha. 9:6, 7; Mat. 24:14) Abin farin ciki shi ne mutane da yawa suna saurare mu. A sakamakon haka, yanzu ba sa fushi ko kuma ɓacin rai don abubuwan da suke faruwa. Amma suna da bege cewa abubuwa za su gyaru a nan gaba, kuma hakan yana sa su ‘nemi salama da dukan zuciyarsu.’—Zab. 34:14.
Amma ba kowa ba ne yake son jin wa’azinmu a lokaci na farko da muka kai musu ziyara ba. (Yoh. 3:19) Duk da haka, ruhu mai tsarki yana taimaka mana mu riƙa wa’azi da kwanciyar hankali kuma mu riƙa daraja mutane. Ta yin hakan, muna bin umurnin Yesu da ke littafin Matiyu 10:11-13, ya ce: “Sa’ad da kuka shiga gidan, ku ce, ‘Salama a gare ku.’ Idan gidan ya cancanta, sai salamarku ta sauka a kansa, amma idan bai cancanta ba, sai salamarku ta komo gare ku.” Idan muka bi umurnin Yesu, za mu bar gidan da muka shiga lafiya, da fatan cewa za mu koma mu taimaka wa mutumin a nan gaba.
Ƙari ga haka, muna nuna cewa muna son zaman lafiya idan muna daraja ma’aikatan gwamnati, har ma da waɗanda ba sa so mu riƙa wa’azi. Alal misali, gwamnatin wata ƙasa a Afirka ta ƙi ba mu izinin gina Majami’un Mulki. Da yake muna son a sasanta matsalar, sai aka tura wani ɗan’uwa da ya taɓa yin hidima a wannan ƙasar ya je birnin Landan a Ingila don ya tattauna da Babban Kwamishinan da ke kula da ayyukan wannan ƙasar a Afirka. An umurci ɗan’uwan ya gaya wa Kwamishinan yadda Shaidun Jehobah suke yin aikinsu a ƙasar cikin lumana. Mene ne sakamakon wannan ziyarar?
Ɗan’uwan ya ce: “Da na isa ɗakin karɓan baƙi, sai na ga wata da take aiki a wurin, kuma ta yi ado kamar mutanen da na iya yarensu. Sai na gaishe ta da yarensu. Abin ya ba ta mamaki, sai ta tambaye ni, ‘Kana son ka ga wani ne?’ Na amsa da fara’a cewa na zo ne in ga Babban Kwamishinan. Sai ta kira kwamishinan a waya, kuma da muka haɗu sai ya gaishe ni da yarensu. Bayan haka, ya saurare ni da kyau sa’ad da nake bayyana masa irin aikin da Shaidun Jehobah suke yi.”
Yadda ɗan’uwan ya bayyana wa kwamishinan irin aikin da Shaidun Jehobah suke yi, ya sa ya canja ra’ayinsa game da aikinmu. Ba da daɗewa ba bayan haka, gwamnatin wannan ƙasar da ke Afirka ta ba mu izinin yin gini. Hakika, ’yan’uwa sun yi farin ciki sosai domin wannan sakamakon! Babu shakka, idan muka daraja mutane, hakan zai kawo sakamako mai kyau har ma da zaman lafiya.
KU ZAUNA LAFIYA HAR ABADA
A yau, bayin Jehobah suna zaman lafiya da juna. Kana iya sa mu ci gaba da hakan idan ka yi iya ƙoƙarinka don ka riƙa nuna wannan halin. Kuma abin da ya fi muhimmanci shi ne, za ka sami amincewar Jehobah kuma ka zauna cikin salama har abada a sabuwar duniya.—2 Bit. 3:13, 14.
a A nan gaba, za mu tattauna nasiha a jerin talifofi na ’ya’yan ruhu mai tsarki.