ƘARIN BAYANAI
1 JEHOBAH
Sunan Allah, Jehobah ne kuma mun fahimci cewa sunan yana nufin “Yana Sa Ya Kasance.” Jehobah shi ne Allah Maɗaukaki kuma shi ya halicci kome da kome. Yana da ikon yin duk wani abin da ya ga damar yi.
An rubuta sunan Allah a Ibrananci da harufa huɗu. A Turanci, waɗannan harufa su ne YHWH ko JHVH. A asalin Littafi Mai Tsarki na Ibrananci, sunan Allah ya bayyana kusan sau 7,000. Mutane a duk duniya suna amfani da harsuna dabam-dabam wajen kiran sunan Jehobah.
2 LITTAFI MAI TSARKI HURARREN LITTAFI NE “DAGA ALLAH”
Allah ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki, amma ya yi amfani da mutane wajen rubuta shi. Wannan rubutun yana nan kamar yadda manaja yake gaya wa sakatarensa ya rubuta wasiƙa a madadinsa. Allah ya yi amfani da ruhu mai-tsarki wajen ja-gorar mutanen da suka rubuta Littafi Mai Tsarki don su rubuta Kalmarsa. Ruhun Allah ya ja-gorance su a hanyoyi dabam-dabam, wasu an gaya musu abin da za su rubuta ta hanyar wahayi ko mafarki.
3 ƘA’IDODI
Ƙa’idodi muhimman koyarwa ne a cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ƙa’idar nan “zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki” ta koya mana cewa mutane za su iya rinjaye mu mu yi abubuwa masu kyau ko marar kyau. (1 Korintiyawa 15:33) Ƙa’idar nan kuma “iyakar abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe” ta koya mana cewa duk abu marar kyau da muka yi yana da mummunar sakamako.—Galatiyawa 6:7.
4 ANNABCI
Wannan saƙo ne daga Allah. Zai iya zama bayani a kan Kalmar Allah da ƙa’idodin da Allah yake so mu bi da umurni ko kuma wani hukunci. Zai iya zama saƙo a kan abin da zai faru a nan gaba. Akwai annabci da yawa na Littafi Mai Tsarki da sun riga sun cika.
5 ANNABCI GAME DA ALMASIHU
Yesu ne ya cika annabci da yawa na Littafi Mai Tsarki game da Almasihu. Ka duba akwatin nan “Annabci Game da Almasihu.”
▸ Babi na 2, sakin layi na 17, ƙarin bayani
6 DALILIN DA YA SA ALLAH YA HALICCI MUTANE
Jehobah ya halicci duniya ta zama aljanna don mutanen da suke ƙaunar sa su zauna a cikinta. Nufinsa bai canja ba. Nan ba da daɗewa ba, Allah zai kawar da dukan mugunta kuma zai ba bayinsa rai na har abada.
7 SHAIƊAN IBLIS
Shaiɗan ne mala’ika na farko da ya yi tawaye da Allah. Sunan nan Shaiɗan yana nufin “Mai tsayayya,” domin ya yi tsayayya da Jehobah. Iblis kuma yana nufin “Maƙaryaci.” An ba shi wannan sunan ne domin ya yi ƙarya a kan Allah kuma yana yaudarar mutane.
8 MALA’IKU
Jehobah ya halicci mala’iku da daɗewa kafin ya halicci duniya. An halicce su don su yi rayuwa a sama ne. Akwai mala’iku sama da miliyan ɗari. (Daniyel 7:10) Suna da sunaye da kuma halaye dabam-dabam kuma mala’iku masu aminci ba sa son mutane su bauta musu. Matsayinsu ba ɗaya ba ne kuma suna yin ayyuka dabam-dabam. Wasu suna yin hidima a kursiyin Jehobah da kai saƙo da kāre mutane da ja-gorar mutanen Allah a duniya da zartar da hukunci da kuma goyon bayan wa’azi. (Zabura 34:7; Ru’ya ta Yohanna 14:6; 22:8, 9) A nan gaba, za su yi yaƙi tare da Yesu a Armageddon.—Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16; 19:14, 15.
▸ Babi na 3, sakin layi na 5; Babi na 10, sakin layi na 1
9 ZUNUBI
Duk wani abu da muka yi tunaninsa ko muka aikata da ya saɓa wa nufin Jehobah zunubi ne. Da yake zunubi yana ɓata dangantakarmu da Allah, shi ya sa ya ba mu dokoki da kuma ƙa’idodin da za su taimaka mana mu guji yin zunubi da gangan. Da farko, Jehobah ya halicci kome daidai, amma sa’ad da Adamu da Hawwa’u suka zaɓa su yi wa Jehobah rashin biyayya, sun yi zunubi kuma ba su zama kamiltattu ba. Sun tsufa kuma sun mutu. Mu ma da muka gāji zunubi daga Adamu muna mutuwa.
▸ Babi na 3, sakin layi na 7; Babi na 5, sakin layi na 3
10 ARMAGEDDON
Wannan yaƙi ne da Allah zai yi don ya kawar da muguwar duniyar Shaiɗan da kuma dukan mugunta.
▸ Babi na 3, sakin layi na 13; Babi na 8, sakin layi na 18
11 MULKIN ALLAH
Mulkin Allah gwamnati ce da Jehobah ya kafa a sama. Yesu Kristi yana sarauta a matsayin Sarkin Mulkin. A nan gaba, Jehobah zai yi amfani da Mulkinsa wajen kawar da dukan mugunta. Mulkin Allah zai yi sarauta bisa dukan duniya.
12 YESU KRISTI
Allah ya halicci Yesu kafin ya halicci wasu abubuwa. Jehobah ya aiko da Yesu zuwa duniya don ya mutu a madadin dukan mutane. Jehobah ya ta da Yesu bayan da aka kashe shi. Yesu yana sarauta yanzu a sama a matsayinsa na Sarkin Mulkin Allah.
13 ANNABCIN MAKONNI 70
Littafi Mai Tsarki ya annabta lokacin da Almasihun zai bayyana. Hakan zai faru ne a ƙarshen makonni 69 da ya soma daga shekara ta 455, kuma ya ƙare a shekara ta 29 bayan haihuwar Yesu.
Ta yaya muka san cewa ya ƙare a shekara ta 29? Makonni 69 ɗin sun soma ne a shekara ta 455 sa’ad da Nehemiya ya koma Urushalima don ya sake gina birnin. (Daniyel 9:25; Nehemiya 2:1, 5-8) Kamar yadda furucin nan “dozin” yake nufin 12, hakan ma mako yake tuna mana da lamba 7. Makonni bakwai da aka ambata a nan ba kwanaki bakwai na mako guda ba ne, amma makonnin shekara bakwai ne. Hakan ya jitu da yadda ake yawan ƙirga kwanaki a annabcin Littafi Mai Tsarki, wato “rana guda domin shekara guda.” (Littafin Lissafi 14:34; Ezekiyel 4:6) Hakan yana nufin cewa kowane mako shekara bakwai ne kuma makonni 69 ɗin shekara 483 ne, wato (69 x 7). Idan muka ƙirga shekara 483 daga shekara ta 455 kafin haihuwar Yesu, zai kai mu shekara ta 29 bayan haihuwar Yesu. A wannan shekara ce Yesu ya yi baftisma kuma ya zama Almasihu!—Luka 3:1, 2, 21, 22.
Wannan annabcin ya kuma ambata wani mako ɗaya, wanda shekara bakwai ne. A cikin wannan lokacin ne za a kashe Yesu wato a shekara ta 33, kuma daga shekara ta 36, za a yi wa’azin Mulkin Allah a dukan duniya, ba ga Yahudawa kaɗai ba.—Daniyel 9:24-27.
14 KOYARWAR ALLAH-UKU-CIKIN-ƊAYA BA GASKIYA BA CE
Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah Allah, Mahalicci ne kuma shi ya halicci Yesu kafin ya yi sauran abubuwa. (Kolosiyawa 1:15, 16) Yesu ba Allah Maɗaukaki ba ne. Bai taɓa ce shi da Allah daidai suke ba. A maimakon haka, ya ce: “Uba ya fi ni girma.” (Yohanna 14:28; 1 Korintiyawa 15:28) Amma wasu addinai suna koyar da cewa Allah uku ne cikin ɗaya, wato Uba da Ɗa da kuma ruhu mai-tsarki duk ɗaya ne. Babu furucin nan “Allah-uku-cikin-ɗaya” a cikin Littafi Mai Tsarki. Wannan koyarwar ba gaskiya ba ce.
Ruhu mai tsarki ikon da Allah yake amfani da shi ne don ya cim ma nufinsa. Ruhu mai tsarki ba mutum ba ne. Alal misali, Kiristoci na farko sun ‘cika . . . da ruhu mai-tsarki,’ kuma Jehobah ya ce: ‘Zan zuba ruhuna bisa masu-rai duka.’—Ayyukan Manzanni 2:1-4, 17.
▸ Babi na 4, sakin layi na 12; Babi na 15, sakin layi na 17
15 GICIYE
Kiristoci na gaskiya ba sa amfani da giciye a bautarsu ga Allah. Me ya sa?
An daɗe ana amfani da giciye a bauta ta ƙarya. A zamanin dā, arna ne suke amfani da shi a bautarsu da al’adunsu. Shekara 300 bayan mutuwar Yesu, Kiristoci ba su yi amfani da giciye a bautarsu ba. Shekaru da yawa bayan haka, wani Sarkin Ƙasar Roma mai suna Constantine ya sa aka soma yin amfani da giciye a matsayin alamar da ke wakiltar Kiristanci. An yi amfani da giciyen ne don a san da Kiristoci. Amma giciye ba shi da wani alaƙa da Yesu Kristi. Littafin nan New Catholic Encyclopedia ya ce: “Ana amfani da giciye a zamanin dā kafin ma a soma Kiristanci.”
Yesu bai mutu a kan giciye ba. Kalmar Helenanci da aka fassara “giciye” yana nufin “gungume” da “katako” ko kuma “itace.” Wani juyin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Babu wata kalma a cikin Nassosin Helenanci da ke nufin gungume biyu da aka haɗa wadda aka kira giciye.” Yesu ya mutu ne a kan gungume.
Jehobah ba ya son mu yi amfani da sifofi ko gumaka a bautarmu.—Fitowa 20:4, 5; 1 Korintiyawa 10:14.
16 TARON TUNAWA DA MUTUWAR YESU
Yesu ya umurci almajiransa su tuna da Mutuwarsa. Suna yin hakan kowace shekara a ranar 14 ga watan Nisan, wato a kwanan watan da Isra’ilawa suke Idin Ƙetarewa. Mutanen da za su yi sarauta tare da Yesu a sama suna cin gurasan kuma suna shan ruwan inabin. Mutanen da suke begen yin rayuwa a duniya har abada suna halartan taron, amma ba sa cin gurasan kuma ba sa shan ruwan inabin.
17 KURWA
A juyin New World Translation na Turanci, ana fassara kalmar nan “kurwa” a hanyoyi dabam-dabam. A wasu lokuta yana nufin (1) mutum, (2) dabba, ko (3) ran mutum ko kuma ta dabba. Ga wasu misalai:
Mutum. ‘A zamanin Nuhu, . . . mutane kima, watau masu-rai [“kurwa,” NW] takwas, suka tsira ta wurin ruwa.’ (1 Bitrus 3:20) “Kurwa” da aka ambata a nan tana nufin Nuhu da matarsa, ’ya’yansu maza uku da kuma matan ’ya’yansu.
Dabba. “Allah kuwa ya ce, ‘Bari ruwaye su fid da ɗumbun masu rai [“kurwa,” NW] bari tsuntsaye kuma su riƙa tashi bisa duniya ƙarƙashin sarari.’ Allah kuwa ya ce, ‘Bari duniya ta fid da masu rai [“kurwa,” NW] bisa ga irinsu, shanu, da abubuwa masu rarrafe, da dabbobin duniya bisa ga irinsu.’”—Farawa 1:20, 24, Littafi Mai Tsarki.
Ran mutum ko kuma ta dabba. Jehobah ya ce wa Musa: “Dukan mutanen da suka nemi ranka [“kurwarka,” NW] sun mutu.” (Fitowa 4:19) Sa’ad da Yesu yake duniya, ya ce: “Ni ne makiyayi mai-kyau: makiyayi mai-kyau yakan ba da ransa [“kurwa,” NW] domin tumaki.”—Yohanna 10:11.
Ƙari ga haka, idan mutum ya yi wani abu da “dukan ransa” wato dukan kurwarsa, to hakan yana nufin cewa ya yi shi da zuciya ɗaya. (Matta 22:37; Kubawar Shari’a 6:5) Ana iya kiran mataccen mutum ko dabba mataccen kurwa.—Littafin Lissafi 6:6; Haggai 2:13.
▸ Babi na 6, sakin layi na 5; Babi na 15, sakin layi na 17
18 RUHU
Kalmar Ibrananci da Helenanci da aka fassara zuwa “ruhu” a juyin New World Translation na Turanci tana nufin abubuwa da dama. Tana kuma nufin wani abu da mutum ba zai iya gani ba, kamar iska ko numfashin mutum ko kuma na dabba. Kalmar tana kuma iya nufin halittun ruhu da kuma ruhu mai tsarki na Allah. Littafi Mai Tsarki bai koyar da cewa wani abu a jikin mutum yana ci gaba da wanzuwa bayan mutuwa ba.—Fitowa 35:21; Zabura 104:29; Matta 12:43; Luka 11:13.
▸ Babi na 6, sakin layi na 5; Babi na 15, sakin layi na 17
19 GEHENNA
A cikin juyin Littafi Mai Tsarki na Hausa, an fassara kalmar Helenancin nan ‘Gehenna’ zuwa “Jahannama ko Gidan Wuta.” Gehenna sunan wani kwari ne da ke kusa da Urushalima inda ake ƙona shara a zamanin dā. Babu wani bayani da ya nuna cewa ana hukunta mutane ko dabobbi da rai a wannan kwarin a zamanin Yesu. Saboda haka, Gehenna ba ya wakiltar wani wurin da ake wa mutanen da suka mutu azaba har abada. Sa’ad da Yesu yake magana game da mutanen da aka jefa cikin Gehenna, yana nufin halaka na har abada.—Matta 5:22; 10:28.
20 ADDU’AR UBANGIJI
Wannan addu’ar ce Yesu ya yi sa’ad da yake koya wa almajiransa yin addu’a. Ana kuma kiransa addu’ar Ubanmu ko addu’ar misali. Alal misali, Yesu ya ce mu yi addu’a cewa:
“A tsarkake sunanka”
Muna addu’a cewa Jehobah ya cire dukan ƙaryar da ake yi a kan sunansa. Hakan yana da muhimmanci domin muna son kowa a cikin sama da duniya su daraja da kuma ɗaukaka sunan Allah.
“Mulkinka shi zo”
Muna addu’a cewa Mulkin Allah ya halaka wannan muguwar duniyar Shaiɗan, ya yi sarauta bisa duniya kuma ya mai da duniya aljanna.
“Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya”
Muna addu’a cewa nufin Allah ga duniya ya cika domin ’yan Adam kamiltattu masu aminci su yi rayuwa cikin Aljanna har abada, yadda Jehobah ya so sa’ad da ya halicci mutum.
21 FANSA
Jehobah ya yi tanadin fansa domin ya ceci ’yan Adam daga zunubi da mutuwa. An bukaci wannan fansar domin a maido da cikakken rai da mutum na farko, wato Adamu ya ɓatar kuma a daidaita dangantakar ’yan Adam da Allah. Allah ya aiko da Yesu zuwa duniya domin ya mutu a madadin dukan masu zunubi. Mutuwar Yesu ta sa dukan ’yan Adam sun sami zarafin yin rayuwa har abada a matsayin kamiltattu.
▸ Babi na 8, sakin layi na 21; Babi na 9, sakin layi na 13
22 ME YA SA SHEKARA TA 1914 TAKE DA MUHIMMANCI SOSAI?
Annabcin da ke Daniyel sura 4 ya koya mana cewa Allah zai kafa Mulkinsa a shekara ta 1914.
Annabcin: Jehobah ya sa Sarki Nebuchadnezzar ya yi mafarki game da wani babban itacen da aka sare. Ya ga an saka wa sawayen itacen rawanin ƙarfe da na jangaci domin kada ya yi girma har sai “lokatai guda bakwai” sun wuce. Bayan haka, itacen zai sake girma.—Daniyel 4:1, 10-16.
Ma’anar annabcin: Itacen yana wakiltar sarautar Allah. Jehobah ya daɗe yana amfani da sarakuna a Urushalima don su yi sarauta bisa al’ummar Isra’ila. (1 Labarbaru 29:23) Amma waɗannan sarakunan sun yi rashin aminci kuma sun daina sarauta. An halaka Urushalima a shekara ta 607 kafin haihuwar Yesu. Mafarin “lokatai guda bakwai” ɗin ke nan. (2 Sarakuna 25:1, 8-10; Ezekiyel 21:25-27) Sa’ad da Yesu ya ce, “Al’ummai za su tattake Urushalima kuma har zamanan Al’ummai sun cika,” yana magana a kan wannan “lokatai guda bakwai” ne. (Luka 21:24) Saboda haka, wannan “lokatai guda bakwai” ba su ƙare sa’ad da Yesu yake duniya ba. Jehobah ya yi alkawari cewa zai naɗa Yesu sarki a ƙarshen wannan “lokatai guda bakwai.” Sarautar wannan sabon Sarkin, wato Yesu, zai kawo albarka ga dukan bayin Allah a dukan duniya har abada.—Luka 1:30-33.
Tsawon wannan “lokatai guda bakwai”: Wannan “lokatai guda bakwai” ya ɗauki tsawon shekaru 2,520. Idan muka ƙirga shekaru 2,520 daga shekara ta 607 kafin haihuwar Yesu, za mu tsaya a shekara ta 1914. A wannan shekara ce Jehobah ya naɗa Yesu Almasihu a matsayin Sarkin Mulkin Allah a sama.
To yaya muka sami 2,520? Littafi Mai Tsarki ya ce lokatai uku da rabi, kwanaki 1,260 ne. (Ru’ya ta Yohanna 12:6, 14) Saboda haka, “lokatai guda bakwai” ninki biyu ne na wannan adadin ko kuma kwanaki 2,520 ne. Tsawon wannan kwanaki 2,520, shekaru 2,520 ne. Me ya sa muka ce haka? Domin a wasu lokuta, Littafi Mai Tsarki yana nuna cewa “rana guda . . . shekara guda” ce.—Littafin Lissafi 14:34; Ezekiyel 4:6.
23 MIKA’ILU SHUGABAN MALA’IKU
Littafi Mai Tsarki ya ambata shugaban mala’iku guda ɗaya kawai, kuma sunansa Mika’ilu.—Daniyel 12:1; Yahuda 9.
Mika’ilu Shugaban mala’iku masu aminci na Allah ne. Ru’ya ta Yohanna 12:7 ta ce: “Aka yi yaƙi cikin sama: Mika’ilu da nasa mala’iku sun fita su yi gāba da maciji . . . da nasa mala’iku.” Littafin Ru’ya ta Yohanna ya ce Yesu ne Shugaban rundunar Allah, saboda haka, Mika’ilu ne wani sunan da ake kiran Yesu.—Ru’ya ta Yohanna 19:14-16.
24 KWANAKI NA ƘARSHE
Kwanaki na ƙarshe yana nufin lokacin da abubuwa na musamman za su faru a duniya gab da lokacin da Mulkin Allah zai halaka duniyar Shaiɗan. Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da furuci kamar su “cikar zamani” da “bayanuwar Ɗan mutum,” don ya kwatanta wannan lokacin. (Matta 24:3, 27, 37) “Kwanaki na ƙarshe” sun fara sa’ad da Mulkin Allah ya soma ci a sama a shekara ta 1914, kuma zai ƙare sa’ad da Armageddon ya halaka duniyar Shaiɗan.—2 Timotawus 3:1; 2 Bitrus 3:3.
25 TASHIN MATATTU
Sa’ad da Allah ya sa mutumin da ya mutu ya sake rayuwa, to an ta da shi daga matattu ke nan. Littafi Mai Tsarki ya ambata mutane tara da aka tayar daga matattu. Mutane kamar su Iliya da Elisha da Yesu da Bitrus da kuma Bulus sun ta da mutane daga mutuwa. Allah ne ya ba waɗannan mutanen ikon yin wannan mu’ujizar. Jehobah ya yi alkawari cewa zai tayar da ‘masu adalci da marasa adalci.’ (Ayyukan Manzanni 24:15) Littafi Mai Tsarki ya kuma ambata tashin matattu zuwa sama. Hakan na faruwa sa’ad da mutanen da Allah ya zaɓa ko kuma shafe suka tashi daga matattu zuwa sama don su kasance tare da Yesu.—Yohanna 5:28, 29; 11:25; Filibiyawa 3:11; Ru’ya ta Yohanna 20:5, 6.
26 SIHIRI
Sihiri yana nufin neman yin magana da ruhohi kai tsaye ko da taimakon wani kamar boka ko masu tsafi. Mutanen da suke yin haka sun yarda da koyarwar ƙarya da ake yi cewa ruhun matattu suna ci gaba da wanzuwa kuma suna zama fatalwa. Aljanu suna kuma ƙoƙarin sa mutane su yi rashin biyayya ga Allah. Kallon taurari da yin dūba da tsafi da maita da camfi da kuma bori da dai sauran su, duk sihiri ne. Littattafai da mujallu da fina-finai da waƙoƙi da wasanni da kuma fosta suna sa wasu mutane su ji kamar sihiri abu ne mai kyau. Abubuwan da wasu suke yi a jana’iza kamar su yin hadayu don matattu da yin biki a lokacin jana’iza da bikin cika shekara da mutuwa, da takaba da kuma farkawa duk suna da alaƙa da sihiri. Mutane suna yawan shan ƙwayoyi sa’ad da suke son su yi amfani da ikon aljanu.—Galatiyawa 5:20; Ru’ya ta Yohanna 21:8.
▸ Babi na 10, sakin layi na 10; Babi na 16, sakin layi na 4
27 IKON JEHOBAH NA YIN SARAUTA
Jehobah Allah ne Maɗaukaki, kuma shi ne ya halicci sama da duniya. (Ru’ya ta Yohanna 15:3) Kome nasa ne kuma shi ne yake da ikon yin sarauta a kan dukan halittunsa. (Zabura 24:1; Ishaya 40:21-23; Ru’ya ta Yohanna 4:11) Akwai dokokin da dukan halittunsa suke bi. Jehobah yana kuma da ikon naɗa sarakuna. Idan muka yi biyayya ga Allah kuma muka ƙaunace shi, hakan zai nuna cewa muna goyon bayan sarautarsa.—1 Labarbaru 29:11.
▸ Babi na 11, sakin layi na 10
28 ZUB DA CIKI
Mutanen da suke zub da ciki suna yin hakan da gangan don su kashe jaririn da ba a haifa ba tukun. Mata suna yin ɓari a wasu lokuta kuma wannan ba zub da ciki ba ne. Daga lokacin da mace ta yi juna biyu har ta haihu, jaririn da ke cikinta ba wani gaɓar jikinta ba ne, amma wani mutum ne dabam.
29 ƘARIN JINI
Wannan jinya ce da ake wa mutum ta wajen ƙara masa ɗaya cikin gutsurorin jini guda huɗu ko kuma huɗun baki ɗaya. Zai iya zama jinin da aka ciro daga jikin wani ko wanda aka adana a cikin leda da ɗan daɗewa. Gutsurorin jini huɗu su ne tacaccen ruwan jini da jajayen ƙwayoyin jini da fararen ƙwayoyin jini da kuma kamewar jini.
▸ Babi na 13, sakin layi na 13
30 HORO
Kalmar nan “horo” a cikin Littafi Mai Tsarki ba ta nufin hukunci kaɗai. Idan an yi wa mutum horo, to an koyar da shi ko ilimantar da shi ko kuma yi masa gyara. Jehobah ba ya cin mutuncin mutanen da ya yi musu horo. (Misalai 4:1, 2) Jehobah ya kafa wa iyaye misali mai kyau. Horon da yake wa mutane yana da kyau sosai har yana sa mutane da yawa su so horo. (Misalai 12:1) Jehobah yana ƙaunar bayinsa kuma yana koyar da su. Yana ba su umurni don ya yi musu gyara kuma ya sa su riƙa yin abubuwan da ke faranta masa rai. Iyaye suna wa yaransu horo don su taimaka musu su fahimci amfanin yin biyayya. Yana kuma nufin koya musu su riƙa ƙaunar Jehobah da Kalmarsa, wato Littafi Mai Tsarki kuma su fahimci ƙa’idodin da ke cikinta.
▸ Babi na 14, sakin layi na 13
31 ALJANU
Miyagun halittun ruhu ne masu iko sosai. Aljanu miyagun mala’iku ne. Sun zama miyagu sa’ad da suka yi rashin biyayya ga Allah kuma a sakamakon haka, suka zama maƙiyan Allah. (Farawa 6:2; Yahuda 6) Sun goyi bayan Shaiɗan wajen yin tawaye da Jehobah.—Kubawar Shari’a 32:17; Luka 8:30; Ayyukan Manzanni 16:16; Yaƙub 2:19.