Ta Hannun Yohanna
9 Yayin da yake wucewa, sai ya ga wani mutum da tun aka haife shi makaho ne. 2 Kuma almajiransa suka tambaye shi cewa: “Malam, wane ne ya yi zunubi da ya sa aka haifi mutumin nan makaho, shi ne ko kuma iyayensa?” 3 Sai Yesu ya amsa ya ce: “Ba wai saboda mutumin nan ko kuma iyayensa sun yi zunubi ba ne, amma hakan ya faru ne domin mutane su ga ayyukan Allah a jikinsa. 4 Dole ne mu yi ayyukan Wanda ya aiko ni tun da sauran rana; dare yana zuwa kuma ba wanda zai iya yin aiki. 5 Muddin ina duniya, ni ne hasken duniya.” 6 Bayan da ya faɗi abubuwan nan, sai ya tofa miyau a ƙasa, kuma ya kwaɓa shi da ƙasa, sai ya shafa shi a idanun mutumin, 7 kuma ya ce wa mutumin: “Ka je ka wanke idanunka a tafkin Siluwam” (idan an fassara Siluwam yana nufin “Ɓulɓulowa”). Sai mutumin ya tafi ya wanke idanunsa, kuma ya dawo yana gani.
8 Sai maƙwabtansa da kuma waɗanda a dā sun saba ganin sa yana bara,* suka soma cewa: “Ba wannan ne mutumin da ya saba zama yana bara ba?” 9 Wasu suna cewa: “Shi ne.” Wasu kuma na cewa: “Aꞌa, ba shi ba ne, ya yi kama da shi ne.” Mutumin ya ci-gaba da cewa: “Ni ne shi.” 10 Sai suka tambaye shi cewa: “To, yaya aka yi idanunka suka buɗu?” 11 Sai ya amsa ya ce: “Wani mutum da ake kira Yesu ne ya kwaɓa miyaunsa da ƙasa, ya shafa a idanuna kuma ya ce mini, ‘Ka je Siluwam ka wanke idanunka.’ Sai na je na wanke idanuna kuma na soma gani.” 12 Da jin haka, sai suka ce masa: “Ina mutumin yake?” Sai ya ce: “Ban sani ba.”
13 Sai suka kai mutumin da a dā makaho ne wurin Farisiyawa. 14 A Ranar Assabaci ce Yesu ya kwaɓa miyaunsa da ƙasa kuma ya buɗe idanun mutumin. 15 Sai Farisiyawan ma suka soma tambayar mutumin yadda aka yi idanunsa suka buɗu. Mutumin ya ce musu: “Ya kwaɓa miyaunsa da ƙasa ya shafa a idanuna, kuma da na je na wanke, na soma gani.” 16 Sai wasu daga cikin Farisiyawan suka soma cewa: “Wannan mutumin ba daga wurin Allah ya fito ba, domin ba ya bin dokar Assabaci.” Wasu kuma sun ce: “Ta yaya mutum mai zunubi zai yi ayyukan ban mamaki kamar haka?” Sai kansu ya rabu. 17 Sai Farisiyawan suka sake ce wa makahon: “Mene ne raꞌayinka game da shi, tun da yake idanunka ne ya buɗe?” Sai mutumin ya ce: “Shi annabi ne.”
18 Amma Yahudawan ba su yarda cewa mutumin makaho ne a dā kuma yanzu ya soma gani ba, sai da suka kira iyayensa. 19 Kuma suka tambayi iyayensa suka ce: “Wannan ne ɗanku da kuka ce tun aka haife shi makaho ne? Yaya aka yi yanzu yana gani?” 20 Sai iyayensa suka amsa suka ce: “Mun san cewa wannan ɗanmu ne, kuma tun aka haife shi, makaho ne. 21 Amma yadda aka yi ya soma gani, ba mu sani ba, ko kuma wanda ya buɗe idanunsa, ba mu sani ba. Ku tambaye shi, ai shi ba yaro ba ne. Zai faɗa da kansa.” 22 Iyayensa sun faɗi abubuwan nan ne domin suna tsoron Yahudawan, gama Yahudawan sun riga sun shirya cewa duk wanda ya yarda cewa Yesu ne Kristi, dole a kori mutumin daga majamiꞌa. 23 Shi ya sa iyayensa suka ce: “Ai shi ba yaro ba ne. Ku yi masa tambayar.”
24 Sai suka sake kiran mutumin da a dā makaho ne kuma suka ce masa: “Ka ɗaukaka Allah, mu kam mun san cewa mutumin nan mai zunubi ne.” 25 Sai mutumin ya amsa ya ce: “Ko shi mai zunubi ne, ban sani ba. Abin da na sani shi ne, a dā ni makaho ne, amma yanzu ina gani.” 26 Sai suka ce masa: “Mene ne ya yi maka? Ta yaya ya buɗe idanunka?” 27 Sai ya amsa musu ya ce: “Na riga na gaya muku, duk da haka, ba ku saurara ba. Me ya sa kuke so ku sake ji kuma? Ko dai ku ma kuna so ku zama almajiransa ne?” 28 Sai suka yi masa baꞌa suna cewa: “Kai ne almajirin mutumin nan, amma mu almajiran Musa ne. 29 Mun san cewa Allah ya yi wa Musa magana, amma mutumin nan, ba mu san daga ina ya fito ba.” 30 Sai mutumin ya amsa musu ya ce: “Wannan abin mamaki ne, cewa ba ku san inda ya fito ba, duk da haka ya buɗe idanuna. 31 Mun san cewa Allah ba ya saurarar masu zunubi, amma yana saurarar duk wanda yake tsoron sa kuma yana yin nufinsa. 32 Tun zamanin dā, ba a taɓa jin cewa wani ya buɗe idanun wanda aka haife shi makaho ba. 33 Idan ba daga wurin Allah ne mutumin nan ya fito ba, da ba zai iya yin ko ɗaya daga abubuwan nan ba.” 34 Sai suka amsa masa suka ce: “Kai da aka haife ka cikin zunubi, duk da haka kana koyar da mu?” Sai suka kore shi waje.
35 Yesu ya ji cewa sun kori mutumin waje, kuma saꞌad da ya same mutumin, sai ya ce: “Ka ba da gaskiya ga Ɗan mutum?” 36 Sai mutumin ya amsa ya ce: “Maigirma, wane ne shi, domin in iya ba da gaskiya gare shi?” 37 Sai Yesu ya ce masa: “Ka riga ka gan shi, kuma shi ne yake magana da kai.” 38 Mutumin ya ce: “Ubangiji, na ba da gaskiya gare shi.” Kuma ya rusuna a gabansa. 39 Sai Yesu ya ce: “Na zo duniya ne domin wannan shariꞌar, wato waɗanda ba sa gani su soma gani, kuma waɗanda suke gani su zama makafi.” 40 Sai Farisiyawan waɗanda suke tare da shi suka ji abubuwan da ya faɗa, kuma suka ce masa: “Kana ganin mu ma makafi ne?” 41 Sai Yesu ya ce musu: “Da a ce ku makafi ne, da ba ku da zunubi. Amma yanzu kun ce, ‘Muna gani.’ Don haka, ba za a gafarta zunubanku ba.”*