Ta Hannun Luka
5 Akwai lokacin da mutane suke ta matsowa kusa da Yesu, suna saurarar kalmar Allah, kuma a lokacin Yesu yana tsaye a bakin tafkin Ganisaret.* 2 Sai ya ga jiragen ruwa guda biyu a bakin tafkin. Masu jiragen sun fita suna wanke ragarsu ta kamun kifi. 3 Sai ya shiga ɗaya daga cikin jiragen, wanda na Siman ne, kuma ya gaya wa Siman ya ɗan matsar da jirgin cikin ruwa. Sai ya zauna, kuma ya soma koyar da jamaꞌar daga cikin jirgin ruwan. 4 Da ya gama magana, sai ya ce wa Siman: “Ka tura jirgin ruwan zuwa inda yake da zurfi, kuma ku jefa ragarku don ku kama kifi.” 5 Sai Siman ya amsa masa ya ce: “Malam, mun yi fama dukan dare, ba mu kama kome ba. Amma tun da ka ce in saki ragar, zan yi hakan.” 6 Da suka yi hakan, sun kama kifaye da yawa, har ragarsu ta soma yagewa. 7 Sai suka kira abokansu da ke ɗayan jirgin su zo su taimaka musu, sai suka zo suka cika jirage biyun da kifaye, har jiragen suka soma nitsewa. 8 Da Siman Bitrus ya ga hakan, sai ya durƙusa a gaban Yesu, yana cewa: “Ka rabu da ni Ubangiji, domin ni mai zunubi ne.” 9 Domin shi da mutanen da suke tare da shi sun yi mamaki sosai don yawan kifayen da suka kama. 10 Yaƙub da Yohanna ꞌyaꞌyan Zabadi, waɗanda abokan aikin Siman ne, su ma sun yi mamaki sosai. Sai Yesu ya ce ma Siman: “Ka daina jin tsoro, daga yanzu, za ka soma jawo mutane* kamar yadda ake kama kifi.” 11 Sai suka jawo jiragen zuwa bakin tafkin kuma suka bar kome da kome suka bi shi.
12 Wata rana, saꞌad da Yesu yake wani gari, sai ga wani mutum da ke da cutar kuturta mai tsanani sosai! Da ya ga Yesu, sai ya durƙusa a ƙasa ya roƙe shi cewa: “Ubangiji idan kana so, za ka iya warkar da ni.” 13 Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa mutumin, ya ce: “E, ina so! Na warkar da kai.” Nan da nan cutar kuturtar ta rabu da mutumin. 14 Sai ya umurci mutumin kada ya gaya wa kowa, kuma ya ce masa: “Amma ka je ka nuna kanka a wurin firist, kuma ka miƙa hadaya don tsabtacewarka, kamar yadda Musa ya ce a yi don su ga cewa an warkar da kai.” 15 Labari game da shi ya ci-gaba da yaɗuwa, kuma jamaꞌa sukan taru su saurare shi, yana kuma warkar da cututtukansu. 16 Amma yakan je wuraren da ba kowa don ya yi adduꞌa.
17 Wata rana Yesu yana koyarwa, sai Farisiyawa da malaman da ke koyar da Doka* suka zo daga dukan ƙauyukan da ke yankin Galili, da Yahudiya, da kuma Urushalima, suka zauna a wurin da Yesu yake koyarwa; kuma ikon Jehobah* yana tare da shi domin ya warkar da marasa lafiya. 18 Sai ga wasu mutane suna ɗauke da wani mutum da jikinsa ya shanye, yana kwance a kan tabarma* kuma suna ƙoƙarin shigar da shi ɗakin da Yesu yake don su ajiye shi a gabansa. 19 Da yake sun kasa shigar da shi ɗakin saboda jamaꞌa, sai suka hau rufin gidan, suka cire wani ɓangare na rufin, kuma suka saukar da mutumin kwance a kan tabarma daidai a gaban Yesu. 20 Da ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce: “Abokina, an gafarta zunubanka.” 21 Sai marubuta da Farisiyawa suka soma tunani a zuciyarsu, suna cewa: “Wane ne wannan da ke maganar saɓo? Wane ne zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?” 22 Amma Yesu ya san abin da suke tunani a kai, sai ya ce musu: “Tunanin me kuke yi a zuciyarku? 23 Wanne ne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuma a ce, ‘Ka tashi ka yi tafiya’? 24 Amma domin ku san cewa Ɗan mutum yana da iko a duniya ya gafarta zunubai—” sai ya ce wa mutumin nan da jikinsa ya shanye: “Ina ce maka, Ka tashi, ka ɗauki tabarmarka, ka tafi gida.” 25 Sai ya tashi a gabansu, ya ɗauki abin da yake kwance a kai, ya tafi gida, yana ɗaukaka Allah. 26 Sai dukan jamaꞌar suka yi mamaki sosai, suka soma ɗaukaka Allah, kuma tsoro da mamaki ya kama su, suna cewa: “Mun ga abubuwan ban mamaki yau!”
27 Bayan haka, ya fita sai ya ga wani mutum mai karɓan haraji mai suna Lawi, yana zaune a ofishin karɓan haraji, sai ya ce masa: “Ka zama mabiyina.” 28 Sai ya bar kome, kuma ya tashi ya soma bin Yesu. 29 Sai Lawi ya shirya wa Yesu babbar liyafa a gidansa, kuma akwai masu karɓan haraji da yawa, da wasu mutane da suke cin abinci tare da su a liyafar. 30 Da Farisiyawa da marubutansu suka ga hakan, sai suka soma gunaguni kuma suka ce wa almajiransa: “Me ya sa kuke ci da sha tare da masu karɓan haraji da masu zunubi?” 31 Sai Yesu ya amsa musu ya ce: “Masu ƙoshin lafiya ba sa bukatar likita, amma masu rashin lafiya suna bukatar sa. 32 Na zo ne in kira masu zunubi su tuba, ba masu adalci ba.”
33 Sai suka ce masa: “Almajiran Yohanna sukan yi azumi da kuma adduꞌoꞌi, haka ma da almajiran Farisiyawa, amma almajiranka suna ci da sha.” 34 Sai Yesu ya ce musu: “Ba za ku iya sa abokan ango su yi azumi saꞌad da angon yake tare da su ba, ko ba haka ba? 35 Amma lokaci na zuwa da za a ɗauke angon daga wurinsu, a lokacin ne za su yi azumi.”
36 Ya kuma ba su misali yana cewa: “Babu wanda zai yanka sabon yadi ya yi amfani da shi ya yi fācin tsohuwar riga. Idan ya yi hakan, sabon yadin zai yage ya fita kuma sabon yadin ba zai dace da tsohuwar rigar ba. 37 Ƙari ga haka, babu wanda yake zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna.* Idan ya yi hakan, sabon ruwan inabin zai fashe salkunan, ya zube, kuma salkunan za su lalace. 38 Amma dole a zuba sabon ruwan inabi a cikin sababbin salkuna. 39 Babu wanda zai ce a ba shi sabon ruwan inabi bayan ya sha tsohon, domin zai ce, ‘Ai tsohon ya fi daɗi.’”