Ta Hannun Luka
4 Sai Yesu cike da ruhu mai tsarki ya bar Kogin Jodan, ruhun kuma ya kai shi wurare dabam-dabam a cikin daji 2 na kwana arbaꞌin, inda Ibilis ya gwada shi. Kuma bai ci kome ba a cikin kwanakin nan. Bayan da kwanakin nan suka ƙare, sai yunwa ta kama shi. 3 Saboda haka, Ibilis ya ce masa: “Idan kai ɗan Allah ne, ka gaya wa dutsen nan ya zama burodi.” 4 Amma Yesu ya ce masa: “A rubuce yake cewa, ‘Ba da burodi kaɗai mutum zai rayu ba.’”
5 Sai Ibilis ya kai shi kan wani wuri kuma ya nuna masa dukan mulkokin duniyar nan a cikin ɗan lokaci. 6 Saꞌan nan Ibilis ya ce masa: “Zan ba ka iko a kan dukan mulkokin nan da kuma ɗaukakarsu, domin an riga an ba ni su, kuma ina ba wa duk wanda nake so. 7 Saboda haka, idan ka durƙusa a gabana kuma ka yi mini sujada,* dukansu za su zama naka.” 8 Sai Yesu ya amsa ya ce masa: “A rubuce yake cewa ‘Jehobah* Allahnka ne za ka yi wa sujada, kuma shi kaɗai ne za ka bauta wa.’”*
9 Sai Ibilis ya kai Yesu Urushalima, kuma ya sa shi ya tsaya a wurin da ya fi tsawo a haikalin, sai ya ce masa: “Idan kai ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa, 10 domin a rubuce yake cewa, ‘Zai umurci malaꞌikunsa su taimake ka, su kāre ka,’ 11 kuma ‘Za su ɗauke ka a hannayensu don kada ka buga ƙafafunka a kan dutse.’” 12 Sai Yesu ya amsa masa ya ce: “An faɗa a kalmar Allah cewa, ‘Kada ka gwada Jehobah* Allahnka.’” 13 Da Ibilis ya gama gwada Yesu, sai ya tafi kuma ya bar shi har zuwa lokacin da zai samu wani zarafi mai kyau.
14 Sai Yesu ya koma Galili cike da ikon ruhu mai tsarki. Kuma aka yaɗa labarai masu kyau game da shi a dukan yankunan da ke kewaye. 15 Ƙari ga haka, ya soma koyarwa a majamiꞌunsu, kuma dukan mutane suna ta yabon sa.
16 Sai Yesu ya tafi Nazaret, wurin da ya yi girma, kuma kamar yadda ya saba yi a Ranar Assabaci, ya shiga cikin majamiꞌa, ya tashi tsaye don ya yi karatu. 17 Sai aka ba shi naɗaɗɗen littafin annabi Ishaya, ya buɗe littafin, kuma ya ga wurin da aka rubuta cewa: 18 “Ruhun Jehobah* yana tare da ni, ya naɗa ni don in yi shelar labari mai daɗi ga talakawa. Ya aike ni in yi shela ga waɗanda suke bauta, cewa za su sami ꞌyanci. Kuma ga makafi, cewa za su soma gani, waɗanda aka danne kuma, za su sami ꞌyanci. 19 Kuma in yi waꞌazi game da lokacin da mutane za su sami amincewar Jehobah.”* 20 Sai ya nannaɗe littafin, ya miƙa wa mai kula da majamiꞌar kuma ya zauna; sai dukan waɗanda suke majamiꞌar suka zuba masa ido. 21 Ya soma magana ya ce musu: “A yau wannan nassin da kuka ji yanzu, ya cika.”
22 Sai dukansu suka soma magana mai kyau game da shi, kuma suka yi mamaki game da kalmomi masu daɗin ji da suke fitowa daga bakinsa. Sai suka soma tambaya suna cewa: “Wannan ba ɗan Yusufu ba ne?” 23 Sai ya ce musu: “Na san za ku gaya mini cewa, ‘Likita ka warkar da kanka. Abubuwan da muka ji ka yi a Kafarnahum, ka yi su a nan garinka.’” 24 Ya sake ce musu: “A gaskiya ina gaya muku, babu annabin da ake yarda da shi a garinsa. 25 Ina gaya muku gaskiya: Akwai mata da yawa da mazansu suka mutu a Israꞌila a zamanin Iliya, saꞌad da ba a yi ruwan sama na shekaru uku da wata shida ba, kuma aka yi tsananin yunwa a dukan ƙasar. 26 Duk da haka, ba a tura Iliya wajen ko ɗaya daga cikin waɗannan matan ba, amma wurin da aka tura shi kawai shi ne wurin wata mata da mijinta ya rasu da ke Zarefat a ƙasar Sidon. 27 Ƙari ga haka, akwai kutare da yawa a Israꞌila a zamanin annabi Elisha, duk da haka, ba ɗaya daga cikinsu da aka warkar,* sai Naꞌaman mutumin Siriya ne kawai aka warkar.” 28 Da mutanen da suke cikin majamiꞌar suka ji wannan maganar, sai dukansu suka yi fushi sosai. 29 Sai suka tashi, suka ja Yesu zuwa bayan gari, har suka kai shi saman tudun da aka gina garinsu a kai don su jefo shi daga wurin kuma ya faɗi da kai. 30 Amma ya bi ta cikinsu kuma ya yi tafiyarsa.
31 Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari da ke Galili, kuma yana koyar da su a Ranar Assabaci. 32 Sun yi mamakin yadda yake koyarwa, domin ya yi musu magana da iko. 33 Sai wani mutum da ke da aljani a majamiꞌar ya yi magana da babbar murya ya ce: 34 “Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu mutumin Nazaret? Ka zo nan ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, kai ne Mai Tsarkin Nan na Allah.” 35 Amma Yesu ya tsawata masa, yana cewa: “Ka yi shuru, ka fito daga jikinsa.” Sai aljanin ya sa mutumin ya faɗi a gabansu, kuma ya fita daga jikin mutumin ba tare da ya ji masa rauni ba. 36 Sai dukan mutanen suka yi mamaki sosai kuma suka soma ce wa junansu: “Wane irin magana ne haka? Domin da iko ya umurci ƙazaman ruhohin kuma suka fita!” 37 Kuma labari game da shi ya ci-gaba da yaɗuwa a koꞌina a yankin.
38 Bayan da ya bar majamiꞌar, sai ya shiga gidan Siman. A daidai lokacin, mamar matar Siman tana fama da zazzaɓi mai tsanani sosai, sai suka ce masa ya taimaka mata. 39 Sai ya tsaya a inda take kwance, kuma ya warkar da ita. Nan da nan ta tashi ta soma yi musu hidima.
40 Amma da yamma ta yi, sai mutane suka soma kawo masa masu cututtuka dabam-dabam. Kuma ya warkar da dukansu ta wajen sa hannayensa a kan kowannensu. 41 Aljanu ma sun fito daga jikin mutane da yawa. Suna ihu suna cewa: “Kai ne Ɗan Allah.” Amma ya tsawata musu, kuma ya hana su yin magana, domin sun san cewa shi ne Kristi.
42 Da gari ya waye, sai Yesu ya bar garin ya je wurin da ba kowa. Amma jamaꞌar suka soma neman sa har suka same shi kuma suka yi ƙoƙarin hana shi barin su. 43 Amma ya ce musu: “Dole ne in yi waꞌazin labari mai daɗi na Mulkin Allah a wasu garuruwa ma, domin dalilin da ya sa aka aiko ni ke nan.” 44 Sai ya ci-gaba da yin waꞌazi a majamiꞌun yankin Yahudiya.