Ayyukan Manzanni
3 Wata rana, Bitrus da Yohanna suna tafiya zuwa haikali a lokacin adduꞌa, wajen ƙarfe uku na rana,* 2 kuma a daidai lokacin, mutane suna ɗauke da wani mutum da gurgu ne tun haihuwarsa. A kowace rana, sukan ajiye shi kusa da ƙofar haikalin da ake kiran ta Kyakkyawar Ƙofa, domin ya roƙi kuɗi daga wurin mutanen da suke shiga haikalin. 3 Saꞌad da ya ga Bitrus da Yohanna suna shiga haikalin, sai ya soma roƙon su kuɗi. 4 Amma Bitrus da Yohanna suka kalle shi, suka ce masa: “Ka dube mu.” 5 Sai hankalin gurgun ya koma wurinsu yana tsammanin za su ba shi wani abu. 6 Amma Bitrus ya ce: “Azurfa da zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi ne zan ba ka. A cikin sunan Yesu Kristi mutumin Nazaret, ka tashi ka yi tafiya!” 7 Sai Bitrus ya kama hannun dama na mutumin kuma ya ɗaga shi. Nan take, ƙafafunsa suka yi ƙarfi; 8 Sai ya yi tsalle, ya soma tafiya, kuma ya shiga cikin haikalin da su, yana tafiya yana tsalle yana kuma yabon Allah. 9 Dukan mutanen suka gan shi yana tafiya, yana yabon Allah. 10 Suka kuwa gane cewa shi ne mutumin da ya saba zama yana bara a Kyakkyawar Ƙofa na haikalin, sai suka yi mamaki da farin ciki sosai don abin da ya faru da mutumin.
11 Yayin da mutumin yake riƙe da Bitrus da Yohanna, sai dukan mutane suka gudu suka zo wajensu, a wurin da ake kira Rumfar Sulemanu, suna ta mamaki. 12 Saꞌad da Bitrus ya ga hakan, sai ya ce wa mutanen: “Ya ku mutanen Israꞌila, me ya sa wannan abin yake ba ku mamaki haka? Don me kuke kallon mu, sai ka ce da ikonmu ne muka sa ya yi tafiya ko kuma don adalcinmu ne? 13 Allahn Ibrahim, da na Ishaku, da na Yakubu, Allahn kakanninmu, ya ɗaukaka Bawansa Yesu wanda kuka ba da shi a kashe shi, kuma kuka yi mūsun sanin sa a gaban Bilatus, duk da cewa Bilatus ya so ya sake shi. 14 Hakika, kun yi mūsun sanin mutumin nan mai tsarki, mai adalci, kuma kuka roƙa a sako muku mai kisa, 15 kuka kuwa kashe Shugaba mai ba da rai. Amma Allah ya ta da shi daga mutuwa, kuma mu shaidu ne ga wannan. 16 Ta wurin sunansa, da bangaskiyar da muke da ita ga sunansa ne ya sa wannan mutumin da kuke gani kuma kuka sani ya sami ƙarfi. Bangaskiyar da muke da ita ga Yesu ce ta sa wannan mutum ya sami cikakkiyar lafiya a gabanku duka. 17 Yanzu ꞌyanꞌuwa, na sani cewa a cikin rashin sani ne kuka yi hakan, kamar yadda shugabanninku ma suka yi. 18 Amma ta haka ne Allah ya cika abin da ya faɗa ta bakin dukan annabawa, cewa Kristi zai sha wahala.
19 “Saboda haka, ku tuba, kuma ku juyo domin a wanke zunubanku, hakan zai sa Jehobah* da kansa ya riƙa ƙarfafa ku 20 kuma zai iya aiko Kristi wanda ya naɗa domin ku, wato Yesu. 21 Dole ne Yesu ya zauna a sama, har lokacin da za a mai da dukan abubuwa sabo, kamar yadda Allah ya faɗa tun zamanin dā, ta bakin annabawansa masu tsarki. 22 Hakika, Musa ya ce: ‘Jehobah* Allahnku, zai ta da muku wani annabi kamar ni daga cikin ꞌyanꞌuwanku. Dole ne ku saurari dukan abin da zai faɗa muku. 23 A gaskiya, duk wanda bai saurari wannan Annabin ba, za a hallaka shi gabaki-ɗaya daga cikin mutanen.’ 24 Kuma dukan annabawa, daga Samaꞌila da kuma waɗanda suka biyo bayansa, dukansu da suka yi magana, sun yi magana dalla-dalla game da waɗannan kwanakin. 25 Ku ne ꞌyaꞌyan annabawan, da na yarjejeniyar da Allah ya yi da kakanninku, da ya ce wa Ibrahim: ‘Ta wurin zuriyarka ne dukan iyalan duniya za su sami albarka.’ 26 Bayan da Allah ya ta da Bawansa, ya fara aika shi zuwa wurinku tukuna, don ya yi muku albarka ta wajen sa kowannenku ya juyo daga ayyukansa na mugunta.”