Ta Hannun Yohanna
21 Bayan haka, Yesu ya sake bayyana ga almajiransa a Tekun Tibariya. Kuma ga yadda ya bayyana. 2 Siman Bitrus, da Toma (wanda ake kira ꞌYan Biyu), da Nataniyel daga Kana na Galili, da ꞌyaꞌyan Zabadi, da wasu almajiransa biyu, duk suna nan tare. 3 Siman Bitrus ya ce musu: “Za ni kamun kifi.” Sai suka ce masa: “Mu ma za mu tafi tare da kai.” Sai suka fita, suka shiga cikin jirgin ruwa, amma ba su kama kome a daren ba.
4 Da gari ya soma wayewa, Yesu ya tsaya a bakin teku, amma almajiransa ba su gane cewa Yesu ne ba. 5 Sai Yesu ya ce musu: “Yarana, kuna da abin da za ku ci ne?” Sai suka amsa suka ce: “Aꞌa!” 6 Sai ya ce musu: “Ku jefa ragar kamun kifin a hannun dama na jirgin ruwan, za ku samu.” Sai suka jefa ragar, amma ba su iya jawo ta ba, domin kifayen sun yi yawa. 7 Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus: “Ubangiji ne!” Da Siman Bitrus ya ji cewa Ubangiji ne, sai ya saka mayafinsa, domin dā ma bai sa riga ba. Sai ya yi tsalle ya shiga cikin tekun. 8 Amma sauran almajiran suka zo a cikin ƙaramin jirgin ruwa, suna jan ragar kamun kifin cike da kifaye, domin ba su da nisa daga bakin tekun, wajen ƙafa ɗari uku* ne kawai.
9 Da suka fito bakin tekun, sai suka ga garwashin wuta a wurin da kifaye a kai, da kuma burodi. 10 Sai Yesu ya ce musu: “Ku kawo wasu cikin kifayen da kuka kama yanzu.” 11 Sai Siman Bitrus ya shiga cikin jirgin ruwan, ya jawo ragar kamun kifin cike da manyan kifaye guda ɗari da hamsin da uku. Duk da cewa kifayen suna da yawa, ragar ba ta yage ba. 12 Sai Yesu ya ce musu: “Ku zo, ku ci abincin safe.” Amma babu wani cikin almajiransa da yake da ƙarfin zuciya ya tambaye shi cewa: “Wane ne kai?” domin sun san cewa Ubangijinsu ne. 13 Yesu ya zo ya ɗauki burodin ya ba su, ya kuma ɗauki kifin ya ba su. 14 Wannan ne karo na uku da Yesu ya bayyana ga almajiransa bayan ya tashi daga mutuwa.
15 Saꞌad da suka gama cin abincin safe, Yesu ya ce wa Siman Bitrus: “Siman ɗan Yohanna, kana ƙauna ta fiye da abubuwan nan?” Sai ya amsa masa ya ce: “Ƙwarai kuwa, Ubangiji, ai ka san ina ƙaunar ka.” Sai ya ce masa: “Ka ciyar da ꞌyan tumakina.” 16 Sai Yesu ya sake ce masa a karo na biyu: “Siman ɗan Yohanna, kana ƙauna ta?” Sai ya amsa masa ya ce: “Ƙwarai kuwa, Ubangiji, ai ka san ina ƙaunar ka.” Sai ya ce masa: “Ka yi kiwon ꞌyan tumakina.” 17 Ya kuma ce masa a karo na uku: “Siman ɗan Yohanna, kana ƙauna ta?” Sai Bitrus ya yi baƙin ciki domin Yesu ya tambaye shi a karo na uku cewa: “Kana ƙauna ta?” Sai ya ce masa: “Ubangiji, ai ka san kome; ka san ina ƙaunar ka.” Sai Yesu ya ce masa: “Ka ciyar da ꞌyan tumakina. 18 A gaskiya ina gaya maka, lokacin da kake ƙarami, kakan sa wa kanka riga, kuma ka je duk wurin da ka ga dama. Amma idan ka tsufa, za ka miƙe hannayenka, kuma wani zai saka maka riga, ya kai ka wurin da ba ka so ka je.” 19 Yesu ya faɗi haka ne domin ya nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi don ya ɗaukaka Allah. Bayan da ya faɗi hakan, sai ya ce masa: “Ka ci-gaba da bi na.”
20 Bitrus ya juya, kuma ya ga almajirin da Yesu yake ƙauna yana bin Yesu, wato almajirin da ya matso kusa da Yesu a lokacin da suke cin abincin yamma kuma ya tambaye shi cewa: “Ubangiji, wane ne wannan da zai ci amanarka?” 21 Saꞌad da ya gan shi, sai Bitrus ya ce wa Yesu: “Ubangiji, wannan mutumin kuma fa?” 22 Sai Yesu ya ce masa: “Idan nufina ne ya ci-gaba da rayuwa har sai na dawo, ina ruwanka? Kai dai ka ci-gaba da bi na.” 23 Saboda haka, labarin ya yaɗu tsakanin masu bin Yesu cewa wannan almajirin ba zai mutu ba. Amma, Yesu bai gaya masa cewa ba zai mutu ba, ya dai ce: “Idan nufina ne ya ci-gaba da rayuwa har sai na dawo, ina ruwanka?”
24 Wannan shi ne almajirin da ya ba da shaida game da abubuwan nan, kuma shi ne ya rubuta su, mun kuma san cewa shaidarsa gaskiya ce.
25 Hakika, akwai abubuwa da yawa da Yesu ya yi, waɗanda idan aka rubuta su dalla-dalla yadda suka faru, ina ganin duniya da kanta ma ba za ta iya ɗaukan littattafan* da za a rubuta su a ciki ba.