Ta Hannun Markus
1 Wannan shi ne somawar labari mai daɗi game da Yesu Kristi, Ɗan Allah: 2 Kamar yadda aka rubuta a littafin annabi Ishaya cewa: “(Ga shi! Ina aika manzona ya riga ka, wanda zai shirya maka hanya.) 3 Wata murya tana kira a daji tana cewa: ‘Ku shirya hanyar Jehobah!* Ku sa hanyoyinsa su miƙe.’” 4 Yohanna Mai Baftisma yana daji yana waꞌazi cewa mutane su yi baftisma. Hakan zai nuna cewa sun tuba don a gafarta zunubansu. 5 Sai dukan mutanen yankin Yahudiya da dukan mazaunan Urushalima suna ta zuwa wurinsa, kuma ya yi musu baftisma* a Kogin Jodan, yayin da suke faɗan zunubansu a gaban mutane. 6 Yohanna ya sa tufafin da aka yi da gashin raƙumi kuma ya yi ɗamara da fata. Abincinsa fāra ne da ruwan zuma. 7 Yana waꞌazi, yana cewa: “Wanda yake zuwa a bayana ya fi ni ƙarfi, ko igiyar takalmarsa ma ban isa in sunkuya in kunce ba. 8 Na yi muku baftisma da ruwa, amma shi zai yi muku baftisma da ruhu mai tsarki.”
9 A cikin kwanakin nan, Yesu ya zo wurin Yohanna daga Nazaret da ke Galili, kuma Yohanna ya yi masa baftisma a Kogin Jodan. 10 Nan da nan da Yesu ya fito daga ruwan, sai ya ga sama ya buɗe, kuma ya ga ruhun Allah a kamannin kurciya yana saukowa a kansa. 11 Sai wata murya daga sama ta ce: “Kai Ɗana ne, wanda nake ƙauna, na amince da kai.”
12 Nan da nan ruhun ya sa shi ya shiga cikin daji. 13 Sai ya ci-gaba da zama a dajin har kwana arbaꞌin, kuma a wurin Shaiɗan ya gwada shi. Yesu yana tare da dabbobin daji amma malaꞌiku suna yi masa hidima.
14 Bayan da aka kama Yohanna, Yesu ya tafi Galili, yana waꞌazin labari mai daɗi na Allah, 15 yana cewa: “Lokacin da aka shirya ya cika, kuma Mulkin Allah ya yi kusa. Ku tuba, kuma ku ba da gaskiya ga labari mai daɗin nan.”
16 Da yake tafiya a gefen Tekun Galili, sai ya ga Siman da ɗanꞌuwansa Andarawus suna jefa ragarsu a cikin tekun domin su masu kamun kifi ne. 17 Sai Yesu ya ce musu: “Ku bi ni, zan mai da ku masu jawo mutane kamar yadda ake kama kifi.” 18 Nan da nan suka bar ragarsu suka bi shi. 19 Da ya yi gaba kaɗan, sai ya ga Yaƙub ɗan Zabadi da ɗanꞌuwansa Yohanna a cikin jirgin ruwa, suna gyara ragarsu. 20 Nan da nan sai ya kira su. Sai suka bar babansu Zabadi a cikin jirgin ruwan da mutanen da suke musu aiki kuma suka bi Yesu. 21 Sai suka shiga Kafarnahum.
Da aka soma Assabaci, Yesu ya shiga majamiꞌa ya soma koyarwa. 22 Kuma suka yi mamakin yadda yake koyarwa, domin yana koyar da su kamar wanda yake da iko, ba kamar marubuta ba. 23 A lokacin, akwai wani mutum da ke cikin majamiꞌarsu da ke da ruhu mai ƙazanta, kuma ya yi ihu cewa: 24 “Ina ruwanka da mu, Yesu mutumin Nazaret? Ka zo nan ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, kai ne Mai Tsarkin Nan na Allah!” 25 Amma Yesu ya tsawata masa, yana cewa: “Ka yi shuru, ka fito daga jikinsa!” 26 Bayan da ruhu mai ƙazantan ya sa mutumin farfaɗiya kuma ya yi ihu sosai, sai ya fita daga jikinsa. 27 Sai dukan mutanen suka yi mamaki sosai kuma suka soma tattaunawa da junansu suna cewa: “Mene ne wannan? Sabuwar koyarwa ce! Yana tsawata wa ruhohi masu ƙazanta, kuma suna yi masa biyayya.” 28 Sai labarinsa ya yaɗu da sauri a koꞌina a yankin Galili gabaki-ɗaya.
29 Da suka bar majamiꞌar, sai suka tafi gidan Siman da Andarawus, tare da Yaƙub da Yohanna. 30 Mamar matar Siman tana kwance tana fama da zazzaɓi, kuma nan take, suka gaya wa Yesu game da ita. 31 Sai ya je wajenta, ya kama hannunta, kuma ya taimaka mata ta tashi. Sai zazzaɓin ya bar ta kuma ta soma yi musu hidima.
32 Da yamma, bayan faɗuwar rana, sai mutane suka soma kawo masa dukan waɗanda suke rashin lafiya da masu aljanu; 33 kuma dukan mutanen garin suka taru a ƙofar gidan. 34 Sai ya warkar da mutane da yawa da suke rashin lafiya iri-iri, kuma ya fitar da aljanu da yawa. Amma yana hana aljanun magana, domin sun san cewa shi ne Kristi.*
35 Da sassafe, tun gari bai gama wayewa ba, Yesu ya tashi ya fita waje kuma ya tafi wani wuri don ya kasance shi kaɗai. Sai ya soma adduꞌa a wurin. 36 Amma Siman da waɗanda suke tare da shi suka je neman sa. 37 Da suka gan shi, sai suka ce masa: “Kowa yana neman ka.” 38 Amma Yesu ya ce musu: “Ku zo mu je wani wuri dabam, cikin garuruwa da ke kusa, domin in yi waꞌazi a wuraren ma. Dalilin da ya sa na zo ke nan.” 39 Sai ya je yana waꞌazi a cikin majamiꞌunsu da ke dukan yankin Galili kuma yana fitar da aljanu.
40 Sai wani kuturu ya zo wurin Yesu, ya durƙusa, yana roƙon sa cewa: “Idan kana so, za ka iya warkar da ni.” 41 Sai ya ji tausayin sa, kuma ya miƙa hannu, ya taɓa mutumin, ya ce masa: “E, ina so! Na warkar da kai.” 42 Nan da nan cutar kuturtar ta rabu da mutumin kuma ya zama mai tsabta. 43 Sai Yesu ya ja wa mutumin kunne kuma ya sallame shi nan take, 44 ya ce masa: “Kada ka gaya wa kowa, amma ka je ka nuna kanka a wurin firist, kuma ka miƙa hadaya don tsabtacewarka, yadda Musa ya ce a bayar, don su ga cewa an warkar da kai.” 45 Amma da mutumin ya tafi, sai ya soma yaɗa labarin sosai a koꞌina. Hakan ya sa Yesu ya daina shiga cikin gari inda mutane za su iya ganin sa, amma yakan zauna a bayan gari a wuraren da babu kowa. Duk da haka ma, mutane sun ci-gaba da zuwa wurinsa ta kowane gefe.