Zuwa ga Romawa
16 Ina gabatar muku da ꞌyarꞌuwarmu Fibi, wadda take hidima a ikilisiyar da ke Kankiriya, 2 domin ku marabce ta cikin Ubangiji a hanyar da ta dace da tsarkaka, kuma ku ba ta duk wani taimako da take bukata, domin ita ma ta taimaki mutane da yawa, har da ni.
3 Ku miƙa gaisuwata ga Biriskila da Akila, waɗanda abokan aikina ne cikin Kristi Yesu, 4 su ne suka sa rayukansu cikin haɗari saboda ni, kuma ba ni kaɗai ne nake gode musu ba, amma har da dukan ikilisiyoyin da ke ƙasashe dabam-dabam. 5 Ƙari ga haka, ku gai da mutanen ikilisiyar da ke gidansu. Ku gai da Afanitus wanda nake ƙauna, wanda yake cikin mutanen Asiya na farko da suka soma bin Kristi. 6 Ku gai da Maryamu, wadda ta yi aiki da ƙwazo domin ku. 7 Ku gai da Andaronikus da Yuniyas, waɗanda dangina ne kuma an ɗaure mu a kurkuku tare, su mutane ne da manzanni suka sani sosai, kuma waɗanda suka riga ni soma bin Kristi.
8 Ku miƙa gaisuwata ga Amfiliyatus, wanda nake ƙauna cikin Ubangiji. 9 Ku gai da Urbanus, abokin aikinmu cikin Kristi, da kuma wanda nake ƙauna, wato Sitakis. 10 Ku gai da Afalis, wanda Kristi ya amince da shi. Ku gai da mutanen gidan Aristobulus. 11 Ku gai da Hirudiyan, wanda dangina ne. Ku gai da mutanen gidan Narkisus, waɗanda suke bin Ubangiji. 12 Ku gai da Tirayifina da Tirayifosa, matan da suke yin aikin Ubangiji da ƙwazo. Ku gai da Fasis, wadda nake ƙauna, gama ta yi aikin Ubangiji da ƙwazo. 13 Ku gai da Rufus, wanda Ubangiji ya zaɓa, da kuma mamarsa, wadda take kamar mama a gare ni. 14 Ku gai da Asinkiritus, da Filigon, da Hamis, da Faturobas, da Hermas, da ꞌyanꞌuwa da suke tare da su. 15 Ku gai da Filologus da Juliya, da Niriyus da ꞌyarꞌuwarsa, da Olimfas, da kuma dukan tsarkaka da suke tare da su. 16 Ku gai da juna da sumba mai tsarki. Dukan ikilisiyoyin Kristi sun gaishe ku.
17 Ina roƙon ku ꞌyanꞌuwa, ku yi hankali da waɗanda suke jawo rabuwa da kuma abubuwan sa mutane tuntuɓe, domin hakan ya saɓa wa abubuwan da kuka koya, ku guje su. 18 Gama irin mutanen nan, ba bayin Ubangijinmu Kristi ba ne, amma bayi ne ga cikinsu. Ta wurin yaudara da kuma daɗin baki, suna ruɗin masu tunani kamar yara. 19 Dukan mutane sun san cewa ku masu yin biyayya ne, saboda haka, ina farin ciki domin ku. Amma ina so ku zama masu hikima idan ya zo ga abu mai kyau, kuma ku zama ba ruwanku da mugunta. 20 Ba da daɗewa ba, Allah mai ba da salama zai murƙushe Shaiɗan a ƙarƙashin ƙafafunku. Bari alherin Ubangijinmu Yesu ya kasance tare da ku.
21 Timoti abokin aikina, ya gaishe ku, haka ma Lushiyus, da Jason, da Sosifata, waɗanda dangina ne, suna gaisuwa.
22 Ni, Tartiyus, mai rubuta wannan wasiƙar, na gaishe ku cikin Ubangiji.
23 Gayus, wanda ya karɓe ni a gidansa, wanda dukan ikilisiyar sukan yi taro a gidansa, ya gaishe ku. Erastus, wanda shi ne maꞌajin birnin, ya gaishe ku, ɗanꞌuwansa Kwartus ma, ya gaishe ku. 24* ——
25 Allah zai iya yin amfani da labari mai daɗi da nake shelar sa, da waꞌazi game da Yesu Kristi, ya sa ku tsaya da ƙarfi. Labari mai daɗin yana da alaƙa da asiri mai tsarki da Allah ya bayyana, wannan asirin ya daɗe yana nan a ɓoye. 26 Amma yanzu Allah ya bayyana mana shi, kuma ya yi hakan ta annabcin da ke cikin Nassosi. Bisa ga umurnin Allah madawwami, an bayyana asirin ga dukan alꞌummai domin su ba da gaskiya, su kuma yi biyayya. 27 Bari Allah, wanda shi kaɗai ne mai hikima, ya karɓi ɗaukaka ta wurin Yesu Kristi har abada. Amin.