Ta Hannun Markus
2 Amma, bayan ꞌyan kwanaki, Yesu ya sake komawa Kafarnahum, sai labari ya yaɗu cewa yana gida. 2 Sai mutane da yawa suka taru, har ba sauran wuri, ko a bakin ƙofa ma, kuma ya soma yi musu waꞌazin kalmar Allah. 3 Sai suka kawo masa wani mutum da jikinsa ya shanye, kuma mutane huɗu ne suke ɗauke da shi. 4 Amma sun kasa shigar da shi a inda Yesu yake saboda jamaꞌa, sai suka buɗe rufin gidan daidai inda Yesu yake. Bayan da suka huda rami, sai suka saukar da mutumin kwance a kan tabarma.* 5 Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa mutumin da jikinsa ya shanye: “Ɗana, an gafarta zunubanka.” 6 Wasu marubuta suna wurin, suna tunani a zuciyarsu cewa: 7 “Me ya sa mutumin nan yake magana haka? Yana saɓo ne. Wane ne zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?” 8 Amma nan da nan, Yesu ya gane abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya ce musu: “Me ya sa kuke irin tunanin nan a zuciyarku? 9 Wanne ne ya fi sauƙi, a ce wa mutumin da jikinsa ya shanye, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuma a ce, ‘Ka tashi, ka ɗauki tabarmarka ka yi tafiya’? 10 Amma domin ku san cewa Ɗan mutum yana da ikon gafarta zunubai a duniya—” sai ya ce wa mutumin nan da jikinsa ya shanye: 11 “Ina gaya maka, Ka tashi, ka ɗauki tabarmarka, ka tafi gida.” 12 Sai ya tashi, kuma nan da nan ya ɗauki tabarmarsa, ya fita a gaban dukansu. Sai dukan mutanen suka yi mamaki sosai, kuma suka ɗaukaka Allah, suna cewa: “Ba mu taɓa ganin abu kamar haka ba.”
13 Ya sake fita zuwa bakin teku, sai dukan jamaꞌa suka yi ta zuwa wurinsa kuma ya soma koyar da su. 14 Saꞌad da yake wucewa, sai ya ga Lawi* ɗan Alfiyus yana zaune a ofishin karɓan haraji, sai ya ce masa: “Ka zama mabiyina.” Nan da nan sai ya tashi ya bi Yesu. 15 Daga baya, saꞌad da Yesu yake cin abinci a gidan Lawi, sai mutane da yawa masu karɓan haraji, da masu zunubi, suka zo suna cin abinci tare da Yesu da almajiransa, domin da yawa daga cikinsu ne suke bin Yesu. 16 Amma da marubutan Farisiyawa suka ga cewa yana cin abinci tare da masu zunubi, da masu karɓan haraji, sai suka ce wa almajiransa: “Me haka? Yana cin abinci tare da masu karɓan haraji da masu zunubi.” 17 Da Yesu ya ji hakan, sai ya ce musu: “Masu ƙoshin lafiya ba sa bukatar likita, amma masu rashin lafiya suna bukatar sa. Na zo ne in kira masu zunubi, ba masu adalci ba.”
18 Almajiran Yohanna da Farisiyawa suna yin azumi. Sai suka zo wurin Yesu suka ce masa: “Me ya sa mu almajiran Yohanna da almajiran Farisiyawa muke yin azumi, amma almajiranka ba sa yin azumi?” 19 Sai Yesu ya ce musu: “Abokan ango ba su da dalilin yin azumi saꞌad da angon yake tare da su, ko ba haka ba? Muddin angon yana tare da su, ba sa bukatar yin azumi. 20 Amma lokaci na zuwa da za a ɗauke angon daga wurinsu, a ranar ce za su yi azumi. 21 Ba wanda zai yi fācin tsohuwar riga da sabon yadi. In ya yi hakan, sabon yadin zai sa tsohuwar rigar ta yage, yagewar ma za ta fi ta dā. 22 Kuma babu wanda yake zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna.* Idan ya yi hakan, ruwan inabin zai fashe salkunan, ruwan inabin zai zube, kuma salkunan za su lalace. Amma akan zuba sabon ruwan inabi a cikin sababbin salkuna.”
23 Yayin da Yesu yake wucewa ta gonakin alkama a Ranar Assabaci, sai almajiransa suka fara tsinka alkama yayin da suke tafiya. 24 Sai Farisiyawa suka ce masa: “Duba! Me ya sa almajiranka suke yin abin da Doka* ta hana yi a Ranar Assabaci?” 25 Sai ya ce musu: “Shin ba ku taɓa karanta abin da Dauda ya yi saꞌad da ba shi da abinci, kuma shi da mutanen da suke tare da shi suke jin yunwa ba? 26 A labarin Abiyata wanda babban firist ne, ba ku karanta yadda Dauda ya shiga gidan Allah kuma ya ci burodin da aka miƙa wa Allah, wanda bai kamata wani ya ci ba sai firistoci kaɗai, har ya ba da wasu burodin ga waɗanda suke tare da shi?” 27 Sai ya ce musu: “An yi Ranar Assabaci domin mutum ne, ba a yi mutum domin Ranar Assabaci ba. 28 Don haka, Ɗan mutum Ubangiji ne har ma da na Ranar Assabaci.”