Zuwa ga Romawa
4 To, me za mu ce ita ce ribar da Ibrahim kakan kakanninmu* ya samu? 2 Alal misali, da ayyukan Ibrahim ne sun sa an ɗauke shi a matsayin mai adalci, da zai samu dalilin yin taƙama, amma taƙamarsa ba za ta zama don Allah ba. 3 Gama mene ne nassi ya ce? “Ibrahim ya ba da gaskiya ga Jehobah,* kuma hakan ya sa an ɗauke shi a matsayin mai adalci.” 4 Mutumin da yake aiki, albashin da ake biyan sa ba alheri ne aka yi masa ba amma ladan aikinsa ne. 5 A wani ɓangaren kuma, mutumin da bai dogara ga ayyukansa ba amma ya ba da gaskiya ga Wanda yake ɗaukan mai mugunta a matsayin mai adalci, za a ɗauke shi a matsayin mai adalci don bangaskiyarsa. 6 Wannan shi ne abin da Dauda yake nufi, saꞌad da ya yi magana game da farin ciki da wani mutum ya yi domin Allah ya ce da shi mai adalci, ba domin ayyukan da mutumin ya yi ba, cewa: 7 “Masu farin ciki ne mutanen da Allah ya gafarta musu muguntarsu, da waɗanda aka gafarta musu zunubansu, 8 mai farin ciki ne mutumin da Jehobah* ba zai taɓa riƙe zunubinsa a zuciya ba.”
9 Shin waɗanda suka yi kaciya ne kaɗai suke samun farin cikin nan ko kuwa har ma da waɗanda ba su yi kaciya ba? Domin mun ce: “Bangaskiyar Ibrahim ce ta sa Allah ya ɗauke shi a matsayin mai adalci.” 10 To, a wane lokaci ne aka ce da shi mai adalci? Lokacin da ya yi kaciya ne ko kuma lokacin da bai yi kaciya ba? Ai tun ba a yi masa kaciya ba ne. 11 Kuma ya karɓi alama, wato kaciya, wadda ta tabbatar da adalcin da yake da shi ta wurin bangaskiyar da yake da ita tun bai yi kaciya ba. Ta hakan zai zama uba ga dukan waɗanda suke ba da gaskiya ko da yake ba a yi musu kaciya ba, domin a ɗauke su a matsayin masu adalci; 12 kuma ya iya zama uba ga yaran da aka yi musu kaciya, ba ga waɗanda aka yi musu kaciya kawai ba, amma har ga waɗanda suka ba da gaskiya kamar yadda babanmu Ibrahim ya yi tun kafin a yi masa kaciya.
13 Gama ba ta wurin doka ce aka yi wa Ibrahim ko kuma ꞌyaꞌyansa alkawari cewa za su gāji sabuwar duniya ba, amma domin adalci da ake samuwa ta wurin bangaskiya ne. 14 Idan waɗanda suke bin doka ne za su gāji alkawarin da aka yi, bangaskiya ba ta da amfani kuma alkawarin ya zama banza ke nan. 15 A gaskiya, Doka tana jawo fushi, amma a duk inda babu doka, babu rashin biyayya.
16 Shi ya sa ta wurin bangaskiya ne aka samu alkawarin, domin ya zama bisa ga alherin Allah, ta hakan za a tabbatar da alkawarin ga dukan yaran Ibrahim ba ga waɗanda suke bin Doka kawai ba, amma har ga waɗanda suke da bangaskiya kamar na Ibrahim wanda shi ne baban dukanmu. 17 (Hakan ya yi daidai da abin da aka rubuta cewa: “Na naɗa ka a matsayin baba ga alꞌummai da yawa.”) Ibrahim babanmu ne a gaban Allah, wanda shi Ibrahim ya ba da gaskiya a gare shi. Wannan Allah ne da ke ta da matattu, shi ne kuma yake kiran abubuwan da ba su kasance ba su zama kamar sun kasance.* 18 Ko da yake bai da dalilin kasancewa da bege, begensa ne ya sa ya kasance da bangaskiya cewa zai zama baban alꞌummai da yawa, bisa ga abin da aka faɗa cewa: “Haka zuriyarka za ta zama.” 19 Ya yi tunani a kan jikinsa wanda ya kusan mutuwa, (da yake a lokacin ya kusan shekara ɗari), da kuma Saratu wadda ta wuce shekarun haifuwa, amma bangaskiyarsa ba ta yi sanyi ba. 20 Domin alkawarin da Allah ya yi masa, Ibrahim bai nuna rashin bangaskiya ba; amma bangaskiyarsa ta ƙarfafa shi, kuma ya ɗaukaka Allah. 21 Ƙari ga haka, yana cike da tabbaci cewa Allah zai cika alkawarin da ya yi masa. 22 Hakan ya sa “Allah ya ɗauke shi a matsayin mai adalci.”
23 Amma, furucin nan “Allah ya ɗauke shi a matsayin mai adalci” ba don Ibrahim kaɗai aka rubuta ba, 24 amma an rubuta ne domin mu ma, za a ɗauke mu a matsayin masu adalci ma, domin mun ba da gaskiya ga Allah wanda ya ta da Yesu Ubangijinmu daga mutuwa. 25 Allah ya bari a kashe Yesu domin zunubanmu, kuma ya ta da shi domin ya ɗauke mu a matsayin masu adalci.