Ta Hannun Markus
10 Daga wurin ya tashi zuwa iyakar Yahudiya a ƙetaren Kogin Jodan, sai jamaꞌar suka sake taruwa a inda yake. Sai ya soma koyar da su kamar yadda ya saba. 2 Sai Farisiyawa suka zo da niyyar gwada shi, kuma suka tambaye shi ko ya dace bisa Doka* mutum ya kashe aurensa. 3 Sai Yesu ya amsa musu ya ce: “Wane umurni ne Musa ya ba ku?” 4 Sai suka ce: “Musa ya ce a ba wa matar takardar kashe aure, saꞌan nan a sallame ta.” 5 Sai Yesu ya ce musu: “Saboda taurin zuciyarku ne Musa ya rubuta muku wannan umurnin. 6 Amma, tun daga farkon halitta, ‘Ya halicce su namiji da ta mace. 7 Saboda haka, mutum zai bar babansa da mamarsa, 8 su biyun za su zama jiki ɗaya,’ ta hakan su ba mutum biyu ba kuma, amma mutum ɗaya ne. 9 Don haka, abin da Allah ya haɗa, kada wani mutum ya raba.” 10 Saꞌad da suka sake shiga gida, sai almajiransa suka soma yi masa tambaya a kan batun. 11 Ya ce musu: “Duk wanda ya kashe aurensa* ya kuma auri wata, ya yi zina, kuma ya ci amanar matarsa. 12 Kuma idan mace ta kashe aurenta* ta sake auran wani, ta yi zina.”
13 Sai mutane suka soma kawo wa Yesu yara ƙanana don ya sa hannunsa a kansu, amma almajiransa suka tsawata wa mutanen. 14 Da Yesu ya ga hakan, sai ya yi fushi kuma ya ce musu: “Ku bar ƙananan yaran su zo wurina kuma kada ku hana su, domin Mulkin Allah na irinsu ne. 15 A gaskiya ina gaya muku, duk wanda bai karɓi Mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga cikinsa ba.” 16 Sai ya ɗauki ƙananan yaran a hannayensa, ya sa hannu a kansu, yana yi musu albarka.
17 Da Yesu yake tafiya, sai wani mutum ya zo da gudu, ya durƙusa a gabansa kuma ya tambaye shi cewa: “Malam Nagari, me zan yi don in gāji rai na har abada?” 18 Sai Yesu ya ce masa: “Me ya sa ka kira ni nagari? Babu wani nagari, sai Allah kaɗai. 19 Ka san abin da ke cikin doka, wato: ‘Kada ka yi kisa, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaidar ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama babanka da mamarka.’” 20 Mutumin ya ce masa: “Malam, ai ina yin dukan abubuwan nan tun ina ƙarami.” 21 Yesu ya dube shi kuma ya ƙaunace shi, sai ya ce masa, “Abu ɗaya ne tak ka rasa: Ka je ka sayar da dukan abubuwan da kake da su, ka ba wa talakawa, za ka sami dukiya a sama; sai ka zo ka bi ni.” 22 Amma mutumin bai ji daɗin amsar da Yesu ya ba shi ba, kuma ya tafi yana baƙin ciki, domin yana da dukiya mai yawa.
23 Bayan da Yesu ya dubi mutanen da ke wurin, sai ya ce wa almajiransa: “Zai yi ma waɗanda suke da kuɗi wuya su shiga Mulkin Allah!” 24 Amma almajiransa sun yi mamaki don abin da ya faɗa. Sai Yesu ya ce musu: “Yarana, yana da wuya sosai a shiga Mulkin Allah! 25 Zai fi wa raƙumi sauƙi ya bi ta ramin allura da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.” 26 Sai suka ƙara yin mamaki kuma suka ce masa:* “Wane ne zai iya samun ceto?” 27 Sai Yesu ya kalle su, kuma ya ce: “A wurin mutane kam, ba zai yiwu ba. Amma ba haka yake da Allah ba, domin a wurin Allah kowane abu zai yiwu.” 28 Sai Bitrus ya ce masa: “Ga shi, mun bar kome mun bi ka.” 29 Sai Yesu ya ce: “A gaskiya ina gaya muku, babu wanda ya bar gida, ko ꞌyanꞌuwa maza, ko ꞌyanꞌuwa mata, ko mama, ko baba, ko yara, ko gonaki saboda ni da kuma labari mai daɗi, 30 wanda ba zai sami gidaje, da ꞌyanꞌuwa maza, da ꞌyanꞌuwa mata, da iyaye mata, da yara, da gonaki, fiye da sau ɗari, tare da tsanantawa a wannan zamanin ba. Kuma a zamani mai zuwa,* zai sami rai na har abada. 31 Amma mutane da yawa waɗanda suke na farko za su zama na ƙarshe, na ƙarshe kuma za su zama na farko.”
32 Saꞌad da suke haurawa zuwa Urushalima, Yesu yana tafiya a gabansu, kuma sun yi mamaki sosai, amma waɗanda suke bin su suka soma jin tsoro. Sai Yesu ya sake jan almajiransa goma sha biyu gefe, kuma ya soma gaya musu abubuwan da za su faru da shi ba da daɗewa ba, cewa: 33 “Ga shi! Za mu haura zuwa Urushalima, kuma za a ba da Ɗan mutum a hannun manyan firistoci da marubuta. Za su yanke masa hukuncin kisa, saꞌan nan su ba da shi ga mutanen alꞌummai, 34 kuma za su yi masa baꞌa, su tofa masa miyau, su yi masa bulala kuma su kashe shi, amma bayan kwana uku, zai tashi.”
35 Sai Yaƙub da Yohanna ꞌyaꞌyan Zabadi suka zo wurinsa suka ce masa: “Malam, muna so ka yi mana duk abin da muka roƙe ka.” 36 Sai ya ce musu: “Mene ne kuke so in yi muku?” 37 Suka ce masa: “Saꞌad da ka shiga ɗaukakarka, ka bar ɗayanmu ya zauna a hannun damanka, ɗaya kuma a hannun hagunka.” 38 Amma Yesu ya ce musu: “Ba ku san abin da kuke roƙa ba. Za ku iya shan abin da ke cikin kofi da nake sha? Ko kuma za ku iya yin baftisma da irin baftismar da ake yi mini?” 39 Sai suka ce masa: “Za mu iya.” Sai Yesu ya ce musu: “Lallai za ku sha abin da nake sha, kuma za a yi muku baftisma da irin baftismar da ake yi mini. 40 Amma zama a hannun damana ko haguna, ba ni nake da ikon bayarwa ba. Wannan matsayi ne na waɗanda aka shirya musu.”
41 Da sauran manzanni goma suka ji abin da ya faru, sai suka yi fushi sosai da Yaƙub da Yohanna. 42 Amma Yesu ya kira su, ya ce musu: “Kun san cewa shugabannin alꞌummai suna wahalar da waɗanda suke mulki a kansu kuma manyansu ma suna nuna musu iko. 43 Kada hakan ya faru a tsakaninku; amma duk wanda yake so ya zama babba a cikinku, dole ne ya zama mai yi muku hidima. 44 Kuma duk wanda yake so ya zama na farko a tsakaninku, dole ne ya zama bawanku duka. 45 Gama ko Ɗan mutum ma ya zo, ba domin a yi masa hidima ba, amma domin ya yi hidima, kuma ya ba da ransa a matsayin fansa don ya ceci mutane da yawa.”
46 Sai suka shiga cikin Jeriko. Amma yayin da shi da almajiransa da mutane da yawa suke barin Jeriko, sai ga Bartimawus (ɗan Timawus), wanda makaho ne, yana zaune a bakin hanya yana bara. 47 Saꞌad da ya ji cewa Yesu mutumin Nazaret ne yake wucewa, sai ya ɗaga murya yana cewa: “Yesu, Ɗan Dauda, ka ji tausayi na!” 48 Sai mutane da yawa suka soma tsawata masa, suna ce masa ya yi shuru. Amma sai ƙara ɗaga murya yake yi, yana cewa: “Ɗan Dauda, ka ji tausayi na!” 49 Sai Yesu ya tsaya ya ce: “Ku kira mini shi.” Sai suka kira makahon, suka ce masa: “Kada ka ji tsoro! Ka tashi. Yesu yana kiran ka.” 50 Sai ya yar da mayafinsa kuma ya yi tsalle ya je wurin Yesu. 51 Sai Yesu ya ce masa: “Me kake so in yi maka?” Sai makahon ya ce: “Malam,* ina so in soma gani.” 52 Sai Yesu ya ce masa: “Ka tafi. Bangaskiyarka ta warkar da kai.” Sai nan da nan mutumin ya soma gani, kuma ya soma bin Yesu.