Ta Hannun Luka
23 Sai dukan jamaꞌar suka tashi suka kai shi wurin Bilatus. 2 Sai suka soma zargin sa suna cewa: “Mun ga cewa mutumin nan yana zuga mutane su ƙi yi wa gwamnati biyayya, yana hana biyan haraji ga Kaisar, kuma yana cewa shi ne Kristi sarki.” 3 Sai Bilatus ya tambaye shi cewa: “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Sai Yesu ya amsa ya ce: “Kai ma da kanka ka faɗi hakan.” 4 Sai Bilatus ya gaya wa manyan firistoci da jamaꞌar cewa: “Ban sami mutumin nan da wani laifi ba.” 5 Amma suka nace da cewa: “Yana jawo tashin hankali tsakanin mutane ta wajen koyarwarsa a dukan yankin Yahudiya, ya fara daga Galili har ya iso nan.” 6 Da Bilatus ya ji hakan, sai ya yi tambaya ko Yesu mutumin Galili ne. 7 Bayan da Bilatus ya ji cewa Yesu ya fito daga yankin da Hirudus* yake mulki, sai ya aika shi zuwa wurin Hirudus wanda shi ma ya zo Urushalima a lokacin.
8 Saꞌad da Hirudus ya ga Yesu, ya yi farin ciki sosai. Ya daɗe yana so ya ga Yesu domin ya ji labari sosai game da shi, kuma yana sa rai cewa zai ga wasu alamun da Yesu zai yi. 9 Sai ya soma yi wa Yesu tambayoyi da yawa, amma Yesu bai amsa masa ba. 10 Manyan firistoci da marubuta kuwa suna ta tashi tsaye suna ta zargin sa. 11 Sai Hirudus da sojojinsa suka rena shi, kuma Hirudus ya yi masa baꞌa ta wajen saka masa riga mai kyau sosai, sai ya mai da shi zuwa wurin Bilatus. 12 A ranar, Hirudus da Bilatus suka zama abokai, domin kafin lokacin suna gāba da juna.
13 Sai Bilatus ya tara manyan firistoci, da shugabanni, da jamaꞌa duka 14 kuma ya ce musu: “Kun kawo mini mutumin nan kuma kun zarge shi da zuga mutane su yi rashin biyayya ga gwamnati. Ga shi, na bincika wannan mutumin a gabanku amma ban kama shi da laifin da kuka ce ya yi ba. 15 Ko Hirudus ma bai kama shi da laifi ba, kuma ya mai da shi zuwa wurinmu, don abin da ya yi bai kai a kashe shi ba. 16 Saboda haka, zan yi masa bulala kuma in sake shi.” 17* —— 18 Amma dukan jamaꞌar suka ɗaga murya suka ce: “Ka kashe mutumin nan kuma ka sako mana Barabbas!” 19 (Dama an tsare Barabbas ne domin tawaye da kuma kisan da aka yi a birnin.) 20 Sai Bilatus ya sake yi musu magana domin yana so ya saki Yesu. 21 Sai suka soma ihu suna cewa: “A rataye shi a kan gungume! A rataye shi a kan gungume!”* 22 A karo na uku Bilatus ya ce musu: “Me ya sa? Wane laifi ne mutumin nan ya yi? Ban same shi da wani laifin da ya kai a kashe shi ba. Saboda haka, zan yi masa bulala kuma in sake shi.” 23 Da jin haka, sai suka nace da babbar murya suna cewa a kashe shi,* a ƙarshe dai suka ci nasara. 24 Sai Bilatus ya yanke shawara cewa a yi abin da mutanen suke so. 25 Sai ya saki mutumin da suka ce a sako musu, wanda aka sa a kurkuku saboda tawaye da kuma kisa, amma ya ba da Yesu gare su don su yi abin da suke so.
26 Yayin da suke tafiya da Yesu, sai suka kama wani mutumin Sayirin mai suna Siman, wanda yake dawowa daga ƙauye, sai suka sa shi ya ɗauki gungumen azabar* kuma ya bi bayan Yesu. 27 Mutane da yawa suna bin sa a baya, tare da matan da suka ci-gaba da yin baƙin ciki da kuka domin sa. 28 Amma Yesu ya juya baya ya kalli matan ya ce: “Matan Urushalima, ku daina kuka saboda ni. Amma ku yi kuka don kanku da kuma yaranku. 29 Ga shi, kwanaki suna zuwa saꞌad da mutane za su ce, ‘Masu farin ciki ne matan da ba sa iya ɗaukan ciki, da waɗanda ba su haifu ba, da kuma waɗanda ba su shayar ba!’ 30 Saꞌan nan za su soma ce wa manyan tuddai, ‘Ku faɗo a kanmu!’ za su kuma ce wa ƙananan tuddai, ‘Ku rufe mu!’ 31 Idan sun yi abubuwan nan saꞌad da itace yake ɗanye, mene ne zai faru saꞌad da ya bushe?”
32 Akwai kuma mutane biyu masu laifi da aka tafi da su don a kashe su tare da Yesu. 33 Saꞌad da suka kai wurin da ake kira Ƙoƙon Kai, sai aka rataye shi a kan gungume tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun hagunsa, ɗaya kuma a hannun damansa. 34 Amma Yesu yana cewa: “Uba ka gafarta musu, don ba su san abin da suke yi ba.” Ƙari ga haka, sun jefa ƙuriꞌa don su rarraba rigunansa. 35 Sai mutanen suka tsaya suna kallo. Amma shugabannin suna masa baꞌa suna cewa: “Ya ceci wasu; bari ya ceci kansa mana idan shi ne Kristi na Allah, Wanda Aka Zaɓa.” 36 Har sojojin ma sun yi masa baꞌa, kuma suka hau suka ba shi ruwan inabi da ya yi tsami, 37 suna cewa: “Idan kai ne Sarkin Yahudawa, ka ceci kanka.” 38 Sun kuma rubuta a saman gungumen cewa: “Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.”
39 Saꞌan nan ɗaya daga cikin masu laifin da aka rataye su tare ya soma yi masa baƙar magana yana cewa: “Ba kai ne Kristi ba? Ka ceci kanka har da mu!” 40 Sai ɗayan ya tsawata masa yana cewa: “Ba ka jin tsoron Allah, kai da ka sami hukunci daidai da shi? 41 Mu kam daidai aka yi mana, domin muna samun ladan abin da muka yi ne; amma wannan mutumin bai yi laifi ba.” 42 Sai ya ce: “Yesu, ka tuna da ni saꞌad da ka shiga cikin Mulkinka.” 43 Sai Yesu ya ce masa: “A gaskiya ina gaya maka yau, za ka kasance tare da ni a Aljanna.”
44 A lokacin, wajen ƙarfe goma sha biyu na rana* ne, sai duhu ya rufe koꞌina a ƙasar har zuwa wajen ƙarfe uku na yamma,* 45 domin rana ta daina haske. Sai labulen da ke haikali ya yage a tsakiya, daga sama zuwa ƙasa. 46 Sai Yesu ya yi ihu da babbar murya ya ce: “Uba, na miƙa ruhuna a cikin hannayenka.” Bayan da ya faɗi hakan, sai ya mutu.* 47 Domin ya ga abin da ya faru, sai jamiꞌin sojan ya soma ɗaukaka Allah yana cewa: “A gaskiya, wannan mutum mai adalci ne.” 48 Saꞌad da jamaꞌa da suka zo kallo suka ga abubuwan da suka faru, sai suka koma gida suna buga ƙirji don baƙin ciki. 49 Kuma dukan waɗanda suka san shi sun tsaya daga nesa. Ƙari ga haka, matan da suka bi shi daga Galili suna wurin kuma sun ga abubuwan nan.
50 Akwai wani mutum mai suna Yusufu, shi ɗan Majalisa* ne, mutumin kirki ne kuma mai adalci. 51 (Mutumin nan bai yarda da abin da suka ƙulla da abin da suka yi ba.) Shi daga Arimatiya ne, wani gari a Yahudiya, kuma yana jiran Mulkin Allah. 52 Mutumin nan ya je wurin Bilatus kuma ya roƙa a ba shi gawar Yesu. 53 Sai ya saukar da gawar Yesu, ya naɗe shi da yadin lilin mai kyau, kuma ya sa gawar a cikin kabari da aka tona a dutse, wanda ba a taɓa binne kowa a ciki ba. 54 Ranar, Ranar Shiri* ce, kuma an kusa a soma Assabaci. 55 Matan da suka bi Yesu daga Galili sun bi bayan Yusufu kuma sun kalli kabarin Yesu da kuma yadda aka kwantar da gawarsa. 56 Sai suka koma suka shirya kayan ƙamshi da mān ƙamshi. Amma sun huta a Ranar Assabaci bisa ga doka.