Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • sp pp. 19-22
  • Aljannu Suna Ƙarfafa Yin Tawaye da Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Aljannu Suna Ƙarfafa Yin Tawaye da Allah
  • Ruhohin Matattu—Zasu Taimake Ka ne ko Kuwa Zasu Yi Maka Barna? Sun Wanzu Kuwa Da Gaske?
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Allah ya Hana Ayukan Sihiri
  • Jehobah Yana Taimaka Mana Mu Yi Tsayayya da Mugayen Ruhohi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Su Waye ne Mala’iku Kuma Wane Aiki Suke Yi?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Halittun Ruhu—Yadda Suke Shafanmu
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Kana Tsoron Matattu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Ruhohin Matattu—Zasu Taimake Ka ne ko Kuwa Zasu Yi Maka Barna? Sun Wanzu Kuwa Da Gaske?
sp pp. 19-22

Aljannu Suna Ƙarfafa Yin Tawaye da Allah

Amma me yasa Shaitan da   aljannunsa suke kokuwa   haka don su ruɗas da mu  tane? Domin suna son mu haɗa da su cikin tawayensu. Suna son mu bauta masu. Suna son mu gaskata ƙaryansu kuma mu yi abubuwan da Jehovah baya so. Yawancin waɗannan suna kunshe da al’adu da suke shafe matattu.

Mutuwan wani ƙaunatacce dai abu ne na ɓacinzuciya ƙwarai, kuma daidai ne mutum ya nuna ɓacin ransa. Bayan mutuwan abokinsa Li’azaru, Yesu ya “yi kuka.”​—⁠Yohanna 11:35.

Akwai al’adu dayawa da suke haɗe da mutuwa, kuma waɗannan sun bambanta a duk duniya. Wasu fa, ba su yi gāba da ka’idodin Littafi Mai-tsarki. Amma dai, wasu al’adun an kafa su bisa ra’ayin cewa matattu suna da rai kuma suna iya ganin masu rai. Jana’iza, kuka mara-iyaka, da kuma bikin jana’iza mai-girma duk suna da tushen su cikin ƙin ɓata rai ma ruhohin matattu ne. Amma da shike matattu basu “san komi ba,” waɗanda suke yin waɗannan al’adun gabatarda ƙaryan Shaitan suke yi.​—⁠Mai-Wa’azi 9:⁠5.

Wasu al’adu ko kuwa bukkukuwa sun taso daga gaskatawar cewa matattu suna bukatar taimako daga masu-rai kuma cewa zasu yi ɓarna ga masu-rai in basu yi hakan ba. A wasu ƙasashe ana yin biki da hadayu kwanaki 40 ko kuwa shekara ɗaya bayan mutuwar mutumen. Ana yin haka da jin cewa zai taimake mataccen ya ‘haye zuwa’ cikin lardi na ruhu. Wani sanannen al’ada kuma shine na bada abinci da abin sha ga matattu.

Waɗannan abubuwan ba daidai ba ne gama suna gabatadda ƙaryace-ƙaryacen Shaitan game da matattu ne. Ashe Jehovah zai yarda da yin rabonmu cikin wani al’ada da an kafa bisa koyaswan aljannu? Ko kaɗan!​—⁠2 Korinthiyawa 6:​14-⁠18.

Bayin Allah na gaskiya basu a rabo cikin al’adun da ke goyon bayan ƙaryace-ƙaryacen Shaitan. Maimakon haka, suna taimaka ma waɗanda suke da rai da kuma ta’azantadda su cikin ƙauna. Sun san da cewa idan mutum ya mutu, Jehovah ne kaɗai zai taimake shi.​—⁠Ayuba 14:​14, 15.

Allah ya Hana Ayukan Sihiri

Wasu mutane sukan yi saɗu da aljannu kai tsaye ko kuwa ta wurin mai-mabiya. Ana kiran wannan sihiri. Voodoo, maita, duba, da faɗin gaba, da kuma neman sani game da matattu duka fasalolin sihiri ne.

Littafi Mai-tsarki ya hana waɗannan abubuwa, yana cewa: “Daga cikinka ba za a iske wanda yana . . . yin istihara, ko mai-yin duba, ko mai-waibuwa, ko mai-sihiri, ko mai-arwa, ko mai-magana da mai-mabiya, ko mai-maita, ko mai-sha’ani da matattu. Gama wanda ya aika waɗannan al’amura duka abin ƙyama ne ga Ubangiji [Jehovah].”​—⁠Kubawar Shari’a 18:​10-⁠12.

Don minene kam Jehovah yake galgadas da mu haka da tsanani game da irin al’adun nan?

Domin lafiyar kanmu fa, Jehovah yake galgaɗas da mu game da dukan fasalin sihiri. Yana ƙaunar mutane da kuma kula da su, kuma ya sani cewa waɗanda suka yi sha’ani da aljannu tilas ne su wahalu.

Ɗaya daga cikin irin mutanen nan shine Nilda, wadda mai-mabiya ce a Brazil. Aljannun sun maida ita abin tsiya. Ta labarta cewa: “Ruhohin . . . sun mallake ni, suna motsa zuwa ko’ina. Ina sauyawa tsakanin rai da mutuwa, har kuma na kamu taɓuwa. Aljannun sun tsananta mani ƙwarai har da hakan ya taɓe jijiyoyina. Na kuwa soma shaye-shaye da shan taba kullum kamar magani. Wannan kuwa ya ci gaba haka na shekaru da dama.”

Akwana a tashi fa, da taimakon Jehovah da Shaidunsa a duniya, Nilda ta yantu daga tasirin aljannu kuma yanzu tana rayuwa lafiyayye, mai-tsarki. Ta ce: “Ina fa shawarci kowa, kada ko na ɗan lokaci, ya shaƙu da [miyagun] ruhohi.”

[Hoto a shafi na 19]

An kafa wasu al’adu bisa ƙaryan cewa matattu suna ganin mu

[Hoto a shafi na 20]

An kafa wasu al’adun bisa ƙaryan cewa matattu suna bukatar taimakonmu

[Hoto a shafi na 21]

Allah yana gāba da miyagun abubuwa nan. Yana bukatar cikakken sujada.​—⁠Fitowa 20:5

[Hotuna a shafi na 22]

Waɗanda suke ayukan sihiri sau tari suna wahaluwa. Sukan yi hasarar gidansu, yancinsu, har da ransu ma

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba