Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • we pp. 3-6
  • “It Can’t Be True!”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “It Can’t Be True!”
  • Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Da Akwai Bege na Ƙwarai
  • Begen Tashin Matattu Tabbacacce Ne!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Za A Yi Tashin Matattu!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Mai Ta da Matattu Luka 7:11-15
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Begen Tashin Matattu Yana Da iko
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Dubi Ƙari
Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
we pp. 3-6

“Ba Gaskiya Ba Ne!”

WANI mutumen New York (U.S.A.) ya labarta haka: “Ɗana Jonathan yana ziyartan abokansa da suke mil kaza daga wurinsu. Matata, Valentina, ba ta son ya tafi wurin nan. Tana jin tsoron motocin kan hanyar. Amma yana son na’urorin lantarki, kuma abokansa suna da shagon da zai samu fahimi na ƙwarai. Ina gida a yammancin Manhattan, New York. Matata kuma ta yi tafiya garin ziyarce iyalinta a Puerto Rico. ‘Jonathan zai dawo gida ba da jimawa ba,’ haka nike tunani. Sai kuma aka kaɗa kararrawar kofar. ‘Lallai shine wannan.’ Ba shi ba ne. Yan sanda ne da kuma yan jinyar gaggawa. ‘Ka san wannan lasisin motar?’ yan sandar suka tambaya. ‘I, na ɗana ne, Jonathan.’ ‘Muna da mumunan labari gareka. An yi wata hatsari, kuma . . . ɗanka, . . . ɗanka ya mutu a ciki.’ Martani na na fari shine, ‘Ba gaskiya ba ne!’ Aukuwan nan ya buɗe wata miƙi da har ila tana kan warƙewa, shekaru da dama bayan haka.”

Wani uba cikin Barcelona (Spain) ya rubuta haka: “Can cikin Spain da aka san da shi a shekarun 1960, mun zama iyali ne mai-farinciki. Da akwai María, matata, da yaranmu uku, David, Paquito, da kuma Isabel, shekarunsu 13, 11, and kuma 9.

“Wata rana a Maris 1963 fa, Paquito ya dawo gida daga makaranta yana jin ciwon kai mai-tsanani. Mun damu ƙwarai game da ko minene dalilin haka—amma bada jimawa ba mun gano abinda ya jawo haka. Sa’o’i uku nan gaba ya mutu. Hatsarin ƙwaƙwalwan kai ya auku ko da ya ɗauke ransa.

“Mutuwar Paquito ya auku ko sama da shekaru 30 da suka shige. Duk da haka, baƙincikin mutuwar nan ya kasance tare da mu har wa yau. Babu yadda iyaye zasu yi hasarar yaro kuma kasa jin cewa sun yi rashin wani abinda ke nasu—ko da shekaru nawa suka shige ko kuwa yara nawa su a iya samu bayan wannan.”

Waɗannan aukuwa biyun, inda iyaye suka yi hasarar yara fa, ya misalta misalin zurfi da kuma daɗewar baƙincikin idan wani yaro ya mutu. Dubi gaskiyar kalmomin wani likita wanda ya rubuto: “Mutuwar jariri galiɓa dai shine mafi ban tausayi da kuma baƙinciki fiye da mutuwar babban mutum domin yaro ba shine wanda za a taɓa zace shi ya mutu cikin iyalin ba. . . . Mutuwar wani yaro yana wakilce hasarar bege na gaba, dangantaka [surukai, jikoki], da abubuwa . . . da ba a taɓa mora ko ba.” Kuma irin jin hasara mai-zurfin nan yana iya aika ga kowace mace wadda ta taɓa hasarar jariri ta wurin barin ciki.

Wata mace da aka yi mata rasuwa ta bayyana haka: “Mijina, Russell, ya yi aiki ko kamar mataimakin mai-jinya a daƙin fiɗa cikin Pacific a lokacin Yaƙin Duniya na II. Ya gani kuma tsira ma yaƙoƙi masu-tsanani ko. Ya dawo United States kuma ga rayuwar kwanciyar hali. Nan gaba ya yi hidima kamar ministan Kalmar Allah. Yayinda yake tsakanin shekarunsa na 60 fa ya soma shaida alamar ciwon zuciya. Ya yi ƙoƙarin yin rayuwa mai-kuzari. Sai kuma, wata rana cikin Yuli 1988, ya sha azabar ciwon zuciya mai-tsanani kuma ya mutu. Mutuwarsa abin cin zuciya ne ƙwarai. Ban iya yin ban kwana ba ma. Shi ba mijina ne kawai ba. Shi abokina ne na ƙwarai. Mun yi zaman tare ko na shekaru 40. Ga fa yadda yake yanzu zan fuskanci kaɗaici na musamman.”

Waɗannan kaɗan ne cikin dubban tsautsayi da ke fuskance iyalai a dukan duniya kowace rana. Kamar yadda yawancin mutane masu baƙinciki zasu gaya maka, lokacinda mutuwa ta ɗauke yaronka, mijinki, matarka, iyayenka, abokinka, lallai fa abinda marubuci Kirista Bulus ya kira shi ne, “maƙiyi na ƙarshe.” Sau dayawa fa furci da ake yawan yi yayinda wani mumunan abu ya faru shi ne ƙin yarda, “Ba gaskiya ba ne! Ba zan gaskata da shi ba.” Wasu mayas da martani kuma sukan kasance haka, kamar yadda zamu gani.—1 Korinthiyawa 15:25, 26.

Amma dai, kafin mu yi la’akari da jiye-jiyen baƙinciki fa, bari mu amsa wasu muhimman tambayoyi. Ashe mutuwa yana nufin ƙarshen mutumen ne? Ashe da akwai wani begen sāke ganin ƙaunatattunmu kuma?

Da Akwai Bege na Ƙwarai

Marubucin Littafi Mai-Tsarki Bulus ya bada bege mai-sauƙaƙawa daga wannan “maƙiyi na ƙarshe,” mutuwa. Ya rubuto: “Za a kawas da mutuwa.” “Maƙiyi na ƙarshe da za a kau da shi mutuwa ne.” (1 Korinthiyawa 15:26, The New English Bible) Ta yaya fa Bulus zai kasance da tabbacin haka? Domin wanda ya tashi daga matattu ne ya koyad da shi, Yesu Kristi. (Ayukan Manzanni 9:3-19) Abinda yasa ke nan Bulus ya iya rubutawa haka: “Gama tun da mutuwa ta wurin mutum [Adamu] ta ke, ta wurin mutum [Yesu Kristi] kuma tashin matattu ya ke. Gama kamar yadda cikin Adamu duka suna mutuwa, hakanan cikin Kristi duka zasu rayu.”—1 Korinthiyawa 15:21, 22.

Yesu ya taɓu ƙwarai sa’anda ya saɗu da gwamruwar Nain kuma ga ɗanta da ya mutu. Labarin Littafi Mai-Tsarki ya gaya mana haka: “Ananan da [Yesu] ya kusanci ƙofar birni [Nain], sai ga wani matace, ana ɗauke da shi, tilo ne ga uwatasa, ita kuwa gwamruwa ce: mutane dayawa kuma daga cikin birni suna tare da ita. Sa’anda Ubangiji ya gan ta, ya yi juyayi bisa gareta, ya ce mata, Kada ki yi kuka. Kuma ya kusato ya taɓa ana’ashi: masu-ɗauka suka tsaya. Ya ce, Sarmayi, ina ce maka, Ka tashi. Matacen ya tashi zaune, ya soma yin magana. Ya bada shi ga uwatasa. Tsoro ya kama su duka: suka girmama Allah, suka ce, Wani annabi mai-girma ya tashi daga cikinmu: kuma, Allah ya ziyarci mutanensa.” Duba fa yadda Yesu ya motsu da juyayi don ya tashe mataccen ɗan gwamruwar nan! Ka dai yi tsammanin abinda wannan ke nufa ga gaba!—Luka 7:12-16.

A wurin, a gaban shaidu fa, Yesu ya tafiyadda tashin matattu da ba za a iya manta da shi ba. Hakan dai alamar tashin matattu da ya riga ya annabta kafin wannan aukuwa, watau sabontawa zuwa rai bisa duniya ƙarƙashin “sabobin sammai.” A lokacin nan fa Yesu ya gaya haka: “Kada ku yi mamakin wannan; gama sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru zasu ji muryatasa, su fito kuma.”—Ru’ya ta Yohanna 21:1, 3, 4; Yohanna 5:28, 29; 2 Bitrus 3:13.

Wasu shaidun tashin matattu kuma sun haɗa da Bitrus, tare da wasu cikin 12 ɗin da suka tafi tare da Yesu cikin tafiyarsa. Lallai fa sun ji Yesu wanda aka tashe shi daga matattu ya yi magana a Kogin Galili. Labarin ya gaya mana haka: “Yesu ya ce masu, Ku zo, ku karya kumallonku. Daga cikin almajiran ba wanda yana da ƙarfin hali da zaya tambaye shi, Wanene kai? gama sun sani Ubangiji ne. Yesu ya zo, ya ɗauki dunƙulen gurasa, ya ba su, da kifi kuma. Wannan yanzu lokaci na uku ne da Yesu ya bayanu ga almajiran, bayan da ya tashi daga cikin matattu.”—Yohanna 21:12-14.

Saboda haka ne, Bitrus ya rubuta da tabbaci na sarai haka: “Albarka ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kristi, wanda ya maya haifuwarmu bisa jinƙansa mai-girma zuwa bege mai-rai ta wurin tashin Yesu Kristi daga matattu.”—1 Bitrus 1:3.

Manzo Bulus ya furta tabbataccen begensa yayinda ya ce: “Ina gaskatawa abinda ke bisa ga Attaurat, da waɗanda an rubuta cikin annabawa: ina da bege ga Allah, abinda waɗannan da kansu kuma suna sauraronsa, za a yi tashin matattu, na masu-adilci da na marasa-adilci.”—Ayukan Manzanni 24:14, 15.

Saboda haka miliyoyin mutane suna iya kasance da bege mai-ƙarfi na sake ganin ƙaunatattu nasu kuma bisa duniya amma ƙarƙashin yanayoyi da suka bambanta ƙwarai. Minene waɗannan yanayoyin zasu kasance? Za a sake bada daki dakin mahawara na bege mai-tushi cikin Littafi Mai-Tsarki ga ƙaunatattunmu da suka mutu a sashe na ƙarshe na mujallar nan, mai-jigo “Tabbataccen Bege Ga Matattu.”

Amma a farko fa bari mu yi la’akari da tambayoyi da zaka iya yi yayinda ka ke baƙincikin rashin wani ƙaunatacce: Daidai ne kuwa a yi baƙinciki haka? Ina yadda zan jure da baƙincikina? Minene wasu zasu yi don su taimake ni jurewa? Ina yadda zan taimake wasu da suke baƙinciki? Kuma musamman, Minene Littafi Mai-Tsarki ya faɗa game da tabbataccen bege na matattu? Shin zan sake ganin ƙaunatattuna kuma kuwa? Kuma a ina

Tambayoyin Yin Bimbini

  • Minene mayas da martani da ake yawan yi ga mutuwar wani ƙaunatacce?

  • Minene Yesu ya yi ga gwamruwa a Nain?

  • Wane alkawali game da matattu ne Yesu ya yi?

  • Me yasa Bitrus da Bulus sun kasance da tabbaci haka cewa za a yi tashin matattu?

  • Waɗanne tambayoyi ne suke bukatar amsa?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba