Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • we pp. 14-19
  • How Can I Live With My Grief?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • How Can I Live With My Grief?
  • Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sauƙaƙa Baƙinciki—Ta Yaya?
  • Yin Sha’ani da Jin Laifi
  • Yin Sha’ani da Fushi
  • Taimako Daga Wurin Allah
  • Jimre Baƙin Ciki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Is It Normal to Feel This Way?
    Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
  • Yadda Za Ka Sami Ta’aziya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • How Can Others Help?
    Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
we pp. 14-19

Ina Yadda Zan Jure da Baƙincikina?

“INA jin matsi mai-girma gareni don in danna jiye-jiyena,” in ji Mike yayinda yake tunawa da mutuwar ubansa. Ga Mike fa, danna baƙincikinsa abinda mazakuta ke bukata ne. Duk da haka nan gaba ya gano cewa ba daidai yake ba. Da haka sa’anda abokin Mike ya yi rashin kakansa namiji, Mike ya san abinda zai yi. Ya ce: “Shekaru da dama can baya, da na ɗan taɓa shi bisa kafada kuma in ce, ‘Ka mazakuta.’ Yanzu kuwa na taɓa dantsensa kuma ce, ‘Ka nuna jiye-jiyenka yadda ka ke ji. Hakan zai taimake ka ka jure da shi. In kana son in ƙyalle ka kaɗai, zan yi haka. Idan kana son in zauna, zan zauna. Amma kada ka ji tsoron nuna jiye-jiyenka.’”

MaryAnne ma ta shaida matsi don ta riƙe jiye-jiyenta yayinda mijinta ya mutu. “Na damu ƙwarai game da son zama gurɓi mai-kyau ga wasu,” in ji ta, “har da na hana kaina nuna jiye-jiye da daidai ne. Amma sannu sannu nan gaba na gano cewa ƙoƙarin zama ginshiƙin ƙarfi ga wasu baya taimako na. Na soma bincika yanayi na kuma ina cewa, ‘Yi kuka idan dole in yi kuka. Kada ki yi ƙoƙarin nuna cewa kina da ƙarfi ainun. Ki nuna jiye-jiyenki don ki saku.’”

Saboda haka duk Mike da MaryAnne sun ce: Ka ƙyalle kanka ka yi baƙinciki! Kuma daidai suke. Don me? Domin baƙinciki sauƙaƙawar jiye-jiye da ake bukata ne. Sauƙaƙa jiye-jiyenka zai iya warware matsi da ka ke ji. Asalin yadda ake furta jiye-jiye, idan an haɗa shi da ganewa da taceccen sanarwa, yakan taimake ka ka sanya jiye-jiyenka a inda suka dace.

Hakika fa, ba kowa ne ke nuna baƙinciki a hanya ɗaya ba. Kuma abubuwa kamar ko ƙaunataccen da ya mutu farat ne ko kuwa mutuwar ya zo bayan doguwar rashin lafiya ne zai taɓe martanin jiye-jiyen waɗanda suke da rai. Amma wani abu sarai yake: Danna jiye-jiyenka zai iya kasance da barna duk a fasalin jiki na waje da kuma a jiye-jiye. Ya fi lafiya ka nuna baƙincikinka. Ta yaya? Nassosin suna kunshe wasu shawarwarai masu aikawa.

Sauƙaƙa Baƙinciki—Ta Yaya?

Yin magana zai iya taimaka wajen sauƙaƙawa. Biye da mutuwar dukan yaransa goma, da kuma wasu hatsari da suka auku masa, uban iyali na dā Ayuba ya ce: “Duk na gaji da raina. Zan fita [Ibrananci, “sake,”] da ƙarata a fili; in yi magana cikin ɓacin raina.” (Ayuba 1:2, 18, 19; 10:1) Ayuba bai iya riƙe ƙararsa ba. Yana bukata ya sake shi; yana bukatar yin “magana.” A makamancin hali fa, ɗan wasan kwaikwayo na Turanci Shakespeare ya rubuto cikin Macbeth: “Ka nuna ɓācin rai; gama baƙinciki da ba a nuna shi ba yakan sha kan mutum.”

Saboda haka yin magana game da jiye-jiyenka ga ‘aboki na gaske’ wanda zai saurara da hanƙuri da kuma nuna tausayi zai iya kawo sauƙaƙawa. (Misalai 17:17) Sa abubuwa da sun faru da kuma jiye-jiye cikin kalmomi sau dayawa sukan sa shi ya zama da sauƙi a gane kuma sarrafa shi. Kuma idan wanda ke saurarawar wanda ya taɓa rashin wani a mutuwa ne wanda ya sarrafa yanayinsa ko nata sarai fa, zaka iya samun wasu shawarwarai da zasu taimake ka game da yadda zaka jure da naka. Lokacinda ɗanta ya mutu, wata uwa ta bayyana dalilin da yasa yana taimakawa a yi magana ga wata mace wadda ta fuskance makamancin rashi: “Sanin cewa wata ta shaida abinda ya faru mani ko, kuma ta jure ko sarai daga haka, kuma cewa har ila tana nan kuma tana jin daɗin rayuwa fa abin ƙarfafawa ne gareni.”

Minene zai faru idan baka jin daɗin yin magana game da jiye-jiyenka? Biye da mutuwar Saul da Jonathan fa, Dawuda ya shirya waƙar makoki na jiye-jiye sarai wanda a cikinsa ya zub da baƙincikinsa. Wannan rubutu na makokin ya zama sashen littafin Samuila na Biyu na Littafi Mai-Tsarki daga bisani. (2 Samuila 1:17-27; 2 Labarbaru 35:25) A bai ɗaya fa, wasu sun iske shi da sauƙi su furta kansu ta wurin rubutu. Wata gwamruwa ta rahoto cewa zata iya rubuta jiye-jiyenta sa’annan kuma ta karanta abinda ta rubuta. Ta iske wannan sauƙaƙawa na ƙwarai ne.

Ko ta wurin magana ko kuwa rubutu ne dai, furta jiye-jiyenka zai iya taimake ka ka sauƙaƙa baƙincikinka. Yana taimakawa ma wajen kawas da rashin ganewa. Wata uwa da an yi mata rasuwa ta bayyana haka: “Mijina da ni mun ji labarin yadda wasu aurarru da sun yi kisan aure ko bayan mutuwar wani yaro, kuma ba mu son haka ya faru ma mu. Saboda haka kowane lokaci da muka fusata, kuma muna son kama juna da laifi fa, mukan tattauna zancen tare. Mun dai sarƙu sosai da juna ta wurin yin haka.” Saboda haka, sanas da jiye-jiyenka zai iya taimake ka gane cewa koda shike kana shaida rashi bai ɗaya fa, wasu su a iya nuna baƙincikinsu dabam—a nasu hali da kuma nasu hanya.

Wani abu kuma da zai iya hanzartadda sauƙaƙa baƙinciki shine kuka. Da akwai “lokacin kuka,” in ji Littafi Mai-Tsarki. (Mai-Wa’azi 3:1, 4) Lallai fa mutuwar wani ƙaunatacce yakan kawo irin lokacin nan. Zub da hawayen baƙinciki kamar dai ita ce yanayi na warkaswa da ya dace.

Wata matashiya ta bayyana yadda abuyarta na kurkusa ta taimake ta ta jure yayinda uwarta ta mutu. Ta tuna da haka: “Kullum dai abuyata tana tare da ni. Takan yi kuka tare da ni. Takan yi magana da ni. Na nuna jiye-jiyena a sāke, kuma haka ya kasance da kyau gareni. Ba na jin kunyar yin kuka sam.” (Duba Romawa 12:15.) Ba kuwa ya kamata ka ji kunyar hawayenka ba. Kamar yadda mun gani ko, Littafi Mai-Tsarki yana cike da misalan mazaje da mataye masu bangaskiya—haɗe da Yesu Kristi—waɗanda a fili sun zub da hawayen baƙinciki ba tare da wani jin kunya ba.—Farawa 50:3; 2 Samuila 1:11, 12; Yohanna 11:33, 35.

Zaka iya iske cewa jiye-jiyenka zai zama wanda ba za a iya faɗinsa ba na ɗan lokaci. Hawaye zai iya zuba ba tare da wani shiri ba. Wata gwamruwa ta iske cewa yin cafene a wani kanti (abinda ita da mijin suke yi dā) yakan sa ta kuka, musamman yayinda, kamar yadda ta saɓa yi, ɗauki wani kayan dafuwa da mijin ke yawan so. Ka yi hanƙuri da kanka. Kada ka ji cewa tilas ne ka denna hawayen. Ka tuna fa, abu ne na al’ada kuma sashe na musamman ne yin baƙinciki.

Yin Sha’ani da Jin Laifi

Kamar yadda aka nuna a farko, wasu suna da jin laifi bayan mutuwar wani ƙaunatacce. Hakan zai iya taimaka wajen bayyana baƙinciki na ainun da amintaccen mutumen nan Yakubu ya shaida yayinda aka sa shi ya gaskata da cewa wata “mugun naman jeji” ta kashe ɗansa Yusufu. Yakubu kansa ya aikad da Yusufu don ya duba lafiyar yan’uwansa. Saboda haka mai-yiwuwa ne Yakubu ya azabu da irin jin laifin nan, kamar ‘Don me na aikad da Yusufu shi kaɗai? Don me na aikad da shi a yankin da ke kewaye da bisashe haka?’—Farawa 37:33-35.

Kila kana jin cewa wani ƙyaliya daga gefenka ne ya jawo mutuwar ƙaunatacce naka. Gane irin jin laifin nan—ko na gaske ne ko kuwa tsammani kawai—martanin baƙinciki ne da aka san da shi kuma yana iya zama da taimako kansa. A nan kuma, kada ka iyakanta irin jiye-jiyen nan ga kanka. Yin magana game da yadda ka ke da jin laifi yana tanadar da sauƙaƙawa da ake bukata.

Ka sani kuma, cewa ko da ƙaƙa muke ƙaunar wani fa, ba zamu iya sarrafa ransa ko kuwa nata ba, ba kuwa zamu iya tsare “sa’a, da tsautsayi” daga faɗa ma waɗanda muke ƙaunarsu ba. (Mai-Wa’azi 9:11, NW) Ban da haka, babu shakka fa nufinka ba mumunan abu ba ne. Alal misali, kasa tafiyar wajen likita da sauri ainun, ashe kana nufin cewa ƙaunataccenka ya yi ciwo ne kuma ya mutu? Hakika ba haka ba! To lallai kai ne ka ke da laifin jawo mutuwar wannan? A’a.

Wata uwa ta koyi yadda zata sarrafa jin laifin sa’anda ɗiyarta ta mutu cikin wata hatsarin mota. Ta bayyana haka: “Na zama da jin laifin cewa na aike ta. Amma na zo ga gane cewa bai dace in ji haka ba. Gama babu wani laifi cikin aikan ta tare da ubanta zuwa wani wuri. Hatsari ne kawai na bala’i.”

‘Amma da akwai abubuwa dayawa da ina so da na gaya ko kuwa yi,’ zaka iya faɗin haka. Gaskiya ne, amma wanene cikinmu zai iya faɗan cewa shi kamiltaccen uba, uwa, ko kuwa yaro ne? Littafi Mai-Tsarki ya tunas da mu: “Gama a cikin abu dayawa dukanmu mu kan yi tuntuɓe. Idan wani baya yi tuntuɓe ga wajen magana ba, wannan cikakken mutum ne.” (Yaƙub 3:2; Romawa 5:12) Saboda haka ka yarda da lazun cewa kai ba cikakke ba ne. Cin gaba da tunani game da abubuwa kamar “da na yi wani abu” ba zai canza wani abu ba, amma zai kumamanta saurin warƙewarka.

Idan kana da kosashen dalili na gaskata da cewa jin laifinka gaskiya ne, ba tsammani ba, sai ka yi la’akari da muhimmin dalili na duka na cire jin laifi—gafarar Allah. Littafi Mai-Tsarki ya tabbatas da mu haka: “Idan kai, ya Ubangiji, zaka ƙididdiga laifofi, wa zaya tsaya, ya Ubangiji? Amma akwai gafara a wurinka.” (Zabura 130:3, 4) Ba zaka iya mayas da dā kuma canza wani abu ba. Zaka fa iya, roƙi gafarar Allah domin wasu ƙuraƙurai na dā. Sai kuma me? To dai, idan Allah ya yi alkwalin ya share ƙuraƙuranka na dā, ashe bai kamata ka gafarce kanka ba?—Misalai 28:13; 1 Yohanna 1:9.

Yin Sha’ani da Fushi

Ashe kana jin fushi ne, watakila da likitoci, nas, abokai, ko kuwa ma da wanda ya mutu? Ka gane cewa wannan ma martani ne da ake yawan yi ga wani rashi. Wani marubuci ya ce: “Sai dai ta wurin sanin fushin ne—ba ta mayas da martani ba amma sanin cewa kana jinsa—ne kaɗai zaka iya yantuwa da sakamakon haka mai-mataswa.”

Abin taimako ne ma don a furta ko kuwa yi rabon fushin. Ta yaya? Hakika dai ba ta wurin wawan fushi ba. Littafi Mai-Tsarki ya fadakad cewa dogon fushi yana da haɗari. (Misalai 14:29, 30) Amma zaka iya samun ta’aziya ta wurin yin magana game da shi ga wani aboki mai-ganewa. Wasu kuma sun iske cewa yin wasa mai-cin ƙarfi yayinda suke baƙinciki yana taimakawa wajen sauƙaƙawa.—Duba kuma Afisawa 4:25, 26.

Yayinda muhimmin abu ne ka buɗe kuma zama da gaske game da jiye-jiyenka, ya dace kuwa a samu kalmar yin lura. Da akwai bambanci mai-girma tsakanin furta jiye-jiyenka da zuba su bisa wasu. Babu dalilin kama wasu da laifi domin fushi da kuma baƙincikinka. Saboda haka ka yi lura da furta jiye-jiyenka, ba ta halin hauka ba. (Misalai 18:21) Da akwai wani taimako na musamman cikin jurewa da baƙinciki, kuma zamu tattauna shi yanzu.

Taimako Daga Wurin Allah

Littafi Mai-Tsarki ya tabbatas da mu: “Ubangiji yana kusa da masu-karyayyar zuciya, yana ceton irin waɗanda suke da ruhu mai-tuba.” (Zabura 34:18) I fa, fiye da kome, dangantaka da Allah zai iya taimake ka ga jure da mutuwar wani ƙaunatacce naka. Ta yaya? Dukan shawarwarai da aka bayar ko yanzu haka daga ko kuwa suna cikin jituwa da Kalmar Allah ne, Littafi Mai-Tsarki. Aika su zai iya taimake ka ka jure.

Ƙari ga haka, kada ka rage girman addu’a. Littafi Mai-Tsarki ya zuga mu haka: “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma zaya agaje ka.” (Zabura 55:22) Idan faɗin jiye-jiyenka ga aboki mai-ganewa zai iya taimakawa fa, dubi misalin yadda zai fi taimakawa ka zub da zuciyarka ga “Allah na dukan ta’aziya”!—2 Korinthiyawa 1:3.

Ba wai addu’a dai yana sa mu sauƙaƙawa ba. “Mai-jin addu’a” ya yi alkawalin bada ruhu mai-tsarki ga bayinsa waɗanda suke roƙonsa game da shi. (Zabura 65:2; Luka 11:13) Kuma ruhu mai-tsarki na Allah, ko kuwa ikon aiki, zai iya cika ka da “mafificin girman iko” don ka ci gaba da rayuwa kullum. (2 Korinthiyawa 4:7) Tuna fa: Allah yana iya taimake amintattun bayinsa su jimre da kowanne da kuma dukan matsaloli da su a fuskanta.

Wata mace wadda ta yi rashin ɗanta a mutuwa ta tuna da yadda ikon addu’a ya taimake ta da kuma mijinta a lokacin rashinsu. “Idan mun dawo gida da dare kuma baƙincikin ya zama mara-jimrewa fa, mukan yi addu’a tare da ƙarfi,” haka fa ta bayyana. “Lokaci na fari da zamu yi wani abu ba tare da ita ba—taron ikklisiya na farko da muka hallarta, taron gunduma na farko da muka hallarta—mukan yi addu’a domin ƙarfi. Yayinda muka falka da safe kuma hakikanin yanayin ya zama wanda ba zamu iya jimrewa da shi ba, mukan yi addu’a ga Jehovah don ya taimake mu. Domin wasu dalilai fa, ya zama azaba ne gareni shiga cikin gidan ni kaɗai. Kuma haka kowane lokaci da na dawo gida ni kaɗai, na kan yi addu’a ga Jehovah don ya taimake ni in iya kasance shiru.” Mace mai-amincin nan da ƙarfi kuma daidai ta gaskata da cewa waɗancan addu’o’in sun taimaka ƙwarai. Kai ma zaka iske haka cikin mayas da martani ga addu’o’inka mara sauyewa, ‘salamar Allah da ke zarce dukan tunani zai tsare zuciyarka da kofofin hankalinka.’—Filibbiyawa 4:6, 7; Romawa 12:12.

Taimako da Allah ke bayaswa da amfani yake ƙwarai. Kirista manzo Bulus ya gaya cewa Allah ke “mana ta’aziya cikin dukan ƙuncinmu, har da zamu iya ta’azantadda waɗanda ke cikin kowane irin ƙunci.” Gaskiya fa, taimakon Allah baya kawas da azaba, amma zai sa ya zama da sauƙin jimrewa. Hakan dai bai nufi cewa ba zaka sāke kuka ko kuwa manta da ƙaunatacce naka ba. Amma zaka sami sauƙi. Kuma yayinda ka ke yin haka, abinda ya faru maka zai iya sa ka zama da ƙarin nuna ganewa da ta’aziya cikin taimaka ma wasu su jure da makamancin rashi.—2 Korinthiyawa 1:4.

Tambayoyin Yin Bimbini

  • Me yasa muhimmin abu ne ka kyalle kanka a nuna baƙinciki?

  • Ina yadda zaka sauƙaƙa baƙincikinka?

  • Ina yadda Nassosi zasu iya taimake ka jure da jin laifi da fushi?

  • A wace hanya ce dangantaka da Allah zai taimake ka jure da mutuwar wani ƙaunatacce?

  • Minene wasu shawarwarai masu aikawa na jurewa da baƙinciki?

Wasu Shawarwarai Masu Aiki

Dangana ga abokai: Kada ka jinkirta barin wasu su taimaka idan suka bada hannun taimako kuma lallai zaka more wasu taimako. Ka gane cewa zai iya zama hanyarsu na nuna maka yadda suke ji; watakila ba zasu iya samun kalmomi da suka dace don yin haka ba.—Misalai 18:24.

Ka lura da lafiyarka: Yin baƙinciki zai iya gajiyadda kai, musamman a farkonsa. Jikinka tana bukatar isashen hutu, lafiyayyen wasa, da kuma abinci da ya dace fiye da yadda ya taɓa kasancewa. Bincikawa na sa’i sa’i na likitan da ka saɓa ziyarta zai taimaka ƙwarai.

Jinkirtadda muhimman shawarwarai: Idan ya yiwu, ka jira sai lokacinda ka soma tunani da kyau sosai kafin ka tsai da shawara kamar irin na sayas da gidanka ko kuwa ka canza aikinka. (Misalai 21:5) Wata gwamruwa ta fadi cewa yan kwanaki bayan mutuwar mijinta, ta kyautar ko da yawancin kayayyakin mijin. Nan gaba fa, ta gano cewa ta kyautar da dukiya mai-tamani da take so ƙwarai.

Ka yi hanƙuri da kanka: Sau dayawa baƙinciki yakan daɗe fiye da yadda yawancin mutane suka sani. Tunawa da rashin ƙaunataccen kowace shekara zai iya sabonta ciwon. Muhimman hotuna, waƙoƙi, ko kuwa ƙanshi ma zai iya jawo zub da hawayen. Wani nazarin yan kimiyya na baƙincikin rasuwa ya bayyana matakin baƙinciki kamar haka: “Wanda aka yi masa rasuwar zai iya canza jiye-jiye da sauri da kuma nan da nan daga ɗaya zuwa wani, kuma ƙin tuna da wanda ya mutun zai iya yankewa ta wurin son yin tunani na son rai na ɗan lokaci.” Ka kasance da alkawalan Jehovah masu tamani a zuci.—Filibbiyawa 4:8, 9.

Ka bada zarafi ga wasu: Ka yi ƙoƙarin yin hanƙuri da wasu. Ka gane cewa ba shi da kyau garesu. Kasa sanin abinda zasu faɗa, su a iya faɗi abinda bai dace ba da rawan jiki.—Kolossiyawa 3:12, 13.

Ka maida hankali ga yin amfani da magani ko kuwa giya don jure ma baƙincikinka: Kowane sauƙaƙawa da ƙwaya ko kuwa giya ke bayaswa na ɗan lokaci ne. Ya kamata a sha magani kaɗai sa’anda likita ya shawarta haka. Ka maida hankali; gama wasu magunguna suna kamuwa. Ƙari ga haka, waɗannan zasu iya jinkirtadda matakin yin baƙinciki. Wani nazarin halin cututtuka Bernard Knight ya fadakad haka: “Tilas ne a jimre, shan azabar tsautsayin kuma daga bisani yi hujjarsa kuma kawas da wannan ta wurin bugar da [mutumen] da ƙwayoyi zai tsawonta ko kuwa rikitar da matakin ne kawai.” Sauƙaƙawa na sarai zai zo ta wurin yin bimbini bisa nufe-nufen Jehovah masu-girma.—Zabura 1:2; 119:97.

Ka komo zuwa halinka na dā: A farko mai-yiwuwa zaka yi ma kanka dole ka je aiki, yin cafene, ko kuwa kula da wasu nawayoyi. Amma zaka iya iske cewa halin rayuwarka na dā zai taimake ka ƙwarai da gaske. Ka taƙure da ayukan Kirista.—1 Korinthiyawa 15:58.

Kada ka ji tsoron barin baƙinciki mai-girma ya shige: Abin mamaki kamar yadda yake, wasu da aka yi masu rasuwa su a iya jin tsoron kawas da baƙinciki mai-girma, suna gaskata da cewa hakan zai nuna cewa ƙaunarsu ga wanda ya mutun yana raguwa. Haka fa ba gaskiya ba ne. Kawas da jin zafin zai buɗe hanyar tunani da babu shakka zai kasance tare da kai.—Mai-Wa’azi 3:1, 4.

Kada ka damu ainun: Zaka iya iske kanka kana damuwa, ‘Minene zai faru mani yanzu?’ Littafi Mai-Tsarki ya shawarta cewa mu damu da rana guda a lokaci ɗaya. “Yin rayuwa rana guda a lokaci ɗaya maimakon yin tunanin gaba fa ya taimake ni ƙwarai,” haka wata gwamruwa ta bayyana. Yesu ya gaya ma almajiransa: “Kada fa ku yi alhini a kan gobe: gama gobe za ya yi alhini don kansa.”—Matta 6:25-34.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba