Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • T-25 pp. 2-6
  • Kana da Ruhu Mara Mutuwa Ne?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana da Ruhu Mara Mutuwa Ne?
  • Kana da Ruhu Mara Mutuwa Ne?
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Menene ne Ruhun?
  • “Ga Turɓaya Za Ka Koma”
  • Ruhun Ya “Komo Wurin Allah”
  • Tabbacaccen Bege
  • “Kurwa” da Kuma “Ruhu”—Menene Ainihi Ma’anar Waɗannan Kalmomi?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Ruhohi Basu Taɓa Rayuwa Kuma Mutu a Duniya Ba
    Ruhohin Matattu—Zasu Taimake Ka ne ko Kuwa Zasu Yi Maka Barna? Sun Wanzu Kuwa Da Gaske?
  • A Ina Kakanninmu Suke?
    Hanyar Rai Madawwami​—Ka Same ta Kuwa?
  • Ina Matattu Suke?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Kana da Ruhu Mara Mutuwa Ne?
T-25 pp. 2-6

Kana da Ruhu Mara Mutuwa Ne?

DA AKWAI rai ne bayan mutuwa? Wannan tambayar ta dame mutane shekaru aru aru da suka shige. Tun fil azal, mutane a kowanne mazauni sun yi tunani a kan wannan batun, kuma suka fito da ra’ayi iri iri.

Mutane da yawa sun gaskata cewa “ruhu” yana tsira daga mutuwar mutum. Da gaske ne wani abu yana barin jikin mutum a lokacin mutuwa ya ci gaba da rayuwa? Menene ne ruhu da ke jikin mutum rayayye? Me ke faruwa da shi lokacin da muka mutu? Hurariyar Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki ta ba da amsa ta gaskiya, mai gamsarwa ga waɗannan tambayoyi.

Menene ne Ruhun?

A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmomi da aka fassara “ruhu” ainihi na nufin “numfashi” ne. Amma wannan ya wuce numfasawa kawai. Alal misali marubucin Littafi Mai Tsarki Yaƙub, ya ce: “Jiki ba tare da ruhu matacce ne.” (Yaƙub 2:26) Saboda haka, ruhu abin da yake motsa jiki ne.

Wannan ikon da yake motsa jiki ba zai kasance numfashi ba kawai, ko kuma iska da take wucewa ta cikin huhu ba. Me ya sa? Domin bayan numfashi ya yanke, ƙwayoyin rai suna kasancewa da rai na ɗan gajeran lokaci—“na mintoci da yawa,” in ji The World Book Encyclopedia. Domin wannan dalilin ne ƙoƙarin a farfaɗo da mutum zai iya nasara, kuma za a iya ɗaukar gaɓoɓin jiki daga wani mutum a liƙa wa wani. Amma da zarar tartsatsin rai ya mutu daga ƙwayoyin rai na jiki, dukan ƙoƙarin a farfaɗo da rai zai zama banza. Babu yawan numfashi a duniya da zai farfaɗo da ƙwayar rai ko guda. Saboda haka, ruhun iko ne mai ba da rai da ba a gani—tartsatsin rai—da yake rayar da ƙwayoyin rai. Wannan ikon rai, numfashi ne ke raya shi.—Ayuba 34:14, 15.

Wannan ruhun a jikin mutane ne kawai yake aiki? Littafi Mai Tsarki ya taimake mu kammala da kyau a batun nan. Sarki mai hikima Sulemanu ya rubuta: “Wa ya san ko ruhun mutum za shi bisa ne, ruhun dabba kuma, ko za shi can cikin ƙasa?” (Mai-Wa’azi 3:21) Saboda haka, mutane da dabbobi duk an ce suna da ruhu. Ta yaya wannan zai kasance?

Za a iya gwada ruhu, ko ikon rai da ƙarfin lantarki da yake bi ta cikin inji ko rediyo. Ƙarfin lantarki da ba a gani za a iya amfani da shi a yi abubuwa da yawa, dangane da irin abin da yake ba wa ƙarfi. Alal misali, za a iya sa murhun zamani ya yi zafi, kwamfuta ta ba da sanarwa kuma ta yi lissafi, kuma telibijin ya ba da hotuna da sauti. Amma dai, ƙarfin lantarkin ba ya ɗaukar siffar abin da yake ba wa ƙarfi. Yana kasancewa ƙarfin kawai. Hakazalika, ikon rai ba ya ɗaukar siffar kowacce siffar halittar da yake motsawa. Ba shi da mutumtaka, ko tunani. Mutane da dabbobi suna da ‘ruhu iri ɗaya ne.’ (Mai-Wa’azi 3:19) Saboda haka, idan mutum ya mutu, ruhunsa ba ya zuwa wani wuri ya zama halittar ruhu.

To, menene yanayin matattu? Kuma me yake faruwa da ruhun idan mutum ya mutu?

“Ga Turɓaya Za Ka Koma”

Da mutum na farko, Adamu, ya take umurnin Allah da gangan, Jehovah ya ce masa: “Sai da jiɓi a fuskarka za ka ci abinci, har kuma ka koma ƙasa; gama daga cikinta aka ciro ka: gama turɓaya ne kai, ga turɓaya za ka koma.” (Farawa 3:19) A ina Adamu yake kafin Jehovah ya halicce shi daga turɓaya? Ina, ba ya ko’ina! A sauƙaƙe bai wanzu ba. Saboda haka, da Jehovah Allah ya ce Adamu zai “koma ƙasa,” yana nufin cewa Adamu zai mutu. Adamu ba zai ƙaura zuwa wani wuri na zaman ruhu ba. Idan ya mutu zai sake zama mara rai, mara wanzuwa. Horonsa mutuwa ce—rashin rai—ba ƙaura zuwa wata duniya ba.—Romawa 6:23.

Wasu da suka mutu kuma fa? An bayyana yadda yanayin matattu yake sarai a Mai-Wa’azi 9:5, 10, inda muka karanta: “Matattu ba su san komi ba . . . babu wani aiki, ko dabara, ko ilimi, ko hikima, cikin kabari inda za ka.” Saboda haka, mutuwa, yanayi ne na rashin wanzuwa. Mai Zabura ya rubuta cewa yayin da mutum ya mutu, “numfashinsa ya kan fita, ya kan koma turɓayarsa kuma; a cikin wannan rana shawarwarinsa su kan lalace.”—Zabura 146:4.

A bayyane yake, matattu ba su san kome ba, ba sa aikin kome. Ba su san kome ba. Ba za su iya ganinka ba, ko su saurare ka, ko su yi magana da kai. Ba za su iya taimakon ka ba ko su yi maka lahani. Babu shakka, ba ka bukatar ka tsorace su. Amma ta yaya ruhun “ya kan fita” daga mutumin a lokacin da ya mutu?

Ruhun Ya “Komo Wurin Allah”

Littafi Mai Tsarki ya ce idan mutum ya mutu, “ruhu kuma ya komo wurin Allah wanda ya bayar.” (Mai-Wa’azi 12:7) Wannan yana nufin cewa takamaiman ruhu ne ke tafiya cikin sararin samaniya zuwa gaban Allah? A’a! Hanyar da Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar nan “komo” ba ya bukatar ainihin tafiya daga wani waje zuwa wani. Alal misali, an gaya wa Isra’ilawa marasa aminci: “Ku juyo wurina, ni ma zan koma wurinku, in ji Ubangiji mai-runduna.” (Malachi 3:7) ‘Komawar’ Isra’ilawa ga Jehovah yana nufin juyawa daga hanyar da ba daidai ba kuma jituwa da hanyar adalci na Allah. Kuma ‘komawar’ Jehovah ga Isra’ilawa na nufin sake mai da hankalinsa da albarka ga mutanensa. A yanayi biyun nan ‘komawa’ ya ƙunshi hali, ba tafiya ta zahiri ba daga wani wuri zuwa wani.

Hakazalika, a mutuwa babu ainihin tafiya daga duniya zuwa sama lokacin da ruhun yake ‘komawa’ ga Allah. Ka tuna, ruhun ikon rai ne. Da zarar wannan ikon ya bar mutum, Allah ne kawai yake da ikon dawo masa da shi. Saboda haka, ruhun “ya komo wurin Allah” domin duk wani bege na rayuwa a nan gaba na wannan mutumin yana ga Allah ne kawai.

Alal misali, ka ga abin da Nassosi suka ce game da mutuwar Yesu. Marubucin lingila Luka ya ba da labari: “Yesu kuwa ya yi kira da murya mai-ƙarfi, kāna ya ce, Uba, a cikin hannuwanka ni ke bada ruhuna. Sai da ya faɗi wannan, kāna ya saki ransa.” (Luka 23:46) Da ruhun Yesu ya fita daga jikinsa, ba yana hanyarsa ta zuwa sama ba ne a zahiri. Ba a tashi Yesu daga matattu ba har sai a rana ta uku. Kuma har sai bayan kwana 40 kafin ya haura zuwa sama. (Ayukan Manzanni 1:3, 9) Ko da yake, a lokacin mutuwarsa, Yesu da gaba gaɗi ya danƙa ruhunsa a hannun Ubansa, da cikakken dogara ga iyawar Jehovah na mai da shi zuwa rai.

Hakika, Allah ne kawai zai iya mai da mutum zuwa rai. (Zabura 104:30) Lalle babban zato wannan ya kawo!

Tabbacaccen Bege

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Lokaci na zuwa da duk waɗanda ke kaburbura da za a tuna da su za su ji muryar [Yesu], su kuma fito.” (Yohanna 5:28, 29, New World Translation) Hakika, Yesu Kristi ya yi alkawarin cewa dukan waɗanda Jehovah zai tuna da su za a tashe su daga matattu, ko kuma a mai da su zuwa rai. Maimakon sanarwa ta baƙin ciki cewa mutane sun mutu, rahoton farin ciki zai sanar da waɗanda aka mai da su zuwa rai. Lalle zai kasance abin farin ciki a yi wa ƙaunatattu maraba daga kabari!

Za ka so ka ƙara sani game da yadda za ka amfana daga wannan bege da Allah ya bayar? Muna gayyatarka ka rubuta zuwa ga adireshi na ƙasan nan domin mujallar nan Ruhohin Matattu—Zasu Taimake Ka ne ko Kuwa Zasu Yi Maka Barna? Sun Wanzu Kuwa Da Gaske?

Sai dai ko an nuna alama, dukan ayoyin da aka yi amfani da su daga Litafi Mai-Tsarki ne kuma an yi amfani da harufan zamani.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba