Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • kp pp. 24-27
  • “Kada Ku Faɗa Ga Gwaji”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Kada Ku Faɗa Ga Gwaji”
  • Ka Zauna A Faɗake!
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Gwaji don a Yi Menene?
  • ‘Ka Ci Gaba da Yin Addu’a’
  • Bari Abin da Kake Tsammani Ya Kasance Mai Yiwuwa
  • Ka Tuna da Batutuwan
  • “Ku Kusaci Allah”
  • Ruhu Mai Tsarki Yana Ba Da Ƙarfi A Jimre Da Gwaji Da Kuma Sanyin Gwiwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Yi Tsaro don Kada Ka Fadi Cikin Jarraba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Kana Rayuwa Bisa Addu’ar Misali Kuwa?​—⁠Sashe na II
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Yadda Za Mu Inganta Adduꞌoꞌinmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Ka Zauna A Faɗake!
kp pp. 24-27

“Kada Ku Faɗa Ga Gwaji”

“Ku zauna a faɗake, ku yi addu’a, kada ku faɗa ga gwaji.” —MATIYU 26:41.

MATSIN yana da tsanani—babu wanda ya taɓa shaida irinsa. Yesu Kristi, Ɗan Allah ya kusa ƙarshen rayuwansa a duniya. Yesu ya farga cewa ba da daɗewa ba za a kama shi, a hukunta shi zuwa mutuwa, a rataye shi kan gungumen azaba. Ya sani cewa kowane tsai da shawara ko abin da zai yi zai shafi sunan Ubansa. Kuma Yesu ya sani cewa rayuwa ta mutane na nan gaba a lokacin ne za a sani. Me ya yi sa’ad da yake fuskantar wannan matsi?

2 Yesu ya je lambun Gatsemani da almajiransa. Wuri ne da suka saba zuwa da Yesu. A wajen, ya ɗan yi tafiya daga almajiransa. Sa’ad da yake shi kaɗai ya juya ga Ubansa na samaniya don ya sami ƙarfi, ya gaya masa zuciyarsa gabaki ɗaya ta wurin addu’a—ba sau ɗaya ba amma har sau uku. Ko da shi kamiltacce ne, Yesu bai yi tunanin zai iya fuskantar matsi shi kaɗai ba.—Matiyu 26:36-44.

3 Mu ma a yau muna cikin matsi. A cikin wannan mujallar, a farko mun bincika tabbacin cewa muna zama cikin ƙarshen wannan zamani. Gwaji da kuma matsi da duniyar Shaiɗan ke kawowa suna ƙaruwa. Shawarwari da kuma ayyukan kowannenmu da ya ce yana bauta wa Allah na gaskiya yana shafan sunansa kuma yana shafanmu sosai game da begen rayuwa cikin sabuwar duniyarsa. Muna ƙaunar Jehovah. Muna son mu ‘jimre zuwa ƙarshe’—ƙarshen rayuwarmu ko ƙarshen wannan zamani, duk dai wanda ya zo farko. (Matiyu 24:13) Amma ta yaya za mu riƙe azancinmu na gaggawa kuma mu ci gaba da zama a faɗake?

4 Domin Yesu ya sani cewa almajiransa—na dā da na yanzu—su ma suna cikin matsi, ya ce musu: “Ku zauna a faɗake, ku yi addu’a, kada ku faɗa ga gwaji.” (Matiyu 26:41) Menene ma’anar waɗannan kalmomi a gare mu a yau? Waɗanne gwaji kake fuskanta? Kuma ta yaya za ka “zauna a faɗake”?

Gwaji don a Yi Menene?

5 Dukanmu kullum muna fuskantar gwajin fāɗa wa “tarkon Iblis.” (2 Timoti 2:26) Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu cewa Shaiɗan musamman yana fakon masu bauta wa Jehovah ne. (1 Bitrus 5:8; Wahayin Yahaya 12:12, 17) Saboda me? Ba domin ya kashe mu ba ne. Idan muka mutu da amincinmu ga Allah, Shaiɗan bai yi nasara ba. Shaiɗan ya sani cewa, Jehovah, a lokacinsa zai kawar da mutuwa ta wurin tashin matattu.—Luka 20:37, 38.

6 Shaiɗan yana son ya halaka wani abin da ya fi ranmu na yanzu muhimmanci—amincinmu ga Allah. Shaiɗan yana alla-alla ya tabbatar cewa zai iya juya mu daga Jehovah. Saboda haka, idan ya iya sa mu yi rashin aminci—mu daina wa’azin bishara kuma mu yi banza da mizanan Kirista—Shaiɗan ya yi nasara ke nan! (Afisawa 6:11-13) Saboda haka ne, “mai gwadawan” yake kawo gwaji gare mu.—Matiyu 4:3.

7 “Kissoshin” Shaiɗan dabam dabam suke. (Afisawa 6:11) Zai iya ya gwada mu da son abin duniya, tsoro, shakka, ko kuma son annashuwa. Amma makaminsa na musamman ya haɗa da sa mu sanyin gwiwa. Mai son ɗaukan zarafi ne ƙwarai domin ya san cewa sanyin gwiwa yana raunana mu, kuma yana sa ya zama da sauƙi mu fāɗa wa gwaji. (Karin Magana 24:10) Yana gwada mu musamman lokacin da muke a ‘ragargaje’ don mu kasala.—Zabura 38:8.

8 Da muke daɗa nisa cikin kwanaki na ƙarshe, abubuwan da suke kawo sanyin gwiwa suna ƙaruwa, kuma suna shafanmu ma. (Dubi akwatin nan “Wasu Abubuwa da Suke Kawo Sanyin Gwiwa.”) Ko da me ya jawo shi, sanyin gwiwa na sa kada mu yi ƙarfi. “Yin matuƙar amfani da lokaci” don hakki na ruhaniya—har da yin nazarin Littafi Mai Tsarki, halartan taron Kirista, da kuma sa hannu a hidima—ƙalubale ne idan muna gajiyar jiki, hankali, muna bukatar huta. (Afisawa 5:15, 16) Ka tuna cewa mai gwadawar yana son ka daina bauta ne. Amma wannan ba lokaci ba ne da za a bar kasancewa da ƙwazo game da irin lokaci da muke ciki! (Luka 21:34-36) Ta yaya za ka yi tsayayya da gwaji kuma ka zauna a faɗake? Ka yi la’akari da shawarwari huɗu da za su taimaka.

‘Ka Ci Gaba da Yin Addu’a’

9 Ka dogara ga Jehovah ta wurin addu’a. Ka tuna da misalin Yesu a lambun Gatsemani. Me ya yi sa’ad da yake cikin wannan matsi na tsotsuwar zuciya? Ya je wajen Jehovah don taimako, ya yi addu’a da himma har “jiɓinsa na ɗiɗɗiga ƙasa kamar manyan ɗarsashin jini.” (Luka 22:44) Ka yi tunanin wannan. Yesu ya san Shaiɗan sosai. Sa’ad da yake sama Yesu ya ga dukan gwaji da Shaiɗan yake amfani da su don ya sa bayin Allah su fāɗa a tarkonsa. Duk da haka, Yesu bai taɓa jin zai iya bi da kome da Mai gwadawar zai yi masa ba. Idan kamiltaccen Ɗan Allah ya ga bukatar ya yi addu’a don Allah ya ba shi ƙarfi, ai sai mu fi yin haka!—1 Bitrus 2:21.

10 Ka kuma tuna, cewa bayan ya aririce almajiransa su ci gaba da yin “addu’a,” Yesu ya ce: “Lalle ruhu ya ɗauka, amma jiki rarrauna ne.” (Matiyu 26:41) Wane jiki Yesu yake nufi? Hakika ba jikinsa ba ne; babu wani raunana cikin kamiltaccen jikinsa na mutum. (1 Bitrus 2:22) Amma ba haka na almajiransa yake ba. Saboda ajizancinsu da suka gāda da kuma zunubi, suna bukatar taimako na musamman don su yi tsayayya da gwaji. (Romawa 7:21-24) Abin da ya sa ya aririce su ke nan—da kuma dukan Kiristoci na gaskiya da suke biye da su—su yi addu’a na neman taimakon bi da gwaji. (Matiyu 6:13) Jehovah yana amsa waɗannan addu’o’i. (Zabura 65:2) Ta yaya? Aƙalla a hanyoyi biyu.

11 Da farko, Allah yana taimakonmu mu fahimci gwaji. Gwajin Shaiɗan kamar tarkuna ne da aka jefa a kan wata hanya mai duhu. Idan ba ka gan su ba sai su kama ka. Ta wurin Littafi Mai Tsarki da littattafai masu tushe daga Littafi Mai Tsarki, Jehovah yana ba da haske game da tarkunan Shaiɗan, ta haka suna taimaka mana mu kauce wa fāɗawa cikin gwaji. Shekaru da yawa yanzu, an yi amfani da littattafai da tsarin ayyuka na taron gunduma da manyan taro don a faɗakar da mu game da haɗari irinsu tsoron mutum, lalatar jima’i, son abin duniya, da kuma wasu gwaji na Shaiɗan. (Karin Magana 29:25; 1 Korantiyawa 10:8-11; 1 Timoti 6:9, 10) Kana gode wa Jehovah domin faɗakar da mu game da kissoshin Shaiɗan kuwa? (2 Korantiyawa 2:11) Dukan wannan faɗakarwa amsar addu’o’inka ne don su taimake ka yin tsayayya da gwaji.

12 Na biyu, Jehovah yana amsa addu’o’inmu ta wurin ba mu ƙarfi don mu jimre wa gwaji. Kalmarsa ta ce: “Allah . . . ba zai kuwa yarda a gwada ku fin ƙarfinku ba, amma game da gwajin sai ya ba da mafita.” (1 Korantiyawa 10:13) Allah ba zai yarda wa gwaji ya sha kanmu don mu kasa samun ƙarfi na ruhaniya da za mu iya tsayayya masa ba—idan muka ci gaba da dogara gare shi. Ta yaya yake “ba da mafita” dominmu? Yana ‘ba da ruhu mai tsarki nasa ga waɗanda suka biɗa.’ (Luka 11:13) Wannan ruhu yana iya taimaka mana mu tuna da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da zai iya ƙarfafa shawararmu na yin abin da ke daidai kuma ya taimake mu tsai da shawara na hikima. (Yahaya 14:26; Yakubu 1:5, 6) Zai iya taimakonmu mu nuna halaye da ake bukata don mu yi nasara bisa miyagun halaye. (Galatiyawa 5:22, 23) Ruhun Allah ma yana iya motsa ’yan’uwa masu bi su ‘sanyaya mana.’ (Kolosiyawa 4:11) Kana gode wa Jehovah cewa yana amsa addu’o’inka don taimako?

Bari Abin da Kake Tsammani Ya Kasance Mai Yiwuwa

13 Don mu zauna a faɗake, muna bukatar mu yi tsammanin abubuwan da za su iya yiwuwa. Dukanmu mukan gaji wani lokaci saboda matsi a rayuwa. Amma ya kamata mu tuna cewa Allah bai yi mana alkawarin rayuwa marar wahala a wannan tsohon zamani ba. Har a lokatai da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, bayin Allah sun fuskanci wahala, har da tsanani, talauci, baƙin ciki, da kuma ciwo.—Ayyukan Manzanni 8:1; 2 Korantiyawa 8:1, 2; 1 Tasalonikawa 5:14; 1 Timoti 5:23.

14 A yau, mu ma muna da namu matsaloli. Za mu iya fuskantar tsanani, damuwar rashin kuɗi, fama da baƙin ciki, ciwo, har da wahala a wasu hanyoyi. Idan Jehovah yana kāre mu daga dukan wahala ta hanyar mu’ujiza, wannan ba zai sa Shaiɗan ya zargi Jehovah ba ne? (Karin Magana 27:11) Jehovah yana ƙyalewa a gwada kuma jarabi bayinsa, a wasu yanayi ma har su mutu a hannun ’yan adawa.—Yahaya 16:2.

15 To, menene Jehovah ya yi alkawarinsa? Kamar yadda muka lura, ya yi mana alkawari cewa zai ƙarfafa mu don mu jimre wa gwaji da za mu fuskanta, idan dai mun dogara sosai gare shi. (Karin Magana 3:5, 6) Ta wurin Kalmarsa, ruhunsa, da kuma ƙungiyarsa, yana kāre mu a ruhaniya, yana taimakonmu mu kāre dangantakarmu da shi. Domin wannan dangantaka, ko idan muka mutu ma, mun yi nasara. Babu wani abu—har mutuwa ma—da za ta hana Allah ya albarkaci bayinsa masu aminci. (Ibraniyawa 11:6) A cikin sabuwar duniya da ta kusa, Jehovah ba zai kasa cika dukan alkawuransa masu girma ba game da yi wa waɗanda suke ƙaunarsa albarka.—Zabura 145:16.

Ka Tuna da Batutuwan

16 Don mu jimre har ƙarshe, muna bukatar mu tuna batutuwa na musamman da suke cikin dalilin da ya sa Allah ya ƙyale mugunta. Yana da kyau mu tuna cewa Shaiɗan ya zargi ikon mallaka na Jehovah, musamman a lokatan da kamar matsaloli sun sha kanmu kuma da muke tunani za mu daina bauta. Mayaudarin ya kuma tuhumi ibada da amincin masu bauta wa Allah. (Ayuba 1:8-11; 2:3, 4) Waɗannan batutuwa da yadda Jehovah ya zaɓa ya magance su sun fi kowannenmu. Ta yaya?

17 Yadda Allah ya ƙyale wahala na ɗan lokaci ya taimake wasu su sami gaskiya. Ka yi tunanin wannan: Yesu ya sha wahala domin mu sami rai. (Yahaya 3:16) Ba ma murna domin haka ne? A shirye muke mu daɗa jimre wahala don wasu su sami rai? Dole mu jimre zuwa ƙarshe, dole mu fahimta cewa hikimar Jehovah ta fi tamu girma. (Ishaya 55:9) Za ya kawo ƙarshen mugunta har abada a lokaci da ya fi dacewa kuma domin amfaninmu sosai. Hakika babu wata hanyar yin haka fiye da wannan, ko ba haka ba? Allah ba ya rashin gaskiya!—Romawa 9:14-24.

“Ku Kusaci Allah”

18 Don mu riƙe halin gaggawa namu, muna bukatar mu kasance kusa da Jehovah. Kada ka manta cewa Shaiɗan yana iyakacin ƙoƙarinsa don ya ɓata dangantakarmu da Jehovah. Shaiɗan zai so mu gaskata cewa ƙarshe ba zai taɓa zuwa ba, kuma cewa babu amfani mu yi wa’azin bisharar ko mu yi rayuwa bisa mizanan Littafi Mai Tsarki. Amma shi “maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.” (Yahaya 8:44) Dole mu ƙuduri niyyar mu “yi tsayayya da Iblis.” Dangantakarmu da Jehovah abin da ba za mu so mu yi banza da ita ba ne. Littafi Mai Tsarki ya aririce mu da kyau: “Ku kusaci Allah, shi ma zai kusace ku.” (Yakubu 4:7, 8) Ta yaya za mu kusaci Jehovah?

19 Yin bimbini ta wurin addu’a yana da muhimmanci. Idan kamar matsi na rayuwa sun sha kanka, ka gaya wa Jehovah zuciyarka. Idan ka ambaci ainihin abin da kake so, zai kasance da sauƙi ka ga amsar roƙonka. Wataƙila amsar ba za ta yi daidai da abin da kake so ba, amma idan burinka don ka ɗaukaka shi ne kuma ka riƙe aminci, zai ba ka taimakon da kake bukata don ka yi nasarar jimiri. (1 Yahaya 5:14) Sa’ad da ka ga yadda yake yi maka ja-gora, za ka matsa kusa da shi. Muhimmin abu ne ka yi karatu kuma ka yi tunani a kan halaye da hanyoyin Jehovah yadda suke a bayyane cikin Littafi Mai Tsarki. Irin wannan bimbini zai taimake ka ka san shi sosai; ya motsa zuciyarka kuma ya daɗa ƙaunarka gare shi. (Zabura 19:14) Kuma cewa ƙauna ce, fiye da kome za ta taimake ka ka yi tsayayya da gwaji kuma ka zauna a faɗake.—1 Yahaya 5:3.

20 Domin mu iya kusaci Jehovah muhimmin abu ne mu kasance kusa da ’yan’uwanmu masu bi. Za a tattauna wannan cikin sashe na ƙarshe na wannan mujallar.

TAMBAYOYI DON NAZARI

• Menene Yesu ya yi sa’ad da yake cikin matsi mai tsanani kusa da ƙarshen rayuwarsa, kuma me ya aririce almajiransa su yi? (Sakin layi na 1-4)

• Me ya sa Shaiɗan yake fakon masu bauta wa Jehovah, kuma a waɗanne hanyoyi yake gwada mu? (Sakin layi na 5-8)

• Don mu yi tsayayya da gwaji, me ya sa za mu ci gaba da yin addu’a? (Sakin layi na 9-12), mu yi tsammanin abubuwan da za su yiwu (Sakin layi na 13-15), mu tuna da batutuwan (Sakin layi na 16-17), kuma mu “kusaci Allah” (Sakin layi na 18-20)?

[Akwati a shafi na 25]

Wasu Abubuwa da Suke Kawo Sanyin Gwiwa

Ciwo/tsufa. Idan muna wahalar wani ciwo ko kuma tsufa da ya rage mana himma, muna iya baƙin ciki cewa ba mu da himma a bauta wa Allah ba.—Ibraniyawa 6:10.

Cizon yatsa. Muna iya baƙin ciki idan ba mu sadu da mutane da yawa da suke son wa’azi da muke yi na Kalmar Allah.—Karin Magana 13:12.

Jin cewa ba mu cancanta ba. Wataƙila domin shan wuya na dogon lokaci, wani zai iya jin cewa Jehovah ba ya ƙaunarsa ko ƙaunarta ba.—1 Yahaya 3:19, 20.

Ɓacin rai. Idan wani mai bi ya ɓata wa wani rai, mutumin zai ɓata rai ƙwarai har da zai so ya daina zuwa taron Kirista ko sa hannu a hidimar fage.—Luka 17:1.

Tsanantawa. Mutane da ba sa bin imaninka, za su iya yin maka hamayya, tsananta maka, ko kuma su yi maka ba’a.—2 Timoti 3:12; 2 Bitrus 3:3, 4.

[Hoto a shafi na 26]

Yesu ya aririce mu mu ci gaba da ‘yin addu’a’ don mu sami taimako mu yi tsayayya da gwaji

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba