Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • hf sashe na 4 pp. 12-14
  • Ku Kashe Kuɗi a Hanyar da Ta Dace

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Kashe Kuɗi a Hanyar da Ta Dace
  • Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • 1 KU YI SHIRI DA KYAU
  • 2 KU FAƊI GASKIYA KUMA KU ƊAUKI KUƊI YADDA YA DACE
  • Kashe Kuɗi Yadda Ya Kamata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Kudi Shi Ne Tushen Dukan Mugunta Kuwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
hf sashe na 4 pp. 12-14
Ma’aurata suna kokarin yin cafene daidai da kudin da suke da shi

SASHE NA 4

Ku Kashe Kuɗi a Hanyar da Ta Dace

“Kowane ƙuduri a bisa shawara ya kan kafu.”​—Misalai 20:18

Dukanmu muna bukatar kuɗi don mu biya wa iyalanmu bukatunsu. (Misalai 30:8) Littafi Mai Tsarki ma ya ce, “dukiya, kāriya ce.” (Mai-Wa’azi 7:12) Tattauna batun kuɗi a matsayin ma’aurata yana iya zama abu mai wuya, amma kada ku bar kuɗi ya jawo matsala a tsakaninku. (Afisawa 4:32) Ma’aurata suna bukatar su amince da juna kuma su yanke shawara tare a kan yadda za su kashe kuɗi.

1 KU YI SHIRI DA KYAU

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “In wani daga cikinku na son gina soron bene, da fari ba sai ya zauna ya yi lissafin abin da zai kashe ba, ya ga ko yana da isassun kuɗi da za su ƙare aikin?” (Luka 14:28, Littafi Mai Tsarki) Yana da muhimmanci ku tsara yadda za ku kashe kuɗinku. (Amos 3:3) Ku tsai da shawara a kan abubuwan da kuke bukatar ku saya da kuma yawan kuɗin da kuke so ku kashe wajen sayensu. (Misalai 31:16) Ko da kuna da kuɗin sayan wani abu, ba lallai sai kun saye shi ba. Ku ƙoƙari ku guji karɓan bashi. Kada ku sayi abin da ba ku da kuɗinsa.—Misalai 21:5; 22:7.

SHAWARA:

  • Idan kuɗin da kuka keɓe don yin sayayya a wata ya yi saura, ku zauna ku tattauna abin da za ku yi da shi

  • Idan kun lura cewa kuɗin da kuka kashe ya fi wanda kuka samu, ku tsara yadda za ku rage sayayyar da kuke yi. Alal misali, ku riƙa dafa naku abincin maimakon sayan abinci a waje

Ma’aurata suna tunani game da wani abin da za su kashe kudi mai yawa a kansa

2 KU FAƊI GASKIYA KUMA KU ƊAUKI KUƊI YADDA YA DACE

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Mu yi abubuwan da ke daidai, ba wai a gaban Ubangiji kaɗai ba, har ma a gaban mutane.” (2 Korintiyawa 8:21, LMT) Ku gaya wa junanku gaskiya game da yawan kuɗin da kuke samu da kuma wanda kuke kashewa.

Ku riƙa tattaunawa tare sa’ad da kuke so ku tsai da shawara a kan batun da ya shafi kuɗi. (Misalai 13:10) Tattauna batun kuɗi zai taimaka muku ku zauna lafiya a aurenku. Kada kowannenku ya ɗauka cewa kuɗin da yake samu nasa ne shi kaɗai, domin kuɗin na iyalin ne. —1 Timotawus 5:8.

Ma’aurata suna duba abubuwa da suka rubuta da za su saya sa’ad da suke a kasuwa

SHAWARA:

  • Ku yanke shawara a kan yawan kuɗin da kowannenku zai iya kashewa ba tare da neman izini ba

  • Kada ku jira sai matsalar kuɗi ta taso kafin ku tattauna batun kuɗi

RA’AYINKU GAME DA KUƊI

Kuɗi yana da amfani, amma kada ku bari ya ɓata aurenku ko kuma ya sa ku yawan damuwa. (Matta 6:25-34) Ba sai kun tara kuɗi kafin ku ji daɗin rayuwa ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku tsare kanku daga dukan ƙyashi [‘kwaɗayi,’ LMT].” (Luka 12:15) Aurenku ya fi duk abin da kuɗi zai iya saya daraja. Saboda haka, kada ku raina abin da kuke da shi kuma kada ku yi watsi da dangantakarku da Allah. Idan kuka yi hakan, iyalinku za ta kasance da farin ciki kuma Jehobah zai amince da ku.​—Ibraniyawa 13:5.

KU TAMBAYI KANKU . . .

  • Mene ne muke bukata mu yi a iyalinmu don mu guji cin bashi?

  • Yaushe ne ni da matata muka tattauna game da kudaden da muke samu da kuma yadda muke kasha su?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba