Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • th darasi na 7 p. 10
  • Ka Koyar da Gaskiya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Koyar da Gaskiya
  • Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Gabatar da Nassi Yadda Ya Dace
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Ka Nuna Yadda Za Su Amfana
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Ka Yi Amfani da Tambayoyi
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Maganarka ta Ratsa Zuciya
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
Dubi Ƙari
Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
th darasi na 7 p. 10

DARASI NA 7

Ka Koyar da Gaskiya

Nassin da aka rubuta

Luka 1:3

ABIN DA ZA KA YI: Ka yi amfani da bayanai na gaskiya da za su taimaka wa masu sauraronka su fahimci batun.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka nemi bayanai na gaskiya. Bayaninka ya yi daidai da abin da ke Littafi Mai Tsarki, idan zai yiwu ka karanta wurin. Idan za ka yi magana a kan wani abu daga littafin kimiyya ko jarida ko labarin wani, ka tabbata cewa abin da kake so ka faɗa gaskiya ne.

  • Ka yi amfani da bayanan yadda ya dace. Don mu bayyana darassin da ke nassin da za mu karanta, muna bukatar mu fahimci abin da Jehobah yake so mu koya a ayar. Bayaninmu ya jitu da dukan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, da kuma littattafan “bawan nan mai aminci, mai hikima.” (Mat. 24:45) Idan ka ɗauko bayani daga wasu littattafan da ba na ƙungiyarmu ba, ka faɗi ainihin abin da suka ce.

    Shawara mai amfani

    Kada ka ƙara gishiri a bayanin. Idan binciken ya ce “wasu mutane,” kada ka ce “yawancin mutane.” Ko ka ce “a yawancin lokaci” maimakon “a wasu lokuta.”

  • Ka taimaka wa masu sauraronka su fahimci batun. Bayan ka karanta wani nassi ko kuma wani littafi, ka yi wa masu sauraronka tambaya ko kuma ka gaya musu wani kwatanci don ka taimaka musu su fahimci batun.

SA’AD DA KAKE WA’AZI

A lokacin da kake shirin fita wa’azi, ka yi tunani a kan tambayoyin da za ka yi wa masu sauraronka, kuma ka yi bincike a kan amsar da wataƙila za su ba ka. Idan wanda kake yi masa wa’azi ya yi maka wata tambaya da ba ka san amsar ba, ka gaya masa cewa za ka je ka yi bincike a kan tambayar don ka ba shi amsa in ka sake dawowa.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba