Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • th darasi na 19 p. 22
  • Maganarka ta Ratsa Zuciya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Maganarka ta Ratsa Zuciya
  • Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Magana da Kuzari
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Ka Nuna Yadda Za Su Amfana
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Ka Yi Jawabi Mai Karfafawa
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Ka Nuna Kauna da Tausayi
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
Dubi Ƙari
Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
th darasi na 19 p. 22

DARASI NA 19

Maganarka ta Ratsa Zuciya

Nassin da aka ambata

Karin Magana 3:1

ABIN DA ZA KA YI: Ka taimaka wa masu sauraronka su ga amfanin maganarka kuma su yi amfani da abin da suka koya.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka taimaka wa masu sauraronka su bincika kansu. Ka yi tambayoyi don masu sauraro su bincika ra’ayinsu a kan batun.

  • Ka sa su kasance da manufa mai kyau. Ka ƙarfafa masu sauraronka su yi tunani a kan dalilin da ya sa suke yin ayyuka masu kyau. Ka taimaka musu su ga cewa abu mafi kyau da ya kamata su sa a gaba shi ne, su ƙaunaci Jehobah da mutane kuma su so koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ka taimaka musu su ga hikimar da ke cikin Littafi Mai Tsarki; kada ka cika su da surutu. Maimakon ka sa masu sauraronka su ji kunya bayan ka gama jawabin, ka ƙarfafa su don su yi abubuwan da suka dace.

  • Ka sa su san Jehobah. Ka nuna yadda koyarwa da ƙa’idodi da kuma dokokin da ke cikin Kalmar Allah suke nuna halayen Allah masu kyau da kuma yadda yake ƙaunar mu. Ka taimaka musu su san yadda Allah yake ji da kuma yadda za su faranta masa rai.

    Shawara mai amfani

    Ka tuna cewa Jehobah ne yake jawo mutane don su bauta masa. Ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ka ƙarfafa masu sauraronka.

SA’AD DA KAKE WA’AZI

Idan zai yiwu, ka yi amfani da tambayoyi don ka san abin da mai sauraronka ya yi imani da shi. Ka lura da fuskarsa da muryarsa don ka san yadda yake ji. Amma, ka yi haƙuri, domin sai mai sauraronka ya amince da kai kafin ya gaya maka abin da ke zuciyarsa.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba