Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 2/1 pp. 4-7
  • Tsabta—Mecece Ainihi Take Nufi?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tsabta—Mecece Ainihi Take Nufi?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ra’ayin Allah Game da Tsabta
  • Ɓangarori Huɗu na Tsabta
  • Ka Kasance da Daidaitaccen Ra’ayi
  • Yaya Muhimmancin Tsabta Take?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Allah Yana Kaunar Mutane Masu Tsabta
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Tsabta Me Ya Sa Take Da Muhimmanci?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Jehobah Yana Son Mu Kasance da Tsabta
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 2/1 pp. 4-7

Tsabta—Mecece Ainihi Take Nufi?

DOMIN dattin Turai da Amirka a ƙarnuka na 18 da 19, ’yan mishan na wannan zamanin suka yi wa’azin abin da za a iya kira “koyarwa ta tsabta.” Wannan koyarwar ta daidaita datti da zunubi, kuma suka ce tsabta za ta jawo mutum kusa da Allah. Wataƙila wannan shi ya kawo wannan furcin, “Tsabta ibada ce.”

Ƙungiyar Sojojin Ceto (Salvation Army), wanda William da Catherine Booth, suka kafa, sun ɗauki wannan ɗabi’ar. In ji littafin nan Health and Medicine in the Evangelical Tradition, ɗaya daga cikin kirarinsu na farko shi ne: “Sabulu, Miya, da Ceto.” Sai, sa’ad da Louis Pasteur da wasu suka tabbatar da nasaba da take tsakanin cuta da ƙwayoyin cuta, ya ƙara kuzari ga tsarin kiwon lafiya na jama’a ta hanyar kimiyya.

Wasu cikin matakai da aka ɗauka nan da nan sun haɗa da hana mai ba da shaida ya yi wa Littafi Mai Tsarki sumba a kotu da kuma kawar da moɗa domin kowa a makarantu da kuma tashar jiragen ƙasa. An yi ƙoƙari ma a sake moɗa-guda a wajen hidima ta addini zuwa kowa-da-moɗarsa. Hakika, majagaba na farko sun yi ɗan nasara wajen canza tarbiyyar mutane dangane ga tsabta. Ya taɓa mutanen sosai da wani marubuci ya kira sakamakon, “soyayya da tsabta.”

Wannan “soyayya da tsabta,” a bayyane take cewa ba ta yi zurfi ba. Bai jima ba da ’yan kasuwa suka mai da sabulu abin yau da kullum ya zama kayan alatu. Talla ta basira ta sa masu ciniki suka gaskata cewa yin amfani da wasu kayayyakin tsabta za su bai wa mai amfani da su matsayi da wasu sai dai su yi kishi. Telibijin ya yaɗa wannan ra’ayin. Mutane da suka yi nasara kuma kyawawa da suke bayyana a talla da kamar wasan kwaikwayo, da kyar ake gani suna tsabtace gidansu, suna share filin gida, suna tsince datti, ko kuma su yi shara bayan kyanwarsu ko karensu ya yi najasa.

Da akwai kuma waɗanda suke tunanin cewa zuwa a yi aiki a waje yana kawo kuɗi, amma aiki a gida ko kuma wasu aikin tsabtace gida ba su da riba. Tun da babu riba ta kuɗi, me ya sa za su kula da mahalli? Sakamako ɗaya na wannan shi ne wasu mutane suna tunanin cewa tsabta ta shafi tsabtar jiki ce kawai.

Ra’ayin Allah Game da Tsabta

Babu shakka ƙoƙarce-ƙoƙarce na farko da aka yi a koyar da tsabta ya taimaka wajen kyautata yanayin rayuwar mutane. Haka kuma daidai ne, domin tsabtar hali ne da ya samu asali daga Jehovah Allah mai tsarki da kuma tsabta. Yana koya mana mu amfani kanmu ta wajen zama masu tsarki masu tsabta a dukan tafarkunmu.—Ishaya 48:17; 1 Bitrus 1:15.

Jehovah Allah abin koyi ne a wannan batu. Tsabta, da kuma wasu halayensa marasa ganuwa, ana ganinsu sarai a halittu na zahiri na Allah. (Romawa 1:20) Mun lura cewa halittun kansu ba sa gurɓata mahalli dindindin. Duniya da zagayar rayuwarta da yawa abar al’ajabi ce mai tsabtace kanta. Irin wannan aiki mai tsabta zai zo ne daga wajen Mai Sifantawa mai son tsabta. Daga wannan za mu gano cewa masu bauta wa Allah ya kamata su kasance masu tsabta a dukan ɓangarorin rayuwarsu.

Ɓangarori Huɗu na Tsabta

Littafi Mai Tsarki ya bayyana ɓangarori huɗu na tsabta da masu bauta wa Jehovah za su yi ƙoƙarin kiyayewa. Bari mu bincika su ɗaɗɗaya.

Ta ruhaniya. Wannan ita ce tsabta mafi muhimmanci tsakanin dukansu, domin wannan ta shafi begen mutum na rayuwa har abada. Amma, sau da yawa wannan shi ne ɓangare da aka fi banza da shi. A ce cikin sauƙi, a kasance da tsabta a ruhaniya yana nufin kada a ketare danga da Jehovah ya kafa tsakanin bauta ta gaskiya da ta ƙarya, domin ga Allah dukan wata irin bauta ta ƙarya marar tsabta ce. Manzo Bulus ya rubuta: “Ku fito daga cikinsu, ku ware in ji Ubangiji, Kada ku taɓa kowane abu mara-tsarki; Ni ma in karɓe ku.” (2 Korinthiyawa 6:17) Almajiri Yaƙub ya fito takamaimai a wannan batun: “Addini mai-tsarki mara-ɓāci a gaban Allah Ubanmu ke nan, mutum shi . . . tsare kansa mara-aibi daga duniya.”—Yaƙub 1:27.

Allah ya nuna rashin yardarsa sarai na gama bauta ta ƙarya da ta gaskiya. Bauta ta ƙarya sau da yawa tana haɗawa da ayyuka marasa tsarki da kuma gumaka da alloli da abin ƙyama ne. (Irmiya 32:35) Saboda haka, an aririci Kiristoci na gaskiya su guji saka hannu cikin kowacce irin bauta marar tsarki.—1 Korinthiyawa 10:20, 21; Ru’ya ta Yohanna 18:4.

Ɗabi’a. A nan ma Allah ya bambance tsakanin abin da yake mai tsabta da abin da yake marar tsabta. An kwatanta duniya gabaki ɗayanta a Afisawa 4:17-19: “Masu-duhun hankali, bāre daga ran Allah . . . sun wuce gaban su ji, har sun bada kansu ga lalata, domin su aika dukan ƙazanta tare da kwaɗayi.” Irin tunanin nan na lalata yana bayyana kansa a hanyoyi da yawa, cikin basira da kuma a fili, saboda haka Kiristoci ya kamata su mai da hankali.

Masu ƙaunar Allah sun sani cewa karuwanci, luwaɗi, da fasikanci, da kuma hotunan tsirarun mutane ƙeta mizanan Jehovah ne na ɗabi’a. Amma, nuna irin waɗannan ayyukan ruwan dare ne a duniyar nishaɗi da ta ado. Dole ne Kiristoci su mai da hankali bisa waɗannan halaye. Saka tufafi gajejjeru, masu nuna jiki zuwa taron Kirista ko kuma biki yana jawo hankali ga jikin mutum kuma yana nuna cewa mutumin ya bauɗe daga ɗabi’a mai kyau. Ban da ma kawo tunani marar tsabta na duniya zuwa cikin tarayyar Kirista, irin wannan adon yana iya sa tunani marar kyau a cikin zuciyarsu. Wannan shi ne ɓangare ɗaya da Kiristoci suna bukatar su yi aiki tuƙuru wajen nuna “hikima mai-fitowa daga bisa.”—Yaƙub 3:17.

Hankali. Birnin zuciyar mutum bai kamata ya zama ma’ajin tunani marar tsabta ba. Yesu ya yi gargaɗi bisa sha’awa marar kyau sa’ad da ya ce: “Dukan wanda ya duba mace har ya yi ƙyashinta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.” (Matta 5:28; Markus 7:20-23) Waɗannan kalmomi sun shafi kallon hotunan tsirarun mutane da kuma fim, karanta labarin jima’i marasa tsarki, da kuma sauraren waƙoƙi masu ba da mugun shawara. Saboda haka, Kiristoci dole ne su guji ƙazantar da kansu ta wajen tunani marar tsabta da za su iya kai wa ga lafazi da ayyuka marasa tsabta.—Matta 12:34; 15:18.

Ta jiki. Tsarkaka da kuma tsabta ta jiki suna da nasaba ta kusa a cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, Bulus ya rubuta: “Ƙaunatattu, muna da waɗannan alkawura, bari mu tsarkake kanmu daga dukan ƙazantar jiki da ta ruhu, muna kāmala tsarki cikin tsoron Allah.” (2 Korinthiyawa 7:1) Saboda haka, Kiristoci na gaskiya, ya kamata su yi ƙoƙari su kasance suna da tsabta a jiki, a gida, da kuma kewayen gidajensu, kamar yadda yanayi ya kasance. Har a inda ake karancin ruwan wanka da na wanki, Kiristoci ya kamata su yi iyakacin ƙoƙarinsu su kasance da tsabta da kuma kyaun gani.

Tsabta ta jiki za ta haɗa da guje wa shan kowacce irin taba, yin maye da barasa, da kuma shan kowacce irin muguwar ƙwaya, da suke ɓata kuma suke naƙasa jiki. Makiyayi da aka kwatanta a Waƙar Waƙoƙi yana son ƙanshi mai daɗi na tufafin ’yar nan Bashulammiya. (Waƙar Waƙoƙi 4:11) Tsabtace jikinmu abu ne mai kyau da ya kamata mu yi, tun da ba ma so mu kasance muna ƙanni ga waɗanda suka kewaye mu. Turare suna da daɗi, amma ba abin da za a sauye ba ne da wanka a kai a kai da kuma tufafi masu tsabta.

Ka Kasance da Daidaitaccen Ra’ayi

Sa’ad da ya zo ga tsabta ta jiki, mutane suna wuce gona da iri. A wata ɓangare kuma damuwa ƙwarai game da tsabta za ta iya hana mu farin cikin rayuwa. Za ta iya kuma ci lokacinmu mai tamani. A wani ɓangare kuma, gida marar fasali zai iya yin tsada wajen gyara. Tsakanin waɗannan biyu, ya fi mu daidaita wajen tsabtace gidajenmu su kasance da kyaun gani.

Su Kasance da Sauƙi. Cunkusasshen gida ko ɗaki yana da wuyar tsabtacewa, kuma ba za a iya ganin datti ba da wuri a irin wannan wuri da ya cunkushe. Gida mai sauƙi, mai sarari yana ɗaukan lokaci kaɗan wajen tsabtacewa. An yaba wa rayuwa mai sauƙi ƙwarai a cikin Littafi Mai Tsarki: “Da shi ke muna da abinci da sutura, da su za mu yi wadar zuci.”—1 Timothawus 6:8.

Ka ba shi fasali. Gida mai tsabta hakkin dukan wanda yake zama cikinsa ne. Gidaje marasa fasali sau da yawa suna somawa ne daga ɗakuna marasa fasali. Fasali yana nufin kome a cikinsa yana wajen da ya dace. Alal misali, wajen tufafi masu datti, bai kamata ya zama a filin ɗakin ba. Ko kuma mafi muni ma, a bar abin wasan yara da kuma kayayyakin aiki barkatai. Haɗari da yawa a gida saboda halin rashin fasali ne.

A bayyane yake sarai cewa, tsabta da kuma hanyar rayuwar Kirista ba za a iya bambance su ba. Game da hanyar rayuwa ta ibada, annabi Ishaya ya yi maganar “Hanyar tsarki.” Kuma ya daɗa cewa “marasa-tsarki ba za su bi kanta ba.” (Ishaya 35:8) Hakika, koyon halaye masu kyau na tsabta yanzu yana ba da tabbaci mai ƙarfi game da begenmu bisa alkawuran Allah cewa ba da daɗewa ba zai kafa aljanna mai tsabta ta duniya. Sa’an nan, a dukan ɓangarorin wannan kyakkyawar duniya, dukan mutane za su ɗaukaka Jehovah Allah ta wajen bin kamiltaccen mizanai na tsabta sosai.—Ru’ya ta Yohanna 7:9.

[Hoto a shafi na 6]

Gida mai tsabta hakkin dukan wanda yake zama cikinsa ne

[Hoto a shafi na 7]

Duniya abar al’ajabi ce wajen tsabtace kanta

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba