Rahoto Daga Masu Shelar Mulki
Mutanen Zamani da Aka Kashe Domin Imaninsu Sun Ba da Shaida a Sweden
KALMAR Helenanci ta “shaida” martyr ce, daga nan aka samo kalmar Turanci ta “martyr,” wadda take nufin “wanda ya ba da shaida ta wajen mutuwarsa.” Kiristoci na ƙarni na farko da yawa sun ba da shaida game da Jehovah ta wajen mutuwa domin imaninsu.
Hakazalika, a ƙarni na 20 dubban Shaidu sun mutu a hannun magoya bayan Hitler domin kasancewa a tsaka-tsaki a batun siyasa da kuma na kishin-ƙasa. Mutanen zamani da aka kashe domin imaninsu su ma sun ba da shaida ƙwarai. Haka ya faru a Sweden a baya bayan nan.
A bikin ƙare Yaƙin Duniya na II da shekara 50 ne, gwamnatin Sweden ta fara ilimantar da al’ummarta game da Yaƙin-Ƙare-Dangi. An kira shirin, Rayayyen Tarihi. An gayyaci Shaidun Jehovah su saka hannu kuma su ba da labarin abin da suka fuskanta.
Shaidun suka amsa wajen baza kayayyakin kallo mai jigo, Waɗanda Suka Wahala da Aka Manta da su na Yaƙin-Ƙare-Dangi. Wannan ya fara a Majami’ar Babban Taro na Shaidun Jehovah a Strängnäs. Shaidun waɗanda suka tsira daga Yaƙin-Ƙare-Dangi suna nan su ba da labarin abin da suka fuskanta ga baƙi 8,400 da suka ziyarta a rana ta farko! A ƙarshen shekara ta 1999, kayayyakin kallon sun bayyana a matattarin kayayyakin tarihi fiye da 100 da kuma laburori a dukan cikin ƙasar Sweden, kuma wajen mutane 150,000 suka gani. Baƙin sun haɗa da ma’aikatan gwamnati, suka yi kyawawan maganganu game da abin da suka gani.
Babu wani abu da ya shafi ayyukan Shaidun Jehovah a Sweden da ya samu irin yaɗuwa da mutane suka yi na’am da shi kamar wannan. Baƙi da yawa sun yi tambaya: “Me ya sa ba ku gaya mana game da abin da kuka fuskanta a Yaƙin-Ƙare-Dangi ba a dā?”
Bayan an baza waɗannan kayayyakin kallo a yankinsu, wata ikilisiya ta ba da rahoton ƙarin kashi 30 bisa ɗari na nazarin Littafi Mai Tsarki na gida! Wani Mashaidi ya gayyaci wani abokin aikinsa zuwa wajen kallon. Abokin ya yarda da farin ciki, kuma ya zo da wata abokiya. Daga baya, abokiyar ta ce ta kasa fahimtar yadda mutane za su kasance da irin wannan bangaskiya mai ƙarfi, da za su gwammace a kashe su maimakon su saka hannu cewa sun ƙi imaninsu. Wannan ya kai ga tattaunawa, kuma aka fara nazarin Littafi Mai Tsarki da ita.
Kamar ’yan’uwansu na ƙarni na farko, waɗannan masu aminci da aka kashe domin imaninsu a ƙarni na 20 sun ba da shaida cewa Jehovah ne kaɗai Allah na gaskiya, wanda ya cancanci kafaffen ban gaskiyarmu da kuma aminci.—Ru’ya ta Yohanna 4:11.
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 19]
Ɗan fursuna na sansani: Państwowe Muzeum Oświęcim-Brzezinka, courtesy of the USHMM Photo Archives