Ya Kamata Limamai Su Sa Hannu a Siyasa?
“SA HANNU a siyasa zai iya taimakon matalauta, abin da wani limamin Kirista na Kyanada ya gaya wa masu tafiyar haji ke nan . . . Ko idan tsarin siyasa bai jitu da nufin Allah ba, muna bukatar mu sa hannu a siyasa don ‘a bi da matalauta yadda ya dace.’ ”—Catholic News.
Rahoton manyan mutane a coci da suke goyon bayan sa hannu a siyasa ba sabon abu ba ne; har da shugabannin addini da suke da matsayi. Wasu sun yi ƙoƙarin su gyara siyasa. An so wasu ana kuma tuna da su domin cewa suna biɗan a daina wariyar ƙabilanci kuma a kawar da bawanci.
Har ila, wasu cikin coci ba sa ganin ya dace limamansu su bi siyasa. Waɗanda suke zuwan coci ne a wasu lokatai suke tuhumar dalilin da ya sa limamansu suke sa hannu cikin siyasa in ji wani talifi game da tauhidin siyasa cikin littafin Christian Century. Mutane da yawa da suke bin addini suna ɗaukan coci wuri mai tsarki ne da bai dace ba domin siyasa.
Wannan ya ta da wasu tambayoyi da suke damun dukan waɗanda suke son su ga duniya mai kyau. Limaman Kiristanci za su iya gyara siyasa kuwa?a Sa hannu a siyasa hanyar Allah ce ta kawo gwamnati na duniya mai kyau? Asalin manufar Kiristanci domin ya soma sabuwar hanya ce ta bin siyasa?
Yadda Aka Soma Siyasa Cikin Sunan Kristi
A cikin littafin nan The Early Church, ɗan tarihi Henry Chadwick ya ce ikilisiyar Kirista na farko an san ta cewa “ba ta son mallakar iko da wannan duniya take yi.” Babu ruwanta da “siyasa, ita mai salama ce, jama’a da ba sa son yaƙi.” Littafin nan A History of Christianity ya ce: “Kiristoci sun tabbata ƙwarai cewa babu wani cikinsu da zai riƙe mukami na ƙasa . . . Har a farkon ƙarni na uku Hippolytus ya ce al’adar Kiristanci ita ce mutum zai bar matsayinsa bayan ya zama Kirista.” Da sannu sannu, mutane masu ƙyashin iko suka soma shugabanci cikin ikilisiyoyi da yawa, suna ɗora wa kansu manyan laƙabi. (Ayukan Manzanni 20:29, 30) Wasu suna son su zama shugabannin addini da kuma na siyasa. Wani canji da ya faru farat ɗaya a gwamnatin Roma ya ba wa mutanen coci zarafin da suke nema.
A shekara ta 312 A.Z., Daular Roma Konstantin arne, ya mai da hankalinsa wajen Kiristanci. Abin mamaki limaman coci sun yarda da wata yarjejeniya domin daula arne ya ba su gata. “Coci sun ci gaba da sa hannu a batun siyasa sosai,” in ji Henry Chadwick. Ta yaya sa hannu cikin siyasa ya shafi mutanen coci?
Yadda Siyasa ta Shafi Waɗanda Suka Sa Hannu
Augustine ɗan tauhidi na Katolika na ƙarni na biyar musamman ne ya gabatar da wannan ra’ayi na cewa Allah zai yi amfani da mutanen coci su zama ’yan siyasa. Yana hangar yadda sarautar da cocin yake yi a kan al’ummai zai kawo salama wa mutane. Amma ɗan tarihi H. G. Wells ya rubuta: “Yawancin tarihin Turai daga ƙarni na biyar har zuwa na goma sha biyar ya nuna kasawar ra’ayin cewa gwamnatin Allah ce take sarautar duniya.” Kiristendam ba su kawo salama ga Turai ba, ballantana duniya. Abin da aka yi tsammani Kiristanci ne ya yi rashin daraja a gaban mutane da yawa. Menene ya faru?
Mutane da yawa da suke bin Kiristanci sun shiga siyasa da nagarin nufi, amma sun iske suna aikata mugunta. An san Martin Luther, mai wa’azi kuma mai fassarar Littafi Mai Tsarki a ƙoƙarce-ƙoƙarcensa ya yi gyara cikin Cocin Katolika. Amma, ƙarfin halinsa na yin gāba da koyarwar coci ya sa ya yi farin jini wurin waɗanda suke tawaye don son siyasa. Mutane da yawa ba su girmama Luther kuma ba sa’ad da ya soma zancen siyasa. Da farko ya so talakawan da suke tawaye da masu sarauta ne. Da tawayen ya zama na nuna ƙarfi, ya ƙarfafa masu sarauta su tsayar da tawayen, kuma sun yi haka, sun karkashe dubban mutane. Ba abin mamaki ba ne talakawan suka ɗauke shi maci amana. Luther ya ƙarfafa masu sarauta su ma a tawayensu wa daular Katolika. Hakika, da aka san ’yan Farostatan cewa su mabiyan Luther ne, suka zama rukunin tawaye. Yaya iko ya shafi Luther? Iko ya ɓata shi. Alal misali, a farko ya ƙi tilasta wa mutane su zama ’yan addini, daga baya ya ƙarfafa abokansa na siyasa su halaka waɗanda suka ƙi imanin yin wa jarirai baftisma ta wurin ƙone su.
John Calvin sanannen limami ne a Geneva, amma kuma yana da ikon siyasa ƙwarai. Lokacin da Michael Servetus ya nuna cewa babu Allah-Uku-Cikin-Ɗaya cikin Nassi, Calvin ya yi amfani da ikonsa ya goyi bayan ƙone Servetus a kan gungume. Lallai muguwar bijirewa ce daga koyarwar Yesu!
Wataƙila waɗannan mutane sun manta abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a 1 Yohanna 5:19: “Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” Da gaske ne suna son su gyara siyasa a zamaninsu, ko kuma suna son iko ne domin samun abokai a manyan matsayi? Ko yaya ne, ya kamata da sun tuna da hurarrun kalmomin almajirin Yesu, Yaƙub: “Ba ku sani ba abutar duniya magabtaka ce da Allah? Dukan wanda ya ke so shi zama abokin duniya fa yana maida kansa magabcin Allah.” (Yaƙub 4:4) Yaƙub ya sani cewa Yesu ya gaya wa mabiyansa: “Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.”—Yohanna 17:14.
Duk da haka ma, ko da mutane sun fahimci cewa bai kamata Kiristoci da “ba na duniya ba” su sa hannu a muguntar wannan duniyar, suna nan suna ƙin tsaka tsaki daga siyasa. Suna jin cewa irin tsaka tsakin nan zai hana Kiristoci su ƙaunaci mutane. Suna jin ya dace shugabannin coci su yi magana kuma su sa hannu a kawar da tasiri na ɓatanci da rashin gaskiya.
[Hasiya]
a An ba da ma’anar siyasa cewa ayyuka ne game da gwamnatin wata ƙasa ko wani wuri, musamman ma muhawwara ko faɗa tsakanin mutane ko kuma ’yan zaɓe da suke neman sarauta.