“Shaida Ga Dukan Al’ummai”
“Za ku zama shaiduna . . . har kuma iyakan duniya.”—AYUKAN MANZANNI 1:8.
1. A ina ne almajiran suka fara jin annabcin da ke rubuce a Matta 24:14, kuma a yaushe?
YAWANCINMU mun san kalmomin Yesu da ke rubuce a Matta 24:14. Hakika, annabci ne mai girma! Ka yi tunanin yadda almajiran suka ji sa’ad da suka ji wannan da farko. Shekara ta 33 A.Z., ce. Almajiran suna tare da Yesu na kusan shekara uku, yanzu sun zo Urushalima tare da shi. Sun ga mu’ujizai da ya yi kuma sun saurari koyarwarsa. Ko da sun yi farin ciki don gaskiya mai tamani da Yesu ya koya musu, sun sani cewa ba dukan mutane ba ne suke farin cikin da suke yi. Yesu yana da magabta masu ƙarfi kuma masu iko.
2. Waɗanne haɗari da kalubale ne almajiran za su fuskanta?
2 A kan Dutsen Zaitu, almajirai huɗu suka zauna tare da Yesu, suna sauraransa sa’ad da yake magana game da haɗari da kalubale da za su fuskanta. Da farko, Yesu ya gaya musu cewa za a kashe shi. (Matta 16:21) Yanzu ya bayyana musu sarai cewa su ma za su fuskanci tsanantawa ta zalunci. Ya ce: “[Mutane] za su miƙa ku ga ƙunci, za su kashe ku kuma: za ku zama abin ƙi ga dukan al’ummai sabili da sunana.” Bai tsaya a nan ba. Annabawan ƙarya za su yaudari mutane da yawa. Wasu za su yi tuntuɓe kuma su ci amanar juna su kuma ƙi juna. Har ila “yawancin mutane” za su ƙyale ƙaunarsu ga Allah da kuma Kalmarsa ta yi sanyi.—Matta 24:9-12.
3. Me ya sa kalmomin Yesu da ke Matta 24:14 abin ban mamaki ne da gaske?
3 Bayan ya ambata wannan yanayin ne Yesu ya faɗi abin da ya sa almajiran mamaki. Ya ce: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.” (Matta 24:14) Hakika, aikin “bada shaida ga gaskiya” da Yesu ya soma a Isra’ila zai ci gaba kuma ya yaɗu zuwa dukan duniya. (Yohanna 18:37) Hakika wannan annabci ne mai ban mamaki! Yaɗa wannan aikin zuwa ga “dukan al’ummai” zai kasance da ƙalubale; yin wannan sa’ad da aka zama “abin ƙi ga dukan al’ummai” zai zama mu’ujiza. Cim ma wannan aiki mai girma zai ɗaukaka ikon mallakar Jehobah da kuma ikonsa, zai kuma nuna ƙaunarsa, jinƙansa, da kuma haƙuri. Ƙari ga haka, zai ba bayinsa zarafin nuna bangaskiyarsu da ibadarsu.
4. Su wa aka gaya wa su yi aikin wa’azi, yaya Yesu ya ƙarfafa su?
4 Yesu ya bayyana wa almajiransa sarai cewa suna da aiki mai muhimmanci da za su yi. Kafin ya haura zuwa sama, Yesu ya bayyana musu kuma ya ce: “Za ku karɓi iko lokacinda Ruhu Mai-tsarki ya zo bisanku; za ku zama shaiduna kuma cikin Urushalima da cikin dukan Yahudiya da Samariya, har kuma iyakan duniya.” (Ayukan Manzanni 1:8) Hakika, ba da daɗewa ba wasu za su bi su. Duk da haka, almajiran ba su da yawa. Babu shakka sun sami ƙarfafa da suka san cewa ruhu mai tsarki na Allah zai ba su ƙarfi su cim ma wannan aiki na Allah!
5. Menene almajiran ba su sani ba game da aikin wa’azi?
5 Almajiran sun san an umurce su su yi wa’azin bishara kuma su “almajirtadda dukan al’ummai.” (Matta 28:19, 20) Amma ba su san yadda za su ba da cikakkiyar shaida kuma ba su san lokacin da ƙarshen zai zo ba. Mu ma ba mu sani ba. Jehobah ne kaɗai ya san yadda zai bi da waɗannan al’amura. (Matta 24:36) Sa’ad da Jehobah ya gamsu da yawan aikin wa’azin da aka yi, zai kawo ƙarshen wannan mugun zamani. Lokacin ne Kiristoci za su gane cewa an yi aikin wa’azi yadda Jehobah yake so. Da ƙyar ne waɗannan almajirai na farko su san yawan yadda za a ba da shaida a wannan lokaci na ƙarshe.
Wa’azi a Ƙarni na Farko
6. Menene ya faru a ranar Fentikos ta shekara ta 33 A.Z., da kuma bayan haka?
6 A ƙarni na farko, aikin wa’azin Mulki da almajirantarwa ya kawo sakamako mai ban mamaki. A ranar Fentikos na shekara ta 33 A.Z., kusan almajirai 120 ne suka taru a gidan bene a Urushalima. Aka cika su da ruhu mai tsarki na Allah, manzo Bitrus ya ba da jawabi mai motsawa ya bayyana abin da wannan mu’ujiza yake nufi kuma mutane 3,000 suka zama masu bi kuma aka yi musu baftisma. Wannan somawa ne kaɗai. Duk da ƙoƙarin da shugabannin addinai suka yi na hana wa’azin bishara, “Ubangiji kuma yana tattarawa [almajiran] yau da gobe waɗanda a ke cetonsu.” Ba da daɗewa ba, “yawan mutane ya kai wajen hamsa.” Bayan hakan, “masu-bada gaskiya kuma suka ƙara daɗuwa ga Ubangiji, taro mai-girma ne na maza da mata.”—Ayukan Manzanni 2:1-4, 8, 14, 41, 47; 4:4; 5:14.
7. Me ya sa juyowa na Karniliyus ya zama aukuwa na musamman?
7 A shekara ta 36 A.Z., an yi wani aukuwa mai ban mamaki, wato, juyowa da baftisma na Karniliyus ɗan Al’umma. Da yake ya ja-goranci manzo Bitrus zuwa wurin wannan mutum mai jin tsoron Allah, Jehobah ya nuna cewa umurnin da Yesu ya ba da a “almajirtadda dukan al’ummai” ba ga Yahudawa da suke wasu ƙasashe kawai ba ne. (Ayukan Manzanni 10:44, 45) Yaya waɗanda suke ja-gora suka aikata? Sa’ad da manzannin da dattawa a Yahudiya suka fahimci cewa za a yi wa wasu al’ummai bishara, wato waɗanda ba Yahudawa ba, sai suka ɗaukaka Allah. (Ayukan Manzanni 11:1, 18) Kafin lokacin, aikin wa’azi ya ci gaba da ba da ’ya’ya tsakanin Yahudawa. Wasu shekaru daga baya, mai yiwuwa kusan shekara ta 58 A.Z., an daɗa ’yan Al’ummai da suka ba da gaskiya ga “dubban mutane [Yahudawa] waɗanda sun bada gaskiya.”—Ayukan Manzanni 21:20.
8. Ta yaya bishara ke shafan mutane?
8 Ko da adadin Kiristoci na ƙarni na farko ya ƙaru sosai, bai kamata mu manta cewa adadin na wakiltan mutane na ainihi ba. Saƙon Littafi Mai Tsarki da suka ji yana da iko. (Ibraniyawa 4:12) Ya canja rayuwar mutane da suka amince da shi. Mutane sun tsabtace rayuwarsu, suka yafa sabon hali, kuma suka sulhunta da Allah. (Afisawa 4:22, 23) Hakan yake a yau. Waɗanda suke amincewa da bishara suna da begen rayuwa har abada.—Yohanna 3:16.
Abokan Aiki na Allah
9. Wane gata da kuma hakki ne Kiristoci na farko suka fahimci suke da shi?
9 Kiristoci na farko ba su yabi kansu ba don abin da suka cim ma. Sun fahimci cewa “ikon Ruhu Mai-tsarki” ne ya tallafa wa aikinsu na wa’azi. (Romawa 15:13, 19) Jehobah ne ya sa aka sami ƙaruwa na ruhaniya. Waɗannan Kiristoci sun sani cewa suna da gata da kuma hakkin zama “abokan aiki na Allah.” (1 Korinthiyawa 3:6-9) Saboda haka, daidai da gargaɗin Yesu, sun yi fama a aikin da aka ba su.—Luka 13:24.
10. Waɗanne ƙoƙarce-ƙoƙarce ne wasu Kiristoci na farko suka yi don su yi wa dukan al’ummai wa’azi?
10 Da yake shi “manzon al’ummai ne,” Bulus ya yi tafiya na miloli dubbai a cikin teku da kuma kan hanya, yana kafa ikilisiyoyi da yawa a lardin Roma na Asiya da kuma Helas. (Romawa 11:13) Ya kuma yi tafiya zuwa Roma har ma zuwa Spain. Kafin nan, manzo Bitrus da aka ɗanka wa “bishara [na waɗanda aka yi wa] kaciya,” ya bi wata hanya don ya yi wa’azi a Babila, cibiya ta musamman na Yahudanci a lokacin. (Galatiyawa 2:7-9; 1 Bitrus 5:13) Mata kamar su Tarafina da Tarafusa suna cikin mutane da yawa da suka yi aikin Ubangiji. An ce wata mai suna Barsisa ta “yi aiki dayawa cikin Ubangiji.”—Romawa 16:12.
11. Ta yaya Jehobah ya albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcen almajiran?
11 Jehobah ya albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcen waɗannan ma’aikata masu himma da kuma wasu. Kafin shekara 30 bayan Yesu ya annabta cewa za a yi wa dukan al’ummai wa’azi, Bulus ya rubuta cewa an yi wa’azi “cikin dukan halitta da ke ƙarƙashin sama.” (Kolosiyawa 1:23) Ƙarshen ya zo lokacin? Ya zo a wani azanci. Ya zo a kan zamanin Yahudawa a shekara ta 70 A.Z., sa’ad da sojojin Roma suka halaka Urushalima tare da haikalin. Duk da haka, Jehobah ya ƙudura cewa za a ba da shaida sosai kafin ya kawo ƙarshen dukan zamanin Shaiɗan.
Aikin Wa’azi a Yau
12. Yaya Ɗaliban Littafi Mai Tsarki na farko suka fahimci umurnin a yi wa’azi?
12 A ƙarshen ƙarni na 19, bayan ridda na addini ya kasance na dogon lokaci, sai aka sake kafa bauta ta gaskiya. Ɗaliban Littafi Mai Tsarki yadda ake kiran Shaidun Jehobah a lokacin, sun fahimci cewa an ba da umurni a yi almajirai a dukan duniya. (Matta 28:19, 20) A shekara ta 1914, ana da misalin mutane 5,100 da suke aikin wa’azi da ƙwazo, kuma an yaɗa bishara zuwa ƙasashe 68. Amma, waɗannan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki na farko ba su fahimci cikakkiyar ma’anar Matta 24:14 ba. A ƙarshen ƙarni na 19, ƙungiyoyin Littafi Mai Tsarki sun fassara da kuma wallafa Littafi Mai Tsarki da ke ɗauke da bishara ko kuma Linjila a harsuna da yawa kuma sun rarraba a dukan duniya. Shekaru da yawa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suna tunani cewa an riga an yi wa’azi ga dukan al’ummai.
13, 14. Wane fahimtar nufin Allah da ƙudurinsa aka gabatar a fitar Hasumiyar Tsaro ta shekara ta 1928?
13 A hankali, Jehobah ya sa mutanensa suka fahimci nufinsa da kuma ƙudurinsa. (Misalai 4:18) Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba, 1928 ta Turanci ta ce: “Za mu iya faɗan cewa rarraba Littafi Mai Tsarki ya cim ma wa’azin bishara na mulki da aka annabta? Ko kaɗan! Ko da an rarraba Littafi Mai Tsarki, har ila ya wajaba ƙaramin rukunin shaidu na Allah a duniya su buga littattafai da ke bayyana [ƙudurin] Allah kuma su je gidaje inda aka ba da waɗannan Littattafai Masu Tsarki. Idan ba haka ba, mutane ba za su san yadda aka kafa gwamnatin Almasihu a zamaninmu ba.”
14 Wannan fitar Hasumiyar Tsaro ta daɗa cewa: “A shekara ta 1920, . . . Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka fahimci annabcin Ubangijinmu da ke Matta 24:14. Sai suka fahimci cewa ‘wannan Linjila’ da za a yi wa’azinta a dukan duniya don shaida ga ’yan al’ummai ba Linjila ba ce na mulki da ke zuwa amma bishara ce cewa Sarki Almasihu ya soma sarauta bisa duniya.”
15. Ta yaya aka faɗaɗa aikin wa’azi tun shekarun 1920?
15 Wannan “ƙaramin rukunin shaidu” a shekarun 1920 ba su ci gaba da zama ƙaramin rukuni ba. Shekaru nan gaba aka gano “taro mai-girma” na “waɗansu tumaki” kuma aka soma tattara su. (Ru’ya ta Yohanna 7:9; Yohanna 10:16) A yau, da akwai masu shelar bishara 6,613,829 a ƙasashe 235 na duniya. Wannan cikar annabci ne mai ban mamaki! Ba a taɓa yin “wannan bisharar kuwa ta mulki” da girma haka ba. Ba a taɓa samun bayin Jehobah masu aminci da yawa haka ba a duniya.
16. Menene aka cim ma a shekarar hidima da ta gabata? (Dubi taswira a shafuffuka na 23 zuwa 26.)
16 Wannan taro mai girma na Shaidu sun yi aiki tuƙuru a shekarar hidima ta 2005. An ba da fiye da sa’o’i biliyan wajen shelar bishara a ƙasashe 235. An koma ziyara miliyoyi kuma an gudanar da miliyoyin nazarin Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah da suka ba da lokacinsu da kuma dukiyarsu domin su gaya wa mutane Kalmar Allah ne suka cim ma wannan aikin. (Matta 10:8) Ta wajen ruhunsa mai tsarki, Jehobah ya ci gaba da ba bayinsa ƙarfi don su cim ma nufinsa.—Zechariah 4:6.
Yin Aiki Tuƙuru Wajen Ba da Shaida
17. Ta yaya mutanen Jehobah suke bin kalmomin Yesu game da wa’azin bishara?
17 Ko da yake kusan shekara 2,000 ta shige tun lokacin da Yesu ya ce za a yi wa’azin bishara, himmar mutanen Allah ga aikin bai rage ba. Mun san cewa idan mun jimre muna yin abin da ke mai kyau, muna nuna halayen Jehobah, wato, ƙauna, jinƙai da haƙuri. Kamarsa, ba ma son a halaka wani amma muna son mutane su sulhunta ga Jehobah. (2 Bitrus 3:9) Da yake sun himmantu a ruhun Allah, Shaidun Jehobah sun ci gaba da sanar da bishara zuwa iyakar duniya da himma. (Romawa 12:11) Saboda haka, mutane ko’ina suna amince da gaskiyar kuma suna bin ja-gora mai kyau na Jehobah. Ga wasu misalai.
18, 19. Waɗanne labarai za ka ba da na wasu da suka saurari bishara?
18 Charles manomi ne a yammancin Kenya. A shekara ta 1998 ya sayar da taba fiye da kilo 8,000, kuma aka ba shi satifiket na lada da ya nuna shi ne Manomin Taba mafi kyau. A lokacin ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Ba da daɗewa ba ya fahimci cewa wanda yake sa hannu wajen yin taba yana taka umurnin Yesu na mu ƙaunaci maƙwabcinmu. (Matta 22:39) Sa’ad da ya kammala cewa ‘manomin taba mafi kyau’ ainihi ‘mai kisa ne mafi kyau’ Charles ya kashe shuke-shukensa na taba da guba. Ya ci gaba kuma ya keɓe kansa ya yi baftisma, yanzu shi majagaba ne na kullum da kuma bawa mai hidima.
19 Babu shakka cewa Jehobah yana girgiza al’ummai ta wa’azi da ake yi a dukan duniya, kuma muradin, wato mutane, suna shigowa. (Haggai 2:7) Pedro, wanda ke da zama a Portugal, ya shiga makarantar tauhidi sa’ad da yake ɗan shekara 13. Yana son ya zama mai wa’azi a ƙasar waje kuma ya koyar da Littafi Mai Tsarki. Amma, bayan ɗan lokaci ya bar makarantar domin ba a yawan koyar da Littafi Mai Tsarki. Bayan shekara shida ya soma karatun kimiyyar halin ɗan adam a jami’a da ke Lisbon. Ya zauna da bābarsa Mashaidiyar Jehobah, wadda ta ƙarfafa shi ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki. A lokacin Pedro bai tabbata ba ko Allah yana wanzuwa, ko kuwa ya tsai da shawara ko zai yi nazarin Littafi Mai Tsarki ko ba zai yi ba. Ya yi wa malaminsa farfesa magana game da yadda bai iya tsai da shawara ba. Farfesan ya gaya masa cewa ilimin halin ɗan adam ya koyar cewa mutane da ba sa iya tsai da shawara suna yi wa kansu lahani. Sai Pedro ya tsai da shawara ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Ya yi baftisma kwanan baya kuma yanzu yana gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na kansa.
20. Me ya sa za mu yi farin ciki cewa ana ba da shaida a dukan duniya?
20 Har ila ba mu san har yaushe za a ba da shaida ga dukan al’ummai ba, ko kuwa rana da sa’ar da ƙarshen zai zo. Mun dai san cewa ba zai daɗe ba. Muna farin ciki cewa wa’azin bishara da ake yaɗawa ko’ina yana cikin abubuwa da suka nuna cewa lokaci ya kusa da Mulkin Allah zai sake sarautar ’yan adam. (Daniel 2:44) Da shigewar kowace shekara, ana ba miliyoyi zarafi su saurari bishara, kuma wannan na ɗaukaka Allahnmu, Jehobah. Bari ya zama ƙudurinka ka kasance da aminci kuma tare da ’yan’uwanka a dukan duniya ku shagala cikin aikin ba da shaida ga dukan al’ummai. Ta yin haka, za mu ceci kanmu da waɗanda suka saurare mu.—1 Timothawus 4:16.
Ka Tuna?
• Me ya sa Matta 24:14 annabci ne na ban mamaki?
• Waɗanne ƙoƙarce-ƙoƙarce Kiristoci na farko suka yi don su yi wa’azi kuma da wane sakamako?
• Ta yaya Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka fahimci bukatar ba da shaida ga dukan al’ummai?
• Menene ya burge ka da ka bincika ayyukan mutanen Jehobah a shekarar hidima da ta shige?
[Taswira a shafi na 23-26]
2005 SERVICE YEAR REPORT OF JEHOVAH’S WITNESSES WORLDWIDE
(See bound volume)
[Map/Hotuna a shafi na 21]
Bulus ya yi tafiya na miloli dubbai a ƙasa da kuma teku don ya yi wa’azin bishara
[Hoto a shafi na 20]
Jehobah ya ja-goranci Bitrus ya yi wa’azi ga Karniliyus da kuma iyalinsa