An Fallasa Magabcin Kristi
TA YAYA za ka kāre kanka idan ka san cewa akwai mugun ciwon da ke kama mutane a yankinku? Wataƙila za ka ƙarfafa garkuwan jikinka kuma ka kauce wa mutanen da suke da ciwon. Dole ne mu yi hakan a hanya ta ruhaniya. Nassosi sun gaya mana cewa magabcin Kristi “yana nan duniya.” (1 Yohanna 4:3) Idan ba ma son mu kamu da “ciwo mai yaɗuwa,” dole ne mu san abubuwan da ke kawo ciwon kuma mu guje musu. Abin farin ciki, Littafi Mai Tsarki ya ba da ƙarin bayani a kan batun.
“Magabcin Kristi” na nufin “yin gāba da Kristi.” A ma’anarta mai girma, kalmar na nuna dukan waɗanda suke hamayya ko kuwa suke da’awar cewa su ne Kristi ko kuma wakilansa. Yesu da kansa ya ce: “Wanda ba shi wajena, gāba da ni ya ke; wanda ba ya tarawa tare da ni ba, warwatsawa ya ke yi.”—Luka 11:23.
Hakika, Yohanna ya rubuta game da magabcin Kristi fiye da shekara 60 bayan mutuwar Yesu da tashinsa daga matattu zuwa sama. Shi ya sa, dole ne a fahimci ayyukan magabtan Kristi ta yadda suke shafan mabiyan Yesu masu aminci a duniya.—Matta 25:40, 45.
Magabcin Kristi Suna Gaba da Mabiyansa
Yesu ya yi wa mabiyansa kashedi cewa duniya za ta ƙi su. Ya ce: Mutane “za su miƙa ku ga ƙunci, za su kashe ku kuma: za ku zama abin ƙi ga dukan al’ummai sabili da sunana. Kuma masu-karyan annabci dayawa za su tashi, su ɓadda mutane dayawa.”—Matta 24:9, 11.
Domin ana tsananta wa almajiran Yesu saboda “sunan [Yesu],” masu tsananta musu magabtan Kristi ne. “Masu-karyan annabci” da wasu cikinsu Kiristoci ne a dā, su ma magabtan Kristi ne. (2 Yohanna 7) Yohanna ya rubuta: Waɗannan “magabtan Kristi dayawa . . . Suka fita daga cikinmu, amma ba na cikinmu ba ne; gama da namu ne, da sun lizima tare da mu.”—1 Yohanna 2:18, 19.
Kalmomin Yesu da Yohanna sun nuna sarai cewa magabcin Kristi ba mutum ɗaya ba ne amma mutane ne da yawa. Bugu da ƙari, domin su annabawan ƙarya ne, manufarsu ta musamman ita ce ruɗun addini. Waɗanne dabaru ne suke amfani da su?
Yaɗa Ƙaryace-Ƙaryacen Addini
Manzo Bulus ya gargaɗi Timoti abokin aikinsa ya mai da hankali da koyarwar ’yan ridda, kamarsu Himinayus da Filitus, waɗanda “maganarsu kuwa za ta ci kamar zuganye.” Bulus ya daɗa: “Mutane masu-kuskure wajen gaskiya, suna cewa, Tashin ya rigaya ya wuce, su kan kuwa jirkitadda bangaskiyar waɗansu.” (2 Timothawus 2:16-18) Mai yiwuwa, Himinayus da Filitus sun koyar da cewa tashin matattu na alama ne da kuma cewa Kiristoci sun riga sun tashi a azanci ta ruhaniya. Hakika, Bulus da kansa ya faɗa sarai cewa zama tabbataccen almajiri na Yesu yana sa mutum ya zama rayayye a gaban Allah. (Afisawa 2:1-5) Duk da haka, koyarwar Himinayus da Filitus ta raina alkawarin Yesu na tashin matattu na zahiri a Mulkin Allah.—Yohanna 5:28, 29.
Daga baya kuma wani rukuni na masu ra’ayin cewa duk abin da ba na ruhaniya ba ne, ba shi da kyau ko kuwa zunubi ne sun sake kirkiro da ra’ayin tashin matattu na alama. Da yake sun gaskata cewa za a iya samun ilimi na sihiri, waɗannan mutanen sun haɗa Kiristanci na ’yan ridda da falsafa na Helenanci da sihiri na mutanen Gabas. Alal misali, sun gaskata cewa dukan al’amura na zahiri mugunta ne, saboda haka Yesu bai zo a zahiri ba amma dai yana da jikin ɗan adam. Kamar yadda muka gani, wannan shi ne ainihin abin da manzo Yohanna ya yi kashedi a kai.—1 Yohanna 4:2, 3; 2 Yohanna 7.
Wata koyarwar ƙarya kuwa da aka kirkiro ƙarnuka daga baya ita ce allah-uku-cikin ɗaya, da yake nuna cewa Yesu Allah ne Maɗaukaki da kuma Ɗan Allah. A cikin littafinsa The Church of the First Three Centuries, Dakta Alvan Lamson ya faɗi cewa koyarwar allah-uku-cikin ɗaya “ba ta fito daga Nassosin Yahudawa da kuma Nassosin Kirista ba; ya ce Limaman Coci ne suka kafa kuma suka haɗa ta da Kiristanci.” Su waye ne waɗannan “Limaman Coci”? Limaman ’yan ridda ne waɗanda suke ɗaukaka koyarwar arne Plato ɗan falsafa na Helenanci.
Haɗa koyarwar allah-uku-cikin ɗaya aikin magabcin Kristi ne, domin wannan koyarwar ta sa Allah ya zama ƙage kuma ta sha kan dangantakarsa da Ɗansa. (Yohanna 14:28; 15:10; Kolossiyawa 1:15) Ka yi tunani, ta yaya mutum zai ‘kusaci Allah’ yadda Nassosi ya ƙarfafa, idan Allah ƙage ne?—Yaƙub 4:8.
Masu fassaran Littafi Mai Tsarki da yawa sun daɗa ga wannan rikitarwa, domin sun cire sunan Allah, Jehobah a nasu fassarar, duk da cewa ya bayyana sau 7,000 a littafi na asali! Hakika, yin ƙoƙarin juya Maɗaukaki zuwa ƙagen da ba shi da suna, rashin daraja ne sosai ga Mahaliccinmu da kuma hurarriyar Kalmarsa. (Ru’ya ta Yohanna 22:18, 19) Ƙari ga haka, sake sunan Allah da laƙabai kamar Ubangiji da Allah ya saɓa wa addu’ar misali na Yesu da ta ce: “A tsarkake sunanka.”—Matta 6:9.
Magabtan Kristi Sun Ƙi Mulkin Allah
Magabtan Kristi suna ƙwazo a cikin “kwanaki na ƙarshe,” lokacin da muke ciki yanzu. (2 Timothawus 3:1) Manufar waɗannan mayaudara na zamani shi ne su yaudari mutane game da matsayin Yesu a Mulkin Allah, gwamnati na samaniya da yanzu zai yi sarauta bisa dukan duniya.—Daniel 7:13, 14; Ru’ya ta Yohanna 11:15.
Alal misali, wasu shugabanan addinai suna wa’azi cewa Mulkin Allah yanayin zuciyar mutane ne, ra’ayin da ba shi da tushe a cikin Nassosi. (Daniel 2:44) Wasu suna da’awar cewa Kristi yana amfani da gwamnati da kuma ƙungiyoyin mutane. Amma, Yesu ya ce: ‘Mulkina ba na wannan duniya ba ne.’ (Yohanna 18:36) Hakika, Shaiɗan ne “sarkin duniya” da kuma “allah na wannan zamani,” ba Kristi ba. (Yohanna 14:30; 2 Korinthiyawa 4:4) Wannan ya bayyana dalilin da ya sa Yesu ba da daɗewa ba zai kawar da dukan gwamnatocin ’yan adam kuma ya zama ainihin Sarkin duniya. (Zabura 2:2, 6-9; Ru’ya ta Yohanna 19:11-21) Mutane suna addu’a don wannan sa’ad da suka maimaita Addu’ar Ubangiji, suna cewa: “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya.”—Matta 6:10.
Domin suna tallafa wa tsarin siyasa na duniya, yawancin shugabannin addini sun tsananta wa waɗanda suke shelar gaskiya game da Mulkin Allah. Abin farin ciki, littafin Ru’ya ta Yohanna cikin Littafi Mai Tsarki ya ambata karuwa ta alama, wato, “Babila Babba” da ta yi “maye da jinin tsarkaka, da jinin shaidu na Yesu.” (Ru’ya ta Yohanna 17:4-6) Tana karuwanci na ruhaniya ta wurin goyon bayan “sarakunan” duniya ko kuma shugabanni masu siyasa, kuma tana samun lada. Wannan mace ta alama addinan ƙarya na duniya ne. Sashe ne na musamman na magabcin Kristi.—Ru’ya ta Yohanna 18:2, 3; Yaƙub 4:4.
Magabtan Kristi Suna “Ƙaiƙayin Kunnuwa”
Ban da ƙin gaskiyar Littafi Mai Tsarki, yawancin mutane da suke da’awar cewa su Kiristoci ne sun ƙi mizanan Littafi Mai Tsarki game da hali domin ɗabi’ar da ake bi a ko’ina. Kalmar Allah ta annabta cewa za a yi haka, tana cewa: “Kwanaki za su zo inda ba za su daure da koyarwa mai-lafiya ba [mutane da suke da’awa suna bauta wa Allah]; amma bisa ga ƙaiƙayin kunnuwa za su tattara wa kansu masu-koyarwa bisa ga sha’awoyinsu.” (2 Timothawus 4:3) An kwatanta waɗannan malaman ƙarya cewa su “masu-ƙaryan manzanci ne, ma’aikata masu-ha’inci, suna mayasda kansu manzannin Kristi.” Littafi Mai Tsarki ya ci gaba da cewa: “Matuƙarsu gwargwadon ayyukansu ne.”—2 Korinthiyawa 11:13-15.
Ayyukansu ya haɗa da “miyagun gurori,” waɗanda rashin daraja ƙa’idodi masu girma ne. (2 Bitrus 2:1-3, 12-14) Ba ma ganin shugabannin addinai da yawa da kuma mabiyansu da suka amince da ayyuka da ba su da kyau, kamar su luwaɗi da kuma zina? Ka ɗauki ɗan lokaci ka gwada waɗannan ra’ayoyi da ke ko’ina da kuma salon rayuwa da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa a Leviticus 18:22; Romawa 1:26, 27; 1 Korinthiyawa 6:9, 10; Ibraniyawa 13:4; da Yahuda 7.
“Ku Gwada Ruhohi”
Domin abubuwan da aka ambata a baya, ya kamata mu yi biyayya da kalmomin manzo Yohanna cewa kada mu yi wasa da imaninmu na addini. Ya yi gargaɗi: “Kada ku bada gaskiya ga kowane ruhu, amma ku gwada ruhohi, ko na Allah ne: gama masu-ƙaryan annabci dayawa sun fita zuwa cikin duniya.”—1 Yohanna 4:1.
Ka yi la’akari da misalin mutane masu “darajar hali” da ke zaune a birnin Biriya a ƙarni na farko. “Suka karɓi magana da yardar rai sarai, suna bin cikin littattafai kowace rana, su gani ko waɗannan al’amura [da Bulus da Sila suka faɗa] haka su ke.” (Ayukan Manzanni 17:10, 11) Hakika, ko da suna so su koya, mutanen Biriya sun tabbata cewa abin da suka ji kuma suka amince da shi yana da tushe cikin Nassosi.
A yau ma, tabbatattun Kiristoci ba sa yarda ra’ayin da ke ko’ina ya rinjaye su amma suna manne wa gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Manzo Bulus ya rubuta: ‘Abin da ni ke addu’a ke nan, ƙaunarku ta yalwata har gaba gaba cikin sani da ganewa duka.’—Filibbiyawa 1:9.
Idan ba ka riga ka yi haka ba, ka tabbata cewa ka sami “sani da ganewa duka” ta wajen koyan abin da Littafi Mai Tsarki ainihi yake koyarwa. “Maganganun rikici” na magabtan Kristi ba ya yaudarar waɗanda suka yi koyi da mutanen Biriya. (2 Bitrus 2:3) Maimakon haka, gaskiya ta ruhaniya na Kristi da mabiyansa na gaskiya ta ’yantar da su.—Yohanna 8:32, 36.
[Box/Hoto a shafi na 12]
ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE GAME DA MAGABCIN KRISTI
“Ya’ya ƙanƙanana, sa’a ta ƙarshe ke nan [mai yiwuwa ƙarshen lokatan manzanni]: kamar yadda kuka ji magabcin Kristi yana zuwa, ko yanzu magabtan Kristi dayawa sun taso.”—1 Yohanna 2:18.
“Wanene maƙaryaci sai wanda yana musun Yesu shi ne Kristi? Magabcin Kristi ke nan, shi wanda ya ke musun Uban da Ɗan.” —1 Yohanna 2:22.
“Kowane ruhu wanda ba ya shaida Yesu ba, ba na Allah ba ne: ruhun magabcin Kristi ke nan, wanda kun ji labari yana zuwa; ko yanzu yana nan duniya.” —1 Yohanna 4:3.
“Masu-ruɗin mutane dayawa sun fita zuwa cikin duniya, watau waɗanda ba su shaida Yesu Kristi ya zo cikin jiki ba. Mai-ruɗewa ke nan da magabcin Kristi.”—2 Yohanna 7.