Tsabta Me Ya Sa Take Da Muhimmanci?
Annoba ta shafi mutane na shekaru dubbai. Wasu mutane sun yi tsammanin cewa waɗannan alamu na fushin Allah kuma aiko ne don ya yi wa masu zunubi horo. Bincike da aka yi sosai na ƙarnuka da yawa sun nuna cewa ƙananan halittu ne da suke zama tare da mu ne suke jawo cuta.
Masu bincike sun gano cewa ɓeraye, kyankyasai, ƙuda, da kuma sauro suna iya yaɗa cuta. Sun kuma gano cewa sau da yawa mutane suna jawo wa kansu cututtuka ta wajen rashin tsabta. Tsabta za ta iya sa mutum ya rayu ko ya mutu.
Hakika, tsaba ya bambanta bisa ga al’adu da kuma yanayin wurin. A wuraren da babu ruwan fanfo ko kuma ban daƙi masu kyau, tsabta yana iya kasancewa da wuya. Duk da haka, Allah ya ba Isra’ilawa na dā umurni game da tsabta sa’ad suke tafiya a cikin jeji, wato, suna cikin wasu yanayi da zai sa kasancewa da tsabta ta zama da wuya.
Me ya sa tsabta take da muhimmanci ga Allah? Ta yaya ne za a iya kasancewa da tsabta? Menene kai da iyalinka za ku iya yi don ku rage haɗarin kamuwa da cuta?
AN TASHI makaranta, Max,a da ke zama a Kamaru ya dawo gida. Cike da yunwa da kishin ruwa, ya shiga cikin gida ya rungumi karensa, sai ya aje jakarsa bisa taburin cin abinci, ya zauna yana jiran abincinsa.
Daga cikin kicin da mamarsa ta ji shigowar Max sai ta kawo masa shinkafa da wake da ɗuminsa. Sai ta ɓata fuska da ta ga jakar makarantarsa a bisa taburin da ta goge. Ta kalli ɗanta sai ta ce a hankali, “Maaaax!” Ɗan ya fahimce ta, nan da nan sai ya ɗauke jakarsa kuma ya je ya wanke hannunsa. Bada daɗewa ba sai ya dawo don ya ci abincinsa. Sai ya ce “Ki yi haƙuri, Mama. Na mance ne.”
Mace mai kula da iyalinta sosai za ta iya yin abubuwa da yawa don su kasance da tsabta, ko da yake za ta bukaci dukansu su ba da haɗin kai. Kamar yadda labarin Max ya nuna, ana bukatar koyarwa na dogon lokaci saboda kasancewa da tsabta yana bukatar ƙoƙari sosai kuma yara suna bukatar a riƙa tuna musu a kai a kai.
Mamar Max ta fahimci cewa abinci zai iya gurɓata a hanyoyi dabam dabam. Saboda haka, tana wanke hannayenta sosai kafin da taɓa kayan abinci kuma tana rufe abincin don kada ƙuda su gurɓata shi. Ta wajen adana abinci da kuma ta wajen tsabtace gidanta, ba ta samun matsalar ɓeraye da na kyankyasai da yawa.
Wani dalili mai muhimmanci da ya sa mahaifiyar Max take kula sosai shi ne don tana son ta faranta wa Allah rai. “Littafi Mai Tsarki ya ce dole ne mutanen Allah su zama masu tsarki, domin Allah mai tsarki ne,” in ji ta. (1 Bitrus 1:16) Ta kuma daɗa cewa, “Tsarki yana da nasaba da tsabta. Shi ya sa nake son gidanmu ya kasance da tsabta kuma iyalinmu su zama masu tsabta. Hakika, hakan zai yiwu ne kawai idan kowa a iyalin ya ba da haɗin kai.”
Ba da Haɗin Kai Daga Iyali Yana da Muhimmanci
Kamar yadda mahaifiyar Max ta lura, tsabta abu ne da kowa a cikin iyalin ya kamata ya ba da haɗin kai. Wasu iyalai sukan zauna su tattauna abin da iyalinsu suke bukata da kuma gyara da ya kamata su yi a cikin gida da kuma waje. Wannan kuma zai ƙarfafa iyalin kuma ya tuna wa kowannen su hakkin da yake da shi wajen kula da lafiyar juna. Alal misali, Mama za ta bayyana wa manyan yaranta dalilin da ya kamata su wanke hannayensu bayan sun fito daga ban daƙi, riƙe abubuwa kamar kuɗi, da kuma kafin su ci abinci. Su kuma tabbata cewa ƙananan sun ɗauki wannan batu da muhimmanci.
Za a iya raba wa kowa aiki a cikin iyali. Iyalin za su iya tsai da shawara cewa za su riƙa tsabtace gidansu kowane mako a kai a kai kuma su tsabtace gidansu sosai sau ɗaya ko biyu a shekara. A wajen kuma fa? Stewart L. Udall wani mai kula da mahalli ya yi magana game da ƙasar Amirka, ya ce: “Muna zama a ƙasar da sai kara lalacewa take yi kuma duka mahallin sai gurɓacewa suke yi.”
Haka kake ji game da mahallinka? A dā a wani gari a Afirka ta Tsakiya mai shela yakan kaɗa ƙararrawa don ya jawo hankalin mutane. Da babban murya, yana tuna wa mutanen garin cewa su tsabtace garin, su kwashe salga ko kuma kwata, su datse rassan itatuwa, su yi fitiki kuma su kona bola.
Zubar da shara matsala ce a dukan duniya kuma ya dami hukumomi da yawa. A wasu unguwanni ba a kwasan bola, har su taru a kan tituna. Za a iya roƙan ’yan ƙasan su taimaka. A matsayinsu na ’yan ƙasa masu kirki, ya kamata Kiristoci su zama na farko a yin biyayya ga dokar Kaisar ba tare da gunaguni ba. (Romawa 13:3, 5-7) Da yardan rai, Kiristoci na gaskiya suna aiki sosai da ƙwazo. Suna sha’awar mahalli mai tsabta kuma suna tsabtace mahallinsu ba sai mai shela ya tuna musu ba. Sun fahimci cewa tsabta yana nuna tarbiyya da kuma hali mai kyau. Yana somawa da kowane mutum da kuma kowane iyali. Tsabtace ko’ina a gida zai kai ga samu lafiyar jiki kuma zai sa unguwar ta kasance da tsabta.
Tsabtace Jiki Yana Ɗaukaka Allahn da Muke Bauta Masa
Tsabtace jikinmu da tufafinmu suna nuna irin bauta da muke yi kuma sau da yawa hakan yana sa mutane su ga cewa mun bambanta. Wani rukunin matasa maza da mata guda 15 suka shiga gidan abinci, bayan da suka dawo daga babban taro na Shaidun Jehobah a Toulouse dake ƙasar Faransa. Wasu ma’aurata tsofaffi da suka zauna kusa da su suna tsammanin cewa matasan za su soma surutu suna damun mutane. Amma, yadda suka kame kansu suna hira ba tare da damun mutane ba da kuma yadda suka yi ado ya burge waɗannan ma’aurata. Sa’ad da matasa za su tafi, ma’auratan suka yaba musu saboda halinsu mai kyau kuma suka gaya wa ɗaya daga cikinsu cewa a yau da wuya a sami matasa masu irin wannan halin.
Baƙi da suke zuwa ofishin reshe, maɗaba’a da kuma mazaunin Shaidun Jehobah suna sha’awar irin tsabta da ake yi a wajen. Ana bukatar waɗanda suke aiki a wajajjen nan su sa tufafi masu tsabta, su riƙa wanka da wanki a kai a kai. Yin amfani da turare ba zai hana tsabtace jiki ba. Sa’ad da waɗannan da suka ba da kansu a aikin hidima na cikakken lokaci suka yi wa maƙwabtansu wa’azi da yamma ko kuma a ƙarshen mako, tufafinsu masu tsabta suna sa mutane su saurari wa’azin.
‘Ku Zama Masu-Koyi da Allah’
An aririce Kiristoci su ‘zama masu-koyi da Allah.’ (Afisawa 5:1) Annabi Ishaya ya rubuta wani wahayi da mala’ika ya kwatanta Mahalicci da waɗannan kalaman “Mai-tsarki, Mai-tsarki, Mai-tsarki.” (Ishaya 6:3) Wannan kwatancin ya nanata cewa Allah mai tsarki ne kuma mai tsabta. Saboda haka, Allah yana bukatar dukan bayinsa su kasance da tsarki da kuma tsabta. Ya ce musu: “Ku za ku zama masu-tsarki; gama ni mai-tsarki ne.”—1 Bitrus 1:16.
Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa Kiristoci su “yafa tufafi da ya dace.” (1 Timothawus 2:9; LMT) Ba abin mamaki ba ne, a littafi Ru’ya ta Yohanna, “linen mai-labshi, mai-walƙiya, mai-tsabta” yana wakiltan ayyuka masu adalci da Allah ya ɗauke su masu tsarki. (Ru’ya ta Yohanna 19:8) A wani ɓangare kuma, sau da yawa a cikin Nassosi ana kwatanta zunubi da tabo ko kuma datti.—Misalai 15:26; Ishaya 1:16; Yaƙub 1:27.
A yau, mutane da yawa suna zama a wuraren da zai zama da wuya su kasance da tsabta ta jiki, ta ɗabi’a da kuma ta ruhaniya. Za a magance wannan matsalar sa’ad da Allah zai “sabonta dukan abu.” (Ru’ya ta Yohanna 21:5) Sa’ad da wannan alkawari ya cika, kowane irin rashin tsabta za su shuɗe har abada.
[Hasiya]
a An canja sunan.
[Akwati da ke shafi na 22]
Allah Yana Bukatar a Yi Tsabta
Sa’ad da suke tafiya a jeji, an umurci Isra’ilawa su kula sosai su binne bahayansu. (Kubawar Shari’a 23:12-14) Wannan kuwa ya zama aiki mai wuya, musamman ma saboda faɗin sansanin, amma hakan ya taimaka wajen kiyaye cututtuka kamar zazzaɓin taifot da kuma kwalera.
An umurci mutanen su wanke ko kuma su kona duk abin da ya taɓa gawa. Ko da yake ba su fahimci dalilin yin hakan ba, amma ya taimaki Isra’ilawa su guji kamuwa da cuta.—Leviticus 11:32-38.
Dole ne Firistoci su wanke hannayensu da ƙafafunsu kafin su yi wani aiki a cikin mazauni. Cika kwanon da ruwa ba zai yi sauƙi ba, amma wanke hannuwa doka ce da dole a bi ta.—Fitowa 30:17-21.
[Akwati da ke shafi na 23]
Tunasarwa Daga Wani Likita
Ruwa abu ne mai muhimmanci a rayuwa, amma idan ruwa ya gurɓata zai iya jawo cuta da mutuwa. Likita J. Mbangue Lobe, shugaban sashen ilimantar da likitoci a tashar jirgin ruwa da ke Douala a ƙasar Kamaru, ya ba da bayanin abin da ya kamata a yi, a wani ganawa da aka yi da shi.
“Ka tafasa ruwanka idan kana shakkarsa.” Amma ya yi gargaɗi: “Yin amfani da abubuwan da za su kashe cuta da ke cikin ruwan yana da kyau amma idan ba a yi amfani da su yadda ya kamata ba za su iya kai ga haɗari. Ku riƙa wanke hannayenku da sabulu kafin ku ci abinci da kuma idan kuka fito daga ban daƙi. Sandan sabulu ba shi da tsada, talakawa ma za su iya sayensa. Ku riƙa wanke tufafinku koyaushe, ku wanke da ruwan zafi idan kuna da cuta a fatanku.”
Likitan ya ci gaba, “dole ne kowa a cikin iyalin ya tsabtace cikin gida da mahallinta. Sau da yawa ba a tsabtace ban daƙi hakan kuwa sai ya zama wajen zaman kyankyasai da ƙuda.” Ya kuma yi wani gargaɗi game da yara: “Ku mai da hankali don kada ku yi wanka a irin waɗannan ruwa da suke taruwa a unguwarku. Suna cike da ƙwayoyin cuta masu haɗari. Ku yi wanka kafin ku kwanta, ku wanke haƙoranku sosai daddare, kuma ku yi amfani da gidan sauro idan za ku yi barci.” Abu mafi muhimmanci game da wannan gargaɗi shi ne ku yi amfani da su don ku guji matsala.
[Hotunan da ke shafi na 22]
Wanke tufafinka yana kiyayewa wajen kamuwa da cuta
[Hotunan da ke shafi na 22]
Kiristoci suna ƙoƙari su tsabtace mahallinsu
[Hotunan da ke shafi na 22]
Mace mai kula za ta yi iya ƙoƙarinta idan ya zo ga tsabtace gidanta