Yadda Za Ka Fahimci Littafi Mai Tsarki
3. Ka Karɓi Taimako Daga Wasu
Sa’ad da ɗan bincike mai suna Edward John Eyre ya yi tafiya mai wuyar gaske zuwa Nullarbor, mazauna Ostareliya sun koya wa Eyre yadda ake samun ruwa daga ƙasa da kuma itatuwan turare. Amincewa da taimako daga waɗanda suka san ƙasar sosai ya ceci ran Eyre daga baya.
KAMAR yadda wannan misalin ya nuna, samun nasara a aiki mai wuya sosai yana bukatar taimako daga wanda ya ƙware sosai a aikin. Haka yake sa’ad da ka soma karanta Littafi Mai Tsarki.
Yesu bai yi tsammanin cewa mabiyinsa za su fahimci Littafi Mai Tsarki ba tare da taimakon wasu ba. A wani lokaci, “ya buɗe hankalinsu, domin su fahimci littattafai.” (Luka 24:45) Yesu ya fahimci cewa masu karanta Littafi Mai Tsarki suna bukatan taimako don su fahimci koyarwar Nassosi.
Taimako Daga Wa?
Yesu ya gaya wa mabiyinsa na gaskiya su ba da wannan taimakon. Kafin ya koma sama, Yesu ya ba da wannan umurnin: “Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai, . . . kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.” (Matta 28:19, 20) Ainihin aikin Kiristoci shi ne koyarwa, kuma hakan ya haɗa da bayyana yadda za a iya yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a rayuwa ta yau da kullum. Kiristoci na gaskiya suna taimaka wa mutane su fahimci Littafi Mai Tsarki.
Ba da daɗewa ba da Yesu ya ba da wannan umurnin, wani abu mai ban sha’awa ya faru. Littafi Mai Tsarki ya ba da labarin wani Bahabashe da ke aiki a gidan sarauta, wanda ke karanta wani sashe na annabcin Ishaya. Ya karanta wani sashe da bai fahimta ba. In ji labarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki, wurin da bai fahimta ba shi ne: “Aka ja shi kamar tunkiya zuwa wurin yanka; kamar yadda ɗan rago kuma a gaban mai-saisaya yana shuru, hakanan ba ya buɗe bakinsa ba: Cikin ƙasƙantarsa aka ƙwace masa shari’a: wa za ya bada labarin tsararsa? Gama an ɗauki ransa daga duniya.”—Ayyukan Manzanni 8:32, 33; Ishaya 53:7, 8.
Bahabashen ya tambayi Filibbus, wanda ƙwararren Kirista ne da ya san Nassosi sosai: “Annabi yana ambaton wanene? kansa ne, ko wani ne?” (Ayyukan Manzanni 8:34) Wannan Bahabashen ya riga ya je Urushalima don bauta, kuma wataƙila ya yi roƙo don ja-gora. Babu shakka, yana karatu cike da ɗoki, da tawali’u. Amma duk da haka, wannan ma’aikacin gidan sarautan bai fahimci wannan sashen ba. Da tawali’u, ya nemi taimako daga Filibbus. Amsar da Filibbus ya bayar ta sa mutumin farin ciki sosai har hakan ya motsa shi ya zama Kirista.—Ayyukan Manzanni 8:35-39.
Shaidun Jehobah suna ci gaba da yin ayyukan da Filibbus da wasu Kiristoci na zamanin dā suka yi. A ƙasashe fiye da 235, Shaidu suna ba da kansu don su taimaka wa wasu su fahimci ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Suna yin hakan ta wajen tattauna Nassosi dalla-dalla. Irin wannan nazarin na Littafi Mai Tsarki dalla-dalla ya ƙunshi bayyana abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da wani batu.a—Ka duba akwatin nan “Amsoshi Masu Gamsarwa Na Tambayoyin Littafi Mai Tsarki.”
“An Amsa Duka Tambayoyi Na”
Steven, Valvanera, da Jo-Anne, da aka yi ƙaulinsu a talifi na farko, sun soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. “Na yi mamaki cewa ta wajen gwada ƙa’idodi ko labarai da ke cikin Nassi da juna, a yawancin lokaci, za ka sami amsar a cikin Littafi Mai Tsarki,” in ji Steven. “Kafin na soma nazarin Littafi Mai Tsari, babu wanda ya nuna mini yadda zan yi hakan. Na samu kwanciyar hankali sa’ad da na san cewa Littafi Mai Tsarki ya ba da amsoshi masu gamsarwa kuma ya faɗi gaskiya game da Allah.
Valvanera ta yarda. “Dukan abubuwan da Shaidun Jehobah suka koya mini daidai suke,” in ji ta. “Na koyi cewa ba na bukatan na gaskata abu kawai domin ‘Coci’ ne ya koyar, amma domin an ba da bayanai masu gamsarwa game da komi.” Jo-Anne ta ce: “Domin an amsa dukan tambayoyi na daga Littafi Mai Tsarki, hakan ya motsa ni na daraja Mawallafin, saboda ya yi tanadin amsa ga duk wata tambayar da mutum ke da ita.”
Ka san wani Mashaidin Jehobah? Ka tuntuɓe shi ko ita ta nuna maka yadda ake yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Idan ba ka san ɗaya daga Shaidun Jehobah ba, don Allah ka rubuta zuwa ɗaya daga cikin adireshin da ke shafi na 4 na mujallar nan. Da taimakon ruhu mai tsarki na Allah, son sani, da kuma taimako daga malamin Littafi Mai Tsarki wanda ya ƙware, Kalmar Allah ba za ta yi maka wuyan fahimta ba. Za ka iya fahimtar Littafi Mai Tsarki!
[Hasiya]
a Littafin da ya taimaka wa mutane da yawa game batun Nassosi shi ne Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
[Akwati/Hotunan da ke shafi na 8]
Amsoshi Masu Gamsarwa Na Tambayoyin Littafi Mai Tsarki
Wasu batutuwan da Shaidun Jehobah suke tattaunawa a tsarin nazarin Littafi Mai Tsarki:
• Menene nufin Allah ga duniya?
• Ina Matattu Suke?
• Muna rayuwa ne a “kwanakin ƙarshe”?
• Me ya sa Allah ya ƙyale wahala?
• Ta yaya zan sa rayuwar iyalina ta zama na farin ciki?
[Hotunan da ke shafi na 7]
Don ka fahimci Littafi Mai Tsarki . . . ka yi addu’a don samun ruhun Allah, ka karanta Littafi Mai Tsarki da zuciya ɗaya, ka karɓi taimako daga wasu