Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 5/15 pp. 24-25
  • Abin da Ya Sa Rayuwarmu Take da Ma’ana Sosai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin da Ya Sa Rayuwarmu Take da Ma’ana Sosai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • JEHOBAH YA ZAMA MANA “ƘAGARA MAI TSAWO”
  • RAYUWARMU TANA DA MA’ANA
  • Yadda Za Ka Sami Salama Duk da Cewa Ana Yaki da Tashin Hankali
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2025
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 5/15 pp. 24-25

TARIHI

Abin da Ya Sa Rayuwarmu Take da Ma’ana Sosai

Patricia Smith ce ta ba da labarin

BA DA daɗewa ba bayan na haifi ɗana Gary a shekara ta 1958, sai na ga alama cewa ba shi da isashen lafiya. Amma, sai bayan wata goma ne likitoci suka gano ciwonta, kuma bayan shekara biyar kafin ƙwararrun likitoci a Landan suka tabbatar da wannan cutar. Na yi baƙin ciki sosai sa’ad da na haifi ’yata Louise bayan shekara tara, kuma na gano cewa ciwonta ya fi na Gary tsanani.

Likitocin suka gaya mini cewa: “’Ya’yanki biyu suna da matsala a matattarin sanin asalin halittarsu, kuma hakan ya sa suna da cutar LMBB.”a A lokacin, likitoci ba su da ilimi sosai game da wannan cutar. Alamomin cutar sun haɗa da rashin gani sosai da ke jawo makanta da yawan kiɓa da yawan yatsun hannu ko na kafa da jinkirin girma da ciwon ƙwaƙwalwa da ciwon sukari da sanyin ƙashi da kuma ciwon koɗa. Saboda haka, kula da yarana zai zama babbar matsala. Binciken da aka yi kwanan nan ya nuna cewa mutum ɗaya cikin mutane dubu 125 yana da wannan cutar a ƙasar Biritaniya, ko da yake ta wasu ba ta yi tsanani ba.

JEHOBAH YA ZAMA MANA “ƘAGARA MAI TSAWO”

Na ɗan tattauna da wata Mashaidiya jim kaɗan bayan aurena, kuma nan da nan, na fahimci cewa suna koyar da gaskiya. Amma, mijina ba ya son saƙonsu. Ban samu damar halartar taro da su ba domin aikin da mijina yake yi ya sa muna ƙaura a kai a kai. Duk da haka, na ci gaba da karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin addu’a ga Jehobah. Na karanta cewa Jehobah “za ya zama ƙagara mai-tsawo domin waɗanda ake zaluntarsu, ƙagara mai-tsawo cikin wokatan wahala,” kuma ba zai yasar da ‘masu-nemansa ba.’ Hakan ya ta’azantar da ni sosai.—Zab. 9:9, 10.

Gary ba ya gani sosai, saboda haka, mun kai shi makaranta ta musamman a kudancin Ingila sa’ad da yake ɗan shekara shida. Kuma makarantar kwana ce. Yakan kira ni a waya a kai a kai don ya gaya mini matsalolinsa, kuma na taimaka masa ya fahimci ƙa’idojin Nassosi. ’Yan shekaru bayan na haifi Louise, sai na soma ciwon shanyewar jiki da kuma sanyin ƙashi. Gary ya dawo gida sa’ad da yake ɗan shekara 16. Ciwonsa ya daɗa tsanani, kuma ya makanta a shekara ta 1975. A shekara ta 1977 kuma, sai maigidana ya yashe mu.

Ba da daɗewa ba bayan dawowar Gary, sai muka soma halartar taro a wata ikilisiya, kuma na yi baftisma a shekara ta 1974. Na yi farin ciki sosai yadda wani dattijo, ya taimaka wa Gary ya jimre da matsalolin da ciwon ya jawo masa sa’ad da yake girma. ’Yan’uwa shaidu sun taimaka mini da aikace-aikacen gida. Daga baya, sai gwamnati ta soma biyan biyar cikinsu don su ci gaba da taimaka mana. Hakan ya taimaka mana sosai.

Gary ya samu ci gaba sosai kuma ya yi baftisma a shekara ta 1982. Ya so ya yi hidimar majagaba na ɗan lokaci, sai na taimaka masa ya yi hakan na ’yan shekaru. Ya yi farin ciki sosai sa’ad da mai kula da da’ira ya tambaye shi cewa, “Me ya hana ka zama majagaba na kullum?” Wannan tambayar ta ƙarfafa Gary ya zama majagaba a shekara ta 1990.

An yi masa aiki a kwatangwalonsa a shekara ta 1999, kuma an sake yin hakan a shekara ta 2008. Amma, ciwon Louise ya fi hakan tsanani, kuma an haife ta a makance. Sa’ad da na ga yatsu guda shida a ƙafanta, sai na san cewa ita ma tana da wannan cutar. Binciken da likitoci suka yi ya nuna cewa tana da matsala sosai a gaɓoɓin jikinta na ciki-ciki. An yi mata fiɗa sau da sau. Hakan ya haɗa da fiɗar koɗa har sau biyar. Har ila, tana da ciwon sukari.

Louise ta san cewa fiɗar da za a yi mata za ta iya sa ranta a cikin haɗari. Saboda haka, takan gaya wa likitoci masu yin fiɗa da kuma sauran masu jinyarta cewa ba ta karɓar ƙarin jini. Hakan ya sa suka zama abokai.

RAYUWARMU TANA DA MA’ANA

Muna yin ayyuka da yawa da suka shafi bautarmu ga Jehobah a gidanmu. Kafin a fitar da na’ura kamar su talabijin da bidiyo, ina yin awoyi wajen karanta wa Gary da Louise littattafai. A yanzu, muna sauraron karatun Littafi Mai Tsarki da kuma wasu shirye-shirye da muka saukar daga dandalin www.pr2711.com, kuma hakan yana taimaka mana mu ba da kalamai a taro.

Gary yakan haddace kalamansa. Kuma idan aka ba shi aiki a Makarantar Hidima ta Allah, sai ya yi magana daga zuciyarsa. Ya zama bawa mai hidima a shekara ta 1995, kuma kullum yana marabtar ’yan’uwa a Majami’ar Mulki. An kuma sanya shi ya riƙa kula da sashen sauti a ikilisiyarsu.

’Yan’uwa suna fita wa’azi tare da shi, kuma suna tura shi a keken guragu, saboda ciwon sanyin ƙashi da yake da shi. Wani ɗan’uwa ya taimaka masa ya yi nazari da ɗalibinsa. Gary ya kuma ƙarfafa wani ɗan’uwa da ya daina bauta wa Jehobah da ƙwazo har shekara 25. Wannan ɗalibinsa da kuma ɗan’uwan nan suna halartar taro yanzu.

Sa’ad da Louise take ’yar shekara tara, kakarta ta koya mata saƙa, kuma ni da wata mai kula da ita mun koya mata yin wasu irin aikace-aikace. Tana jin daɗin saƙa sosai, kuma ta saƙa wa yara da kuma tsofaffin ikilisiyar bargo. Tana yin katin gaisuwa ta kuma aika wa ’yan’uwa. Kuma hakan na sa su farin ciki sosai. Louise ta koyi yin rubutu a kwamfuta. Amma yanzu, tana amfani da wata irin kwamfuta mai magana don aika wa abokanta saƙon imel. Ta yi baftisma sa’ad da take ’yar shekara 17. Mukan yi hidimar majagaba na ɗan lokaci tare a duk watan da ake kamfen ɗin wa’azi. Kamar Gary, Louise ma tana haddace nassosin da suka nuna tana da bege cewa a sabuwar duniya, “za a buɗe idanun makafi” kuma “wanda yake zaune a ciki ba za ya ce, Ina ciwo ba.”—Isa. 33:24; 35:5.

Muna godiya sosai don gaskiyar da ke cikin Kalmar Allah! Muna kuma godiya ga ’yan’uwa a ikilisiyarmu don suna mara mana baya. Da ba don su ba, da mun rasa na yi. Mafi muhimmanci ma, taimakon da Jehobah ya yi mana ne ya sa rayuwarmu ta kasance da ma’ana.

a Cutar nan LMBB tana nufin Laurence-Moon-Bardet-Biedl, kuma sunayen likitoci huɗu da suka gano cutar ke nan. Mutum zai kamu da wannan cutar idan iyayensa suna da matsala a matattarin sanin asalin halittarsu. A yau, an fi sanin cutar da suna Bardet-Biedl a Turanci, kuma ba ta da magani.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba