Ka Daraja Amincin Jehobah Da Gafartawarsa
“Nagari ne kai, ya Ubangiji, mai-hanzarin gafartawa kuwa, mai-yawan jinƙai ga dukan waɗanda su ke kira gareka.”—ZAB. 86:5.
1, 2. (a) Me ya sa muke daraja abokai masu aminci da suke gafartawa? (b) Waɗanne tambayoyi ne za a ba da amsoshinsu?
TA YAYA za ka kwatanta abokin kirki? Wata ’yar’uwa mai suna Ashley ta ce: “Ƙawar kirki ita ce wadda take a shirye a koyaushe ta taimaka miki kuma ta gafarta miki a duk sa’ad da kika yi kuskure.” Dukanmu muna son irin waɗannan abokan. Suna sa mu kasance da kwanciyar hankali kuma mu ji suna ƙaunarmu.—Mis. 17:17.
2 Jehobah ne Aboki mafi aminci da kuma gafartawa. Yana aikata kamar yadda marubucin zabura ya kwatanta: “Nagari ne kai, ya Ubangiji, mai-hanzarin gafartawa kuwa, mai-yawan jinƙai [ko, “ƙauna ta aminci”] ga dukan waɗanda su ke kira gareka.” (Zab. 86:5) Ta yaya mutum zai iya zama mai aminci da kuma gafartawa? Ta yaya Jehobah yake nuna waɗannan halaye masu kyau? Ta yaya za mu iya yin koyi da shi? Amsoshin waɗannan tambayoyin za su taimaka mana mu ƙaunaci Jehobah sosai, a matsayin Abokinmu na kud da kud. Za su kuma sa abokantarmu ta daɗa ɗanko sosai.—1 Yoh. 4:7, 8.
JEHOBAH MAI AMINCI NE
3. Mene ne aminci?
3 Mutum mai aminci yana manne wa wanda yake ƙauna. Yana nuna ƙaunarsa ga mutumin ta wajen taimaka da kuma tallafa masa, har ma a yanayi mai wuya. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Jehobah a matsayin mai aminci. Babu wanda ya kai shi aminci.—R. Yoh. 16:5.
4, 5. (a) Ta yaya Jehobah yake nuna cewa shi mai aminci ne? (b) Ta yaya za mu ƙarfafa sa’ad da muka yi tunani a kan amincin Jehobah?
4 Ta yaya Jehobah ya nuna cewa shi mai aminci ne? A kowane lokaci, yana tallafa wa masu bauta masa da aminci. Ɗaya cikinsu, shi ne Sarki Dauda wanda ya nuna cewa Jehobah amintacce ne. (Karanta Zabura 101:6.) A lokacin da Dauda yake fuskantar gwaje-gwaje, Jehobah ya yi masa ja-gora, ya kāre shi kuma ya cece shi. (2 Sam. 22:1) Dauda ya san cewa Jehobah yana nuna aminci ta wajen aikatawa don ya taimaki bayinsa. Me ya sa Jehobah ya kasance da aminci ga Dauda? Domin Dauda yana da “aminci.” Jehobah yana ƙaunar bayinsa domin amincinsu, kuma yana da aminci ga waɗanda suka kasance da aminci a gare shi.—Mis. 2:6-8.
5 Sa’ad da muka yi tunani a kan yadda Jehobah yake kasancewa da aminci ga bayinsa, hakan zai ƙarfafa mu. Wani amintaccen ɗan’uwa mai suna Reed ya ce: “Ina samun ƙarfafa sosai sa’ad da na karanta game da yadda Jehobah ya taimaka wa Dauda a cikin yanayi mai wuya. Ya kula da Dauda, har sa’ad da yake tsere wa Saul kuma yake zama a cikin koguna. Hakan ya ƙarfafa ni sosai! Kuma, ya tuna mini cewa ko da wane irin yanayi ne nake ciki kuma kome tsananinsa, Jehobah zai taimaka mini muddin na kasance da aminci a gare shi.” Babu shakka, kai ma kana jin hakan.—Rom. 8:38, 39.
6. A waɗanne hanyoyi ne kuma Jehobah yake kasancewa da aminci, kuma yaya bayinsa suke amfana?
6 A waɗanne hanyoyi ne kuma Jehobah ya nuna cewa shi mai aminci ne? Yana bin mizanansa a koyaushe. Ya tabbatar mana: “Har tsufarku kuma, ni ne shi.” (Isha. 46:4) Yana tsai da dukan shawarwarinsa bisa mizanansa, kuma ba ya canjawa. (Mal. 3:6) Ƙari ga haka, Jehobah yana kasancewa da aminci ta wajen cika alkawarinsa. (Isha. 55:11) Dukan amintattun bayin Jehobah suna amfana domin amincinsa. Ta yaya? Ya yi alkawari cewa zai albarkace mu idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu bi dokokinsa, kuma muna da tabbaci cewa zai yi hakan.—Isha. 48:17, 18.
KA ZAMA MAI AMINCI KAMAR JEHOBAH
7. A wace hanya ce za mu iya zama masu aminci kamar Allah?
7 Ta yaya za mu zama masu aminci kamar Jehobah? Hanya ɗaya ita ce ta wajen taimakon waɗanda suke cikin yanayi mai wuya. (Mis. 3:27) Alal misali, shin ka san wani ɗan’uwa da ya yi sanyin gwiwa wataƙila domin rashin lafiya ko don iyalinsa suna tsananta masa ko kuma don kasawarsa? Kana iya ƙarfafa mutumin da “zantattuka masu-alheri, masu-ƙarfafawa.” (Zak. 1:13)a Idan ka yi hakan, kana nuna cewa kai amini ne, “wanda ya fi ɗan’uwa mannewa.”—Mis. 18:24.
8. Ta yaya za mu kasance da aminci idan muna da aure?
8 Da akwai wasu hanyoyi kuma da za mu kasance da aminci ga waɗanda muke ƙauna. Alal misali, idan muna da aure, ya kamata mu kasance da aminci ga matarmu ko kuma mijinmu. (Mis. 5:15-18) Saboda haka, ya kamata mu guji kome da zai sa mu yi zina. (Mat. 5:28) Ƙari ga haka, muna nuna wa ’yan’uwanmu cewa mu masu aminci ne ta wajen ƙin yin gulma ko tsegumi, kuma ba za mu saurara ko kuma yi baƙar magana game da su ba.—Mis. 12:18.
9, 10. (a) Ga waye ne musamman za mu kasance da aminci? (b) Me ya sa bai da sauƙi mu riƙa yin biyayya ga Jehobah a koyaushe?
9 Mafi muhimmanci ma, muna bukatar mu kasance da aminci ga Jehobah. Ta yaya za mu iya yin hakan? Ta wajen son abin da Jehobah yake so da kuma ƙin abin da ya tsana. Sa’annan, wajibi ne mu yi rayuwa a hanyar da ke faranta wa Jehobah rai. (Karanta Zabura 97:10.) Idan muka koya kasancewa da ra’ayin Jehobah, zai fi sauƙi mu yi masa biyayya.—Zab. 119:104.
10 Hakika, bai da sauƙi a riƙa yi wa Jehobah biyayya a koyaushe. Wajibi ne mu yi ƙoƙari sosai don mu kasance da aminci a gare shi. Alal misali, wata Kirista da ba ta yi aure ba za ta so ta yi hakan. Amma, ba ta samu mutumin da ya dace ba tukun a cikin ƙungiyar Jehobah. (1 Kor. 7:39) Abokan aikinta da ba Shaidu ba suna iya neman haɗa ta da wani don su riƙa yin soyayya. Ko da yake ’yar’uwar za ta riƙa ji ta kaɗaita, amma ta ƙudura niyya cewa za ta kasance da aminci ga Jehobah. Kiristocin da suke jimre irin wannan yanayin, misali ne mai kyau na masu aminci. Jehobah zai albarkaci dukan waɗanda suka ci gaba da bauta masa da aminci a cikin yanayi mai wuya.—Ibran. 11:6.
JEHOBAH MAI GAFARTAWA NE
11. Mene ne yake nufi mutum ya riƙa gafartawa?
11 Mene ne gafartawa? Mutum mai gafartawa ba ya ci gaba da yin fushi da mutanen da suka ɓata masa rai. Hakan ba ya nufin cewa ya amince da abin da suka yi ko kuma ya yi kamar babu abin da ya faru. Maimakon haka, ya ƙi yin fushi ne kawai. Nassosi sun koya mana cewa Jehobah yana “hanzarin gafartawa.” Kuma yana yin hakan ga waɗanda suka tuba da gaske.—Zab. 86:5.
12. (a) Ta yaya Jehobah yake gafartawa? (b) Mene ne yake nufi “a shafe” zunubin mutum?
12 Ta yaya Jehobah yake gafartawa? Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah yana gafartawa “a yalwace” wato, gabaki ɗaya kuma har abada. (Isha. 55:7.) Ta yaya muka san cewa Jehobah yana gafartawa gabaki ɗaya? Ka yi la’akari da alkawari da ke Ayyukan Manzanni 3:19. (Karanta.) Manzo Bitrus ya gaya wa masu sauraronsa cewa, “ku tuba . . . ku juyo.” Mutumin da ya tuba da gaske zai tsai da shawara cewa ba zai sake maimaita zunubinsa ba. (2 Kor. 7:10, 11) Zai juyo, wato zai daina yin abin da bai dace ba kuma ya yi iya ƙoƙarinsa don ya faranta wa Allah rai. Idan waɗanda suka saurari Bitrus suka tuba da gaske, mene ne zai zama sakamakon? Bitrus ya ce, za “a shafe” zunubansu. Saboda haka, sa’ad da Jehobah ya gafarta mana, kamar ya shafe zunubanmu, wato ya gafarta gabaki ɗaya.—Ibran. 10:22; 1 Yoh. 1:7.
13. Mene ne kalamin nan “ba ni kuwa ƙara tuna da zunubinsu ba” ya tabbatar mana?
13 Ta yaya muka san cewa Jehobah ba ya tuna da zunubanmu idan ya gafarta mana? Mun koya yadda Jehobah yake gafarta wa mutane daga abin da ya gaya wa Irmiya a wani annabcin da ya yi game da Kiristoci shafaffu. (Karanta Irmiya 31:34.) Jehobah ya ce: “Zan gafarta muguntarsu, ba ni kuwa ƙara tuna da zunubinsu ba.” Saboda haka, muddin Jehobah ya gafarta mana, ba zai sake tuna da zunubanmu don ya hukunta mu ba.—Rom. 4:7, 8.
14. Me ya sa za mu ƙarfafa sa’ad da muka yi bimbini a kan yadda Jehobah yake gafarta wa mutane? Ka ba da misali.
14 Za mu ƙarfafa sa’ad da muka yi bimbini a kan yadda Jehobah yake gafarta mana. Alal misali, bari mu tattauna game da wata ’yar’uwa wadda za mu kira Elaine a wannan talifin. An yi mata yankan zumunci, sai aka dawo da ita bayan shekaru da yawa. Ta ce: “Ko da yake ina gaya wa kaina da kuma wasu cewa na gaskata Jehobah ya gafarta mini, amma ina ganin cewa ya fi ƙaunar wasu mutane.” Elaine ta ƙarfafa sa’ad da ta yi bimbini a kan yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta yadda Jehobah yake gafarta wa mutane. Alal misali, ta karanta cewa sa’ad da Jehobah ya gafarta zunubai, yana kamar ya tsarkake mu daga zunubanmu. Ba ma bukatar mu ji muna da alhakin zunubanmu a rayuwarmu ba.b Elaine ta ce: “Na fahimci cewa ban gaskata Jehobah yana iya gafarta mini ba, kuma ina ganin zan ɗauki wannan alhakin duk rayuwata. Ko da yake zai ɗauki lokaci in kusanci Jehobah sosai amma yanzu na soma ganin cewa zan iya yin hakan, kuma kamar an kawar mini da wata matsala.” Hakika, Jehobah Allah ne mai ƙauna da kuma gafarta wa mutane!—Zab. 103:9.
KA RIƘA GAFARTAWA KAMAR JEHOBAH
15. Ta yaya za mu iya yin koyi da yadda Jehobah yake gafarta wa mutane?
15 Za mu iya yin koyi da Jehobah ta wajen gafarta wa mutane. (Karanta Luka 17:3, 4.) Ka tuna cewa idan Jehobah ya gafarta wa mutum, ba zai ƙara tuna da abin da ya yi ba. Sa’ad da muka gafarta wa mutane, mu ma ya kamata mu manta da abin da suka yi mana kuma kada mu ƙara ambata kuskurensu a nan gaba.
16. (a) Shin gafarta wa mutane yana nufin mu yi na’am da zunubansu ko kuma mu ƙyale su su wulakanta mu? Ka bayyana. (b) Idan muna son Allah ya gafarta mana, me ya wajaba mu yi?
16 Gafarta wa mutane ba ya nufin cewa mun yi na’am da abin da suka yi ko kuma muna son a wulakanta mu ba. Amma, yana nufin ba ma son mu ci gaba da yin fushi da su. Kuma yana da muhimmanci mu tuna cewa idan muna son Jehobah ya gafarta mana, wajibi ne mu riƙa gafarta wa mutane. (Mat. 6:14, 15) Jehobah ya san cewa “mu turɓaya ne” da kuma ajizai. (Zab. 103:14) Saboda haka, sa’ad da wasu suka yi mana baƙar magana ko kuma suka ɓata mana rai, ya kamata mu tuna cewa su ajizai ne kamar mu, kuma zai dace mu gafarta musu da dukan zuciyarmu.—Afis. 4:32; Kol. 3:13.
17. Mene ne zai taimaka maka ka gafarta wa mutumin da ya ɓata maka rai?
17 Hakika, ba shi da sauƙi mu riƙa gafarta wa mutane. A zamanin Bulus, wasu Kiristoci shafaffu sun bukaci taimako don su warware matsalolin da ke tsakaninsu. (Filib. 4:2) Idan ɗan’uwa ya ɓata mana rai, mene ne zai iya taimaka mana mu gafarta masa? Ka yi la’akari da Ayuba. Eliphaz da Bildad da Zophar sun ce su abokansa ne, amma sun zarge shi cewa ya yi munanan abubuwa, kuma hakan ya ɓata wa Ayuba rai sosai. (Ayu. 10:1; 19:2) Jehobah ya tsauta wa waɗannan abokan ƙarya. Ya gaya musu su je su sami Ayuba kuma su miƙa hadayu don zunubansu. (Ayu. 42:7-9) Amma, Jehobah ya gaya wa Ayuba ya ɗauki mataki. Mene ne zai yi? Ya ce ya yi musu addu’a. Ayuba ya yi hakan, kuma Jehobah ya albarkace shi don ya gafarta musu. (Karanta Ayuba 42:10, 12, 16, 17.) Wane darasi ne muka koya? Idan ka yi wa wanda ya ɓata maka rai addu’a, hakan zai taimake ka ka daina fushi da shi.
KA CI GABA DA FAHIMTAR HALAYEN JEHOBAH
18, 19. Ta yaya za mu ci gaba da fahimtar halaye masu kyau na Jehobah?
18 Mun ji daɗin koyon halayen Jehobah. Mun koyi cewa yana da sauƙin hali, ba ya son kai, shi mai karimci ne da mai sanin yakamata da aminci kuma yana gafarta wa mutane. Hakika, da akwai ƙarin abubuwa da za mu koya game da Jehobah. Muna iya koya game da shi har abada. (M. Wa. 3:11) Mun yarda da manzo Bulus wanda ya ce: “Oh! zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa!” Muna iya faɗin hakan game da ƙauna da kuma halaye shida da muka tattauna a waɗannan talifofin.—Rom. 11:33.
19 Bari mu ci gaba da ƙara koyo game da halayen Jehobah, mu yi bimbini a kansu kuma mu nuna su a rayuwarmu. (Afis. 5:1) Yayin da muka yi hakan, za mu yarda da marubucin zabura wanda ya ce: “Ya yi mini kyau in kusanci Allah.”—Zab. 73:28.
a Za ka samu shawarwari masu kyau a cikin talifin nan “Tsokana Zuwa ga Ƙauna da Nagargarun Ayuka—Ƙaƙa?” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu, 1995.
b Ka duba littafin nan Ka Kusaci Jehovah, babi na 26, sakin layi na 10.