Za Ka Yi Sadaukarwa Don Mulkin Kuwa?
“Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.”—2 KOR. 9:7.
1. Waɗanne irin sadaukarwa ne mutane suke yi, kuma me ya sa?
MUTANE suna sadaukarwa saboda abubuwan da ke da muhimmanci a gare su. Iyaye suna sadaukar da lokacinsu da kuɗinsu da kuma kuzarinsu don ’ya’yansu su amfana. Matasa ’yan wasa da ke da burin yin gasa a Olimfik sukan yi sa’o’i da dama kowace rana suna koyo da kuma horar da kansu yayin da tsaransu suke jin daɗin rayuwa. Yesu ma ya yi sadaukarwa don abubuwan da ke da muhimmanci a gare shi. Bai biɗi rayuwar jin daɗi ba kuma bai yi burin haifan ’ya’ya ba. A maimakon haka, ya yi amfani da ƙarfinsa don tallafa wa Mulkin Allah. (Mat. 4:17; Luk 9:58) Mabiyansa ma sun yi sadaukarwa da yawa. Mulkin Allah shi ne abin da ya fi muhimmanci a rayuwarsu, kuma hakan ne ya sa suka yi sadaukarwa. (Mat. 4:18-22; 19:27) Ya kamata mu tambayi kanmu, ‘Mene ne ya fi muhimmanci a rayuwata?’
2. (a) Waɗanne irin sadaukarwa ne ya zama wajibi ga dukan Kiristoci na gaske? (b) Waɗanne ƙarin sadaukarwa ne wasu suke yi?
2 Wajibi ne dukan Kiristoci na gaske su yi wasu sadaukarwa idan suna so su kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Waɗannan sadaukarwar sun ƙunshi ba da lokaci da kuzari don yin addu’a da karanta Littafi Mai Tsarki da bauta ta iyali da halartan taro da kuma fita wa’azi.a (Josh. 1:8; Mat. 28:19, 20; Ibran. 10:24, 25) Saboda ƙoƙarinmu da kuma albarkar Jehobah, aikin wa’azi yana ci gaba sosai kuma mutane da yawa suna zuwa “dutse na gidan Ubangiji.” (Isha. 2:2) Don su tallafa wa ayyukan Mulki, ’yan’uwa da yawa sun ba da kansu don yin hidima a Bethel ko gina Majami’un Mulki da Majami’un Manyan Taro ko tsara taron gunduma ko kuma taimakawa a lokacin bala’i. Ba a bukatar wannan ƙarin sadaukarwar don a sami rai na har abada, amma yin hakan yana da muhimmanci domin yana sa mu tallafa wa al’amuran Mulki.
3. (a) Ta yaya muke amfana sa’ad da muka yi sadaukarwa saboda Mulkin? (b) Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi la’akari da su?
3 Yanzu ne ya fi muhimmanci mu yi iya ƙoƙarinmu don tallafa wa Mulkin. Abin farin ciki ne cewa mutane da yawa suna yin sadaukarwa da son rai. (Karanta Zabura 54:6.) Idan muka yi irin waɗannan sadaukarwar, za mu yi farin ciki yayin da muke jiran Mulkin Allah ya zo. (K. Sha 16:15; A. M. 20:35) Ya kamata mu tambayi kanmu: Shin akwai hanyoyin da zan iya yin sadaukarwa don Mulkin? Ta yaya nake amfani da lokacina da kuɗaɗena da kuma kuzarina? Waɗanne abubuwa ne ya kamata in yi la’akari da su yayin da nake sadaukarwa? Bari mu tattauna wasu darussa da za mu iya koya daga waɗanda suka yi sadaukarwa da son rai. Hakan zai sa mu daɗa yin farin ciki.
HADAYUN DA AKA YI A ISRA’ILA TA DĀ
4. Ta yaya Isra’ilawa suka amfana daga yin hadayu?
4 Isra’ilawa na dā sun yi hadayu domin a gafarta zunubansu. Ya wajaba su yi hadayu idan suna son Jehobah ya amince da su. Wasu daga cikin hadayun wajibi ne, wasu kuma ana yi da son rai ne. (Lev. 23:37, 38) Za su iya yin hadayun ƙonawa da son rai a matsayin kyauta ga Jehobah. Wani misali na hadayu shi ne wanda aka yi a lokacin keɓe haikali a zamanin Sulemanu.—2 Laba. 7:4-6.
5. Wane tanadi ne Jehobah ya yi don talakawa?
5 Jehobah ya san cewa kowa ba zai iya ba da hadaya iri ɗaya ba. Saboda haka, ya bukaci kowa ya ba da gwargwadon iyawarsa. Jehobah ya ba da doka cewa a yi hadayar dabba kuma a zubar da jinin. Waɗannan hadayun “ishara ce kawai ta kyawawan abubuwan da ke gaba” ta wajen Ɗansa, Yesu. (Ibran. 10:1-4, Littafi Mai Tsarki) Duk da haka, Jehobah ya nuna sanin yakamata sa’ad da ya kafa dokar. Alal misali, ya amince da hadayar tantabaru idan mutumin ba zai iya ba da akuya ko tunkiya ba. Saboda da haka, talakawa ma sun yi farin cikin ba da hadaya ga Jehobah. (Lev. 1:3, 10, 14; 5:7) Ko da yake Jehobah ya amince da hadayun dabbobi dabam-dabam, amma ya bukaci abubuwa biyu daga duk wanda ya yi hadaya da son rai.
6. Waɗanne abu biyu ne ake bukata daga kowane mutum mai yin hadayu, kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci?
6 Na farko, mutumin yana bukatar ya ba da abu mafi kyau. Idan dabbar ba ta da ƙoshin lafiya ko kuma gurguwa ce, Jehobah ba zai amince da hadayar ba. (Lev. 22:18-20) Na biyu, mai yin hadayar yana bukata ya kasance mai tsarki kamar yadda aka bayyana a cikin Dokar. Idan mutumin bai da tsarki, wajibi ne ya yi hadaya ta zunubi tukuna don ya gyara dangantakarsa da Jehobah kafin ya iya ba da hadaya na son rai. (Lev. 5:5, 6, 15) Wannan batu ne mai muhimmanci. Jehobah ya ba da doka cewa a hukunta duk wanda bai tsarkake kansa ba kafin ya ci hadayu na salama, wanda zai iya zama hadaya ta son rai. (Lev. 7:20, 21) Amma idan mutumin mai tsarki ne kuma hadayarsa babu aibi, zai yi farin ciki sosai.—Karanta 1 Labarbaru 29:9.
YIN SADAUKARWA A YAU
7, 8. (a) Wane farin ciki ne waɗanda suke yin sadaukarwa don Mulkin suke morewa? (b) Waɗanne abu ne za mu iya yin sadaukarwa da su?
7 A yau, mutane da yawa suna ba da kansu da yardar rai a bautar Jehobah, kuma hakan yana sa Jehobah farin ciki. Yin aiki tuƙuru don taimaka wa ’yan’uwanmu yana sa mu farin ciki. Wani ɗan’uwa da ke saka hannu a gina Majami’un Mulki da kuma taimaka wa waɗanda bala’i ya faɗa musu ya ce ba zai iya kwatanta irin farin ciki da yake yi ba sa’ad da yake taimaka wa ’yan’uwansa. Ya daɗa cewa, “Ganin yadda ’yan’uwa suke farin ciki da godiya bayan sun shiga sabuwar Majamiar Mulki ko kuma sa’ad da suka sami agaji bayan aukuwar wani bala’i, kwalliya ce da ta biya kuɗin sabulu.”
8 Ƙungiyar Jehobah da ke duniya ta nemi hanyoyin tallafa wa Mulkin a kowane lokaci. A shekara ta 1904, Ɗan’uwa Charles Taze Russell ya rubuta cewa: “Kowannenmu ya ƙoƙarta ya yi amfani da lokacinsa da ikonsa da kuɗinsa da dai sauransu, don ɗaukaka Jehobah.” Ko da yake yin sadaukarwa ga Jehobah yana bukatar ba da wani abu, amma yin hakan zai sa mu sami albarka sosai. (2 Sam. 24:21-24) Shin za mu iya yin amfani da dukiyarmu don tallafa wa Mulkin?
9. Mene ne muka koya daga littafin Luka 10:2-4 game da yin amfani da lokacinmu?
9 Lokacinmu. Yana ɗaukan lokaci sosai kafin a iya fassara da kuma buga littattafanmu ko gina wajajen ibada ko yin shirye-shiryen taron gunduma ko yi wa waɗanda suka fuskanci bala’i agaji ko kuma yin wasu ayyuka da dama masu muhimmanci. Ko da yake muna da sa’o’i ashirin da huɗu kaɗai a rana, Yesu ya ba mu wata ƙa’ida da za ta iya taimaka mana mu yi amfani da lokacinmu yadda ya dace. Sa’ad da Yesu yake tura almajiransa wa’azi, ya ce kada su “yi doguwar gaisuwa da kowa a hanya.” (Luk 10:2-4, LMT) Me ya sa Yesu ya ba da wannan umurnin? Wani masanin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutanen dā ba sa durƙusawa ko kuma su sha hannu sa’ad da suke gaisuwa kamar yadda muke yi a yau, amma suna rungumar juna sau da sau har ma su kwanta ƙasa. Yin hakan na bukatar lokaci sosai.” Yesu ba ya ƙarfafa mabiyansa su yi taurin kai, amma yana so su san cewa ba su da lokaci sosai kuma suna bukatar su fi amfani da lokacinsu wajen yin ayyuka mafi muhimmanci. (Afis. 5:16) Shin za mu iya bin wannan ƙa’idar don mu iya samun isashen lokacin tallafa wa Mulkin?
10, 11. (a) A waɗanne hanyoyi ne ake yin amfani da gudummawar da muke yi? (b) Wace ƙa’ida ce da ke 1 Korintiyawa 16:1, 2 za ta iya taimaka mana?
10 Kuɗinmu. Ana bukatar kuɗi mai yawa don tallafa wa aikin dukan duniya. A kowace shekara, ana kashe miliyoyin daloli don a biya bukatun masu kula masu ziyara da majagaba na musamman da kuma masu wa’azi a ƙasashen waje. Tun daga shekara ta 1999, an gina Majami’un Mulki fiye da 24,500 a wasu ƙasashen da ’yan’uwanmu ba sa da kuɗi sosai. Duk da haka, ana bukatar ƙarin Majami’un Mulki guda 6,400. A kowane wata, ana buga mujallun Hasumiyar Tsaro da kuma Awake! guda miliyan 100. Ana goyon bayan waɗannan ayyukan da gudummawar da kuke yi da son rai.
11 Jehobah ya hure manzo Bulus ya rubuta wata ƙa’idar da za mu bi sa’ad da muke ba da gudummawa. (Karanta 1 Korintiyawa 16:1, 2.) Ya ƙarfafa ’yan’uwansa da ke Koranti cewa kada su jira sai ƙarshen mako kafin su ƙayyade yawan kuɗin da za su bayar, amma su yi hakan tun daga farkon makon. Kamar yadda ake yi a ƙarni na farko, ’yan’uwa a yau suna shiri tun da wuri don su ba da gudummawa da yardar rai. (Luk 21:1-4; A. M. 4:32-35) Jehobah yana daraja yadda bayinsa suke yin gudummawa.
12, 13. Mene ne zai iya hana wasu saka hannu a hidimar Jehobah, amma ta yaya Jehobah zai taimaka musu?
12 Kuzarinmu da kuma ƙwarewarmu. Jehobah yana tallafa mana yayin da muke ƙoƙartawa wajen yin amfani da kuzarinmu da kuma ƙwarewarmu don Mulkin. Ya yi alkawari cewa zai taimaka mana sa’ad da muka kasala. (Isha. 40:29-31) Shin muna ji cewa ba za mu iya taimaka a wannan aikin ba domin ba mu ƙware ba? Muna yin tunani cewa akwai wasu da suka fi mu ƙwarewa? Ka tuna cewa, Jehobah zai iya ƙara maka iyawa, kamar yadda ya yi wa Bezalel da Oholiab.—Fit. 31:1-6; ka duba hoton da ke farkon talifin nan.
13 Jehobah ya ƙarfafa mu cewa kada mu ƙyale kome ya hana mu yin iya ƙoƙarinmu don Mulkin. (Mis. 3:27) Sa’ad da ake sake gina haikalin da ke Urushalima, Jehobah ya gaya wa Yahudawa da ke wurin cewa su riƙa tunani sosai a kan yadda suke tallafa wa aikin ginin. (Hag. 1:2-5) Sun ƙyale wasu abubuwa su janye hankalinsu daga aikin. Ya kamata mu bincika ko abubuwan da muka fi biɗa sun jitu da nufin Jehobah. Shin za mu iya yin tunani sosai game da rayuwarmu da kuma shirya yadda za mu daɗa ƙwazo wajen tallafa wa Mulkin Allah a ƙarshen zamanin nan?
KA YI SADAUKARWA IYA GWARGWADONKA
14, 15. (a) Ta yaya misalin ’yan’uwanmu da ba su da kuɗi sosai ya ƙarfafa ka? (b) Mene ne ya kamata mu ƙudura yi?
14 Mutane da yawa suna zama a ƙasashen da wahala da kuma talauci suka zama gama gari. Ƙungiyarmu tana taimaka wa ’yan’uwa da ke irin waɗannan ƙasashen. (2 Kor. 8:14) Amma, har ’yan’uwanmu da ba su da kuɗi sosai suna ɗaukan gatan yin gudummawa da tamani. Sa’ad da Jehobah ya ga yadda talakawa suke ba da gudummawa da farin ciki, hakan yana faranta masa rai.—2 Kor. 9:7.
15 A wata ƙasa a Afirka da ake talauci sosai, wasu ’yan’uwa sukan nome kayan lambu a wani ɓangaren gonarsu, sai su sayar da amfanin kuma su tallafa wa hidimar Mulkin da kuɗin. A wannan ƙasar kuma, ’yan’uwan suna so su taimaka a wani Majami’ar Mulki da ake ginawa. Amma aikin ya faɗa a daidai lokacin da suke noma. Da yake sun ƙudura za su taimaka, sukan saka hannu a aikin gina Majami’ar Mulkin da rana, sa’an nan da yamma sai su je shuki a gonarsu. Babu shakka, wannan halin sadaukarwa ne! Hakan ya tuna mana ’yan’uwan da ke Makidoniya a ƙarni na farko. “Duk da talaucinsu ainu,” sun roƙi Bulus ya bar su su tallafa wa ’yan’uwansu da ɗan kuɗin da suke da shi. (2 Kor. 8:1-4) Hakazalika, bari kowannenmu ‘ya bayar gwargwadon albarkar Ubangiji Allahnmu wadda ya ba mu.’—Karanta Kubawar Shari’a 16:17.
16. Ta yaya za mu iya tabbata cewa Jehobah zai aminci da sadaukarwar da muke yi?
16 Sa’ad da muke yin sadaukarwa, ya kamata mu mai da hankali don kada mu yi sakaci da abubuwa mafi muhimmanci, kamar kula da iyalinmu. Kamar yadda Isra’ilawa a dā suka yi, wajibi ne mu tabbata cewa Jehobah yana amincewa da sadaukarwar da muka yi da yardar rai. Muna bukatar mu tuna cewa iyalinmu da kuma ibadarmu ga Jehobah ne suka fi muhimmanci. Bai kamata mu ƙi taimaka wa iyalinmu su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah, wai don muna so mu ba da lokaci da abubuwan da muke da su don taimaka ma wasu ba. Ƙari ga haka, ba zai yiwu mu ba Jehobah lokaci da kuzari da kuma wasu abubuwan da ba mu da su ba. (Karanta 2 Korintiyawa 8:12.) Kuma wajibi ne mu ci gaba da ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah don kada ya ƙi amincewa da bautarmu. (1 Kor. 9:26, 27) Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa idan muka yi rayuwar da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, sadaukarwar da muke yi za ta sa mu farin ciki kuma Jehobah zai amince da ita.
SADAUKARWARMU TANA DA TAMANI SOSAI
17, 18. Yaya muke ɗaukan waɗanda suke sadaukarwa don Mulkin, kuma me ya kamata mu yi la’akari da shi?
17 ’Yan’uwanmu da yawa suna ba da lokacinsu da kuzarinsu da kuma kuɗaɗensu wajen tallafa wa aikin Mulkin. (Filib. 2:17) Muna godiya sosai ga waɗanda suke yin hakan. Muna kuma yaba wa yara da kuma matan da mazajensu suke sadaukarwa da son rai don su iya kula da ayyukan Mulkin Allah.
18 Ana bukata a yi aiki tuƙuru don a iya tallafa wa ayyukan Mulkin. Bari kowannenmu ya yi addu’a kuma ya yi tunani sosai a kan yadda zai iya ƙoƙartawa wajen tallafa wa ƙungiyar Jehobah. Za mu iya kasancewa da gaba gaɗi cewa za mu sami lada yanzu kuma za ta daɗa ƙaruwa a “cikin zamani mai-zuwa.”—Mar. 10:28-30.
a Ka duba talifin nan “Ba da Hadayu da Dukan Zuciyarmu ga Jehobah” a fitowar Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Janairu, 2012, shafuffuka na 21-25.