Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w15 10/15 pp. 14-17
  • Ya Tsai da Shawara Mai Kyau Sa’ad da Yake Matashi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ya Tsai da Shawara Mai Kyau Sa’ad da Yake Matashi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • NIKOLAI YA BAYYANA YADDA YA KOYI GASKIYA
  • BUGA LITTATTAFAI
  • MATSALOLIN YIN AIKI A GIDAN KASA
  • AN KAMA NIKOLAI
  • YA CI GABA DA KASANCEWA DA AMINCI
  • Babu Abin da Ya Gagari Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
w15 10/15 pp. 14-17
Nikolai Dubovinsky

Tarihi

Ya Tsai da Shawara Mai Kyau Sa’ad da Yake Matashi

Ilve Apanyuk ce ta ba da labarin

Ilve Apanyuk

BABBAN kawuna Nikolai Dubovinsky ya rubuta tarihinsa game da ibadarsa ga Jehobah, wato yanayi na farin ciki da wahala da ya fuskanta a lokacin mulkin tarayyar Soviet ta dā, sa’ad da aka hana aikin Shaidun Jehobah da kuma bayan haka. Ya rubuta wannan labarin ne a shekarunsa na karshe a rayuwa. Ya kasance da aminci da kwazo kuma duk da cewa ya fuskanci kalubale da kuma matsaloli, ya ji daɗin rayuwa. Nikolai yana son matasa su ji labarinsa. Saboda haka, zan bayyana wasu abubuwa masu muhimmanci da suka faru da shi. An haife shi a shekara ta 1926 kuma iyalinsu manoma ne a kauyen Podvirivka da ke yankin Chernivtsi Oblast a kasar Yukiren.

NIKOLAI YA BAYYANA YADDA YA KOYI GASKIYA

Kawu Nikolai ya fara da cewa: “Wata rana a shekara ta 1941, yayana Ivan ya kawo wasu mujallun Hasumiyar Tsaro da littattafan nan The Harp of God da The Divine Plan of the Ages da kasidu da dama. Na karanta su duka kuma na koyi cewa Shaiɗan ne sanadin dukan wahalolin da muke sha a duniya, ba Allah ba. Hakan ya ba ni mamaki. Na karanta linjila tare da mujallun kuma hakan ya sa na san gaskiyar da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Na yi farin cikin gaya wa mutane abin da na koya game da Mulkin Allah da kwazo. Yayin da na karanta waɗannan mujallu, sai na kara fahimtar gaskiyar kuma hakan ya sa na kasance da burin zama mai bauta wa Jehobah.

“Na san cewa zan sha wahala saboda imanina. A lokacin ana yaki kuma ba na son in yi kisa. Sai na fara haddace ayoyin Littafi Mai Tsarki kamar Matta 10:28 da 26:52 don na shirya kaina saboda gwaji da ke tafe. Na yanke shawara cewa zan kasance da aminci ga Jehobah ko da za a kashe ni!

“Sa’ad da na kai ɗan shekara sha takwas, wato a shekara ta 1944, doka ta bukace ni in shiga aikin soja. Saboda haka, sai aka kai ni inda ake ɗaukan mutane a aikin soja. A nan ne na fara haɗuwa da wasu Shaidun Jehobah, matasa kamar ni. Mun gaya wa hukuma cewa ba za mu saka hannu a yaki ba. Saboda haka, hafsan da hukumar ta aika ya ji haushi kuma ya ce zai hana mu abinci, ya tilasta mana mu haka ramuka ko kuma ya harbe mu. Ba mu ji soro ba kuma muka ce: ‘Muna hannunka. Ka yi mana abin da ka ga dama amma ba za mu karya dokar Allah da ta ce: “Ba za ka yi kisankai ba.”’—Fit. 20:13.

“An tura ni da wasu ’yan’uwa biyu zuwa kasar Belarus don mu je mu yi aiki a gonaki kuma mu gyara gidajen da suka lalace. Ba zan taɓa manta da ɓarnan da yaki ta yi a bayan garin Minsk ba. Bishiyoyi da suka kone suna kwance a kan hanya. Gawawwakin mutane da kuma na dawaki da suka kumbura suna ko’ina a cikin ramuka da kuma jeji. Na ga taragwai da kayan yaki har da tarkacen jirgin da ya faɗi. Hakika, na ga sakamako karya dokokin Allah.

“An daina yakin a shekara ta 1945. Duk da haka, kotu ta yanke mana hukuncin shekara goma a gidan yari don mun ki shiga aikin soja. Mun yi shekara uku ba ma yin taro kuma ba ma samun littattafai. Amma mun tuntuɓi wasu ’yan’uwa mata ta wasika. Daga baya, aka kama su kuma aka yanke musu hukuncin shekara 25 a sansanin aiki.

“Bayan haka, an sake mu a shekara ta 1950 kuma muka koma gida. Mahaifiyata da kanwata Maria sun zama Shaidun Jehobah a lokacin da nake gidan yari, amma yayuna suna kan nazarin Littafi Mai Tsarki! Hukumar tsaro ta Soviet ta so ta sake tura ni gidan yari saboda na ci gaba da yin wa’azi da kwazo. Sa’ad da na kai shekara 24 wani ɗan’uwa da yake shugabantar aikinmu ya ce in taimaka wajen buga littattafanmu a wani gidan kasa.”

BUGA LITTATTAFAI

“Shaidun Jehobah su sha faɗa cewa, ‘Idan an hana aikin bishara ta Mulki, za a ci gaba da yin sa a ɓoye.’ (Mis. 28:28) A wannan lokacin, yawancin aikin buga littattafanmu ana yin su ne a ɓoye a gidan kasa. Na fara yin aikin buga littattafai a gidan kasa da ke inda yayana Dmitry yake. A wani lokacin, ba na barin ɗaki har na sati biyu. Idan fitilar ta mutu saboda rashin iska, sai in kwanta kuma in jira har sai ɗakin ya sake cika da iska.

Zanen gidan kasa a karkashin gidan da Nikolai yake buga littattafai

Zanen gidan kasa a karkashin gidan da Nikolai yake buga littattafai

“Wata rana, ɗan’uwa da nake aiki da shi ya tambaye ni ‘Nikolai, ka yi baftisma kuwa?’ Ko da shi ke na yi hidima na shekara 11 a bautar Jehobah amma ban yi baftisma ba. Saboda haka, ya tattauna batun da ni kuma aka yi min baftisma a daddare a wani tafki. A lokacin ina ɗan shekara 26. Bayan shekara uku na sami karin ayyuka, na zama memban Kwamitin na Kasa. A lokacin ana naɗa ’yan’uwa don su maye gurbin ’yan’uwa da aka kama su. Saboda haka, aikin bishara ta Mulki ta ci gaba.”

MATSALOLIN YIN AIKI A GIDAN KASA

“Aikin buga littattafai a gidan kasa yana da wuya fiye da zama a gidan yari! Da yake ba na so ’yan sandan ciki su kama ni, na yi shekara bakwai ban halarci taro ba. Saboda haka, na karfafa dangantakata da Jehobah da kaina. Ba na yawan ganin ’yan gidanmu sai in na ziyarce su. Amma sun fahimci yanayin da nake ciki kuma sun karfafa ni. Yawan damuwa da kuma kokarin guje wa ’yan sanda ya gajiyar da ni sosai. Muna bukatar mu kasance a shirye don ba mu san abin da zai faru ba. Alal misali, wata rana da yamma ’yan sanda guda biyu sun zo gidan da nake. Na yi tsalle na fita ta tagar gidan kuma na shiga cikin daji a guje. Ina jin wani irin kara yayin da nake gudu. Sa’ad da na ji harbin bindiga, sai na gane cewa karar da na ji na harsashi ne! Ɗaya daga cikin waɗanda suka bi ni ya hau kan doki kuma ya rika harbi har harsashin suka kare. Amma ya harbe ni a hannu. A karshe na tsira sa’ad da na ɓuya a wani jeji bayan na yi kilomita 5 ina gudu. Daga baya, sa’ad da ake shari’a a kotu sai aka gaya mini cewa sun yi harbi har so 32 amma bai same ni ba.

“Da yake ina yawan zama a gidan kasa, na yi fari kamar wanda ba shi da jini a jiki. Hakan ya sa mutane sun san abin da nake yi. Saboda haka, sai na soma zama a cikin rana. Zama a gidan kasa ya shafi lafiyar jikina har ila. A wani lokaci ban iya halartan wani taro mai muhimmanci da ’yan’uwa ba don jini na fita daga hancina da kuma bakina.”

AN KAMA NIKOLAI

Nikolai Dubovinsky a wani sansanin aiki a kasar Mordvinia a shekara ta 1963

A sansanin aiki a kasar Mordvinia a shekara ta 1963

“An kama ni a ranar 26 ga Janairu a shekara ta 1957. Bayan wata 6, sai Kotun Koli na kasar Yukiren ta yanke mini hukuncin kisa kuma aka ce za a harbe ni. Amma tun da doka ta kawar da irin wannan hukuncin a kasar, sai kotu ta canja zuwa ɗaurin shekara 25 a gidan yari. Mu takwas ne aka tura a sansanin aiki. An tura mu aiki a kasar Mordvinia, kuma Shaidun Jehobah da ke kasar sun yi kusan 500. Muna haɗuwa a asirce kuma a kananan rukunoni don mu yi nazarin Hasumiyar Tsaro. Bayan da wani ma’aikacin tsaro ya bincika wasu tsofaffin mujallunmu, sai ya ce: ‘Idan kuka ci gaba da karanta waɗannan mujallu, ba za a iya canja ra’ayin ku ba!’ Kowace rana muna aiki da kwazo, a wani lokaci ma muna yin aiki fiye da wanda aka ba mu. Duk da haka, shugaban sansanin ya ce: ‘Aikin da kuke yi a nan bai da muhimmanci a gare mu. Abin da muke bukata kawai a gare ku shi ne ku ba da haɗin kai kuma ku yi biyayya ga gwamnatin kasar.’”

“Kowace rana muna aiki da kwazo, a wani lokaci ma muna yin aiki fiye da wanda aka ba mu”

YA CI GABA DA KASANCEWA DA AMINCI

Majami’ar Mulki a garin Velikiye Luki

Wata Majami’ar Mulki a garin Velikiye Luki

Bayan da aka fito da shi daga sansanin a shekara ta 1967, Kawu Nikolai ya taimaka wajen shirya ikilisiyoyi a kasar Estonia da kuma birnin St. Petersburg a kasar Rasha. A shekara ta 1991 ne, aka sauke hukuncin da aka yi masa shekaru 34 kafin wannan lokacin saboda babu hujja da ta nuna ya aikata laifi. A wannan lokacin ne aka sake Shaidun Jehobah da yawa da suka sha wahala a karkashin hukumomi. A shekara ta 1996, Nikolai ya koma birnin Velikiye Luki a yankin Pskov Oblast da ke da nisan kilomita 500 daga St. Petersburg. Ya sayi wani karamin gida, kuma aka gina Majami’ar Mulki a wajen a shekara ta 2003. A yau ikilisiyoyi biyu ne suke amfani da Majami’ar Mulkin.

Ni da mijina muna hidima a ofishin Shaidun Jehobah na kasar Rasha. ’Yan watanni kafin mutuwarsa, Kawu Nikolai ya yi mana ziyara ta karshe a watan Maris na shekara ta 2011. Abin da ya faɗa ya ratsa zuciyarmu yayin da yake fara’a kuma ya ce: “Daga dukan alamu, an soma zagaye ta bakwai don kewaye Jericho.” (Josh. 6:15) Yana nufin karshen duniya tana nan tafe. A lokacin shekararsa 85 ne. Ko da shike rayuwarsa ba ta kasance da sauki ba, amma ya kwatanta hakan ta cewa: “Ina farin cikin cewa sa’ad da nake matashi, na yanke shawarar bauta wa Jehobah kuma ban yi nadamar yin haka ba!”

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba