TARIHI
Babu Abin da Ya Gagari Jehobah
WATA rana da matata Mairambubu take cikin bas, sai ta ji wata mata ta ce: “Mutuwa ba za ta ƙara kasancewa ba kuma za a ta da matattu.” Hakan ya sa ta so ta sami ƙarin bayani. Da motar ta tsaya kuma fasinjoji suka sauka, sai ta bi matar da ta yi wannan maganar. Sunan matar Apun Mambetsadykova ne, kuma ita Mashaidiyar Jehobah ce. A lokacin, tattaunawa da Shaidun Jehobah babban laifi ne. Amma abin da Apun ta koya mana ya canja rayuwarmu daga baya.
MUNA AIKI DAGA ASUBA HAR YAMMA
An haife ni a shekara ta 1937, a wata babbar gona da ke kusa da garin Tokmok a ƙasar Kyrgyzstan. Mu mutanen Kyrgyzstan ne kuma muna yaren Kyrgyzanci. Iyayena manoma ne kuma suna aiki a gona daga asuba har yamma. Ana ba masu aiki a gonar abinci, amma sau ɗaya ne kawai ake biyan su albashi a shekara. Bai yi wa mahaifiyata sauƙi ta kula da ni da ƙanwata ba. Saboda haka, na bar makaranta na soma aiki a gonar, bayan na yi shekara biyar kawai ina makaranta.
Tudun Teskey Ala-Too
Akwai talauci sosai a yankinmu, kuma biyan bukatunmu na da wuya sosai. Ƙari ga haka, sa’ad da nake matashi, ban yi tunanin ma’anar rayuwa ba ko kuma abin da zai faru a nan gaba. Saboda haka, ban taɓa tsammani cewa sanin Jehobah Allah da kuma nufinsa zai canja rayuwata ba. Jin yadda ’yan Kyrgyzstan suka soma koya game da Jehobah da kuma yadda aka yi wa’azi a ƙasar gabaki ɗaya, labari ne mai ƙayatarwa. Kuma hakan ya soma ne a yankinmu da ke arewacin Kyrgyzstan.
MASU ZAMAN BAUTA SUN KOYAR DA GASKIYA A KYRGYZSTAN
Mutane a Kyrgyzstan sun soma koya game da Jehobah a shekara ta 1956. Don su yi hakan, suna bukatar su guji ra’ayin ’yan kwaminisanci. Me ya sa? Domin a lokacin, ƙasar Kyrgyzstan tana haɗe da Ƙasar Rasha ta Dā. Amma a dukan ƙasashen, Shaidun Jehobah ba sa saka hannu a batun siyasa. (Yoh. 18:36) Shi ya sa gwamnatin Kwaminisanci suka ɗauke su abokan gāba kuma suna tsananta musu. Amma ba abin da zai hana mutane masu zuciyar kirki koya game da Kalmar Allah. Hakika, ɗaya cikin darussan da na koya a rayuwata shi ne cewa, ga Jehobah ‘abubuwa duka za su yiwu.’—Mar. 10:27.
Emil Yantzen
Tsananta wa Shaidun Jehobah ya sa sun daɗa yawa a ƙasar. Ta yaya hakan ya faru? Yankin Saiberiya na haɗe da ƙasar Rasha ta Dā, kuma wurin ne ake tura waɗanda ake ganin su abokan gāban gwamnati ne zaman bauta. Saboda haka, da yawa cikinsu sun soma zama a Kyrgyzstan sa’ad da aka sako su. Kuma wasu da suke bauta wa Jehobah sun koya wa mutane game da shi. Wani mai suna Emil Yantzen da aka haifa a Kyrgyzstan a shekara ta 1919 yana cikin waɗanda aka tura zaman bauta. Emil ya haɗu da Shaidu a sansanin aiki, sai ya soma bauta wa Jehobah kuma ya dawo gida a 1956. Emil ya zauna kusa da garin Sokuluk da ke kusa da yankinmu. A garin Sokuluk ne aka kafa ikilisiya ta farko a Kyrgyzstan a 1958.
Victor Vinter
Bayan wajen shekara ɗaya, wani ɗan’uwa mai suna Victor Vinter ya ƙaura zuwa garin Sokuluk. Shi mai aminci ne kuma ya sha wahala sosai. An saka shi cikin kurkuku sau da yawa don amincinsa. A ƙaro na farko, ya yi shekara uku, bayan haka, ya sake yin shekara uku. Ban da haka, ya ƙara yin shekara goma a fursuna kuma ya yi zaman bauta shekara biyar. Har ila, tsanantawa bai hana mutane wa’azi da kuma bauta wa Jehobah ba.
AN SOMA WA’AZI KUSA DA GARINMU
Eduard Varter
A shekara ta 1963, da akwai Shaidu kusan 160 a ƙasar Kyrgyzstan. Da yawa daga cikinsu sun fito ne daga ƙasar Jamus da Yukiren da kuma Rasha. Wani mai suna Eduard Varter yana cikinsu kuma ya yi baftisma a Jamus a 1924 kafin aka tura shi zaman bauta. A tsakanin 1940 zuwa 1949, ’yan Nazi suka tura shi sansani. Kuma bayan wasu shekaru, ’yan Kwaminis da ke ƙasar Rasha ta dā suka tura Eduard zaman bauta. A shekara ta 1961, wannan ɗan’uwa mai aminci ya ƙaura zuwa garin Kant da ke kusa da garinmu.
Elizabeth Fot; Aksamai Sultanalieva
Wata ’yar’uwa mai suna Elizabeth Fot mai aminci sosai ga Jehobah tana zama a garin Kant kuma tana ɗinki. Domin ta iya ɗinki sosai, likitoci da malamai suna sayan tufafi daga wurinta. Wata mata mai suna Aksamai Sultanalieva kwastomarta ce, kuma mijin matar lauyan gwamnati ne. Sa’ad da Aksamai ta zo sayan wasu tufafi daga wurin Elizabeth, ta yi mata tambayoyi da yawa game da rayuwa da kuma yanayin matattu. Elizabeth ta amsa tambayoyinta daga Littafi Mai Tsarki. Daga baya, ta zama mai wa’azi da ƙwazo sosai.
Nikolai Chimpoesh
A wannan lokacin, wani ɗan’uwa mai suna Nikolai Chimpoesh daga ƙasar Moldova ya zama mai kula da da’ira kuma ya yi kusan shekara 30 yana wannan hidimar. Nikolai ya ziyarci ikilisiyoyi kuma ya tsara yadda za a riƙa buga da kuma rarraba littattafanmu. Gwamnati ta saka wa ayyukan da yake yi ido. Saboda haka, Ɗan’uwa Eduard Varter ya ba Nikolai shawara cewa: “Idan hukumomi suka tuhume ka, ka kalle su kuma ka gaya musu cewa daga hedkwatarmu da ke Brooklyn ne ake turo mana littattafai. Kada ka ji tsoro.”—Mat. 10:19.
Ba da daɗewa ba bayan wannan tattaunawar da Eduard Varter da Nikolai suka yi, sai aka kai Ɗan’uwa Nikolai zuwa hedkwatar ’yan sandan ciki, wato KGB a garin Kant. Nikolai ya faɗi abin da ya faru cewa: “Ɗan sandan ya tambaye ni wurin da muke samun littattafanmu, sai na gaya masa ana turo mana su daga hedkwatarmu. Bai san abin da zai faɗa ba. Sai ya ce in tafi kuma bai sake kira na ba.” Irin waɗannan Shaidu masu gaba gaɗi sun ci gaba da wa’azi a yanki da ke kusa da garinmu a arewacin Kyrgyzstan. A iyalinmu, matata Mairambubu ce ta fara jin wa’azi game da Jehobah a shekara ta 1981.
MATATA TA KOYI GASKIYA NAN DA NAN
Matata ’yar yankin Naryn ce a ƙasar Kyrgyzstan. Wata rana, ta ziyarci ƙanwata a watan Agusta na 1974. A wurin ne na fara ganinta, kuma na so ta nan da nan. Sai muka yi aure a ranar.
Apun Mambetsadykova
A watan Janairu na 1981 sa’ad da matata take cikin bas zuwa kasuwa, sai ta ji tattaunawa da aka ambata ɗazu. Tana son ƙarin bayani, kuma ta tambayi matar sunanta da adireshinta. Matar ta gaya wa matata cewa sunanta Apun. Amma ta yi hakan da dabara domin an hana Shaidun Jehobah yin aikinsu a tsakanin 1980 zuwa 1989. Apun ta karɓi adireshin matata maimakon ta ba da adireshinta. Kuma matata ta dawo gida tana farin ciki.
Ta ce: “Na ji abubuwa masu ban mamaki a yau. Wata mata ta gaya mini cewa nan ba da daɗewa ba, mutane ba za su ƙara mutuwa ba. Dabobbin daji ma za su yi zaman lafiya da mutane.” A wurina, wannan tatsuniya ce. Sai na ce, “To, bari mu jira har sai ta zo ta ba mu ƙarin bayani.”
’Yar’uwa Apun ta zo gidanmu bayan wata uku. Bayan hakan, wasu ’yan’uwa mata suka ci gaba da ziyartar mu kuma muka haɗu da wasu ʼyan Kyrgyzstan da suka fara zama Shaidun Jehobah. Waɗannan ’yan’uwa mata sun koya mana game da Jehobah da kuma nufinsa don ’yan Adam. Ƙari ga haka, suka karanta mana littafin nan From Paradise Lost to Paradise Regained.a Kuma tun da yake littafin guda ɗaya ne kawai ke garin Tokmok, sai muka kofe shi da kanmu.
Annabcin da ke cikin Farawa 3:15 yana cikin abubuwan da muka fara koya. An koya mana cewa Yesu Almasihu ne zai cika wannan annabcin. Kuma wannan saƙo ne mai muhimmanci da ya kamata kowa ya ji. Hakan dalili ne da ya sa ya kamata mu soma wa’azi. (Mat. 24:14) Ba da daɗewa ba, abin da muke koya ya soma gyara rayuwarmu.
YIN TARO DA BAFTISMA A LOKACIN DA AKA MANA TAKUNKUMI
Wani ɗan’uwa a garin Tokmok ya gayyace mu bikin aure. Kuma ni da matata mun lura cewa yadda Shaidu suke yin abubuwa ya bambanta. Domin ba a ba da giya a bikin ba kuma an tsara shi da kyau. Hakan ya yi dabam da bikin auren da muka saba zuwa, domin mutane sukan sha su bugu. Ban da haka ma, sukan nuna halin rashin ɗa’a kuma suna maganganun banza.
Mun halarci wasu taro a ikilisiyar da ke Tokmok, kuma ana yin taron a waje idan ba a sanyi sosai ko kuma ruwa. ’Yan’uwan sun san cewa ’yan sanda suna saka mana ido. Saboda haka, sukan sa wasu ’yan’uwa maza su yi gadi. Kuma muna yin taro a gida wani ɗan’uwa a lokacin sanyi. A wasu lokuta, ’yan sanda sukan zo gidan kuma su tambaye mu abin da muke yi. Don haka, mun yi hattara sosai a lokacin da ni da matata muka yi baftisma a watan Yuli na 1982 a Ƙogin Chüy. (Mat. 10:16) ’Yan’uwa ba su zo a jere ba kuma mun haɗu a jeji, sai muka rera waƙar Mulki kuma muka saurari jawabin baftisma.
MUN YI AMFANI DA ZARAFIN DA MUKA SAMU DON YIN WA’AZI
A shekara ta 1987, wani ɗan’uwa ya ce in ziyarci wani mutum da ke son saƙonmu a garin Balykchy. Za mu yi tafiya na awa huɗu a jirgin ƙasa kafin mu kai garin. Bayan mu je wa’azi sau da yawa a Balykchy, sai muka lura cewa mutanen suna son jin wa’azi. Wannan zarafi ne na yin ƙwazo a hidima.
Sau da yawa, ni da matata muna zuwa garin Balykchy. Mukan je wurin a ƙarshen mako kuma mu yi wa’azi da taro. Mutane suna son littattafanmu sosai. Saboda haka, muna saka littattafai cikin buhun dankali. Bayan haka, sai mu kai shi garin Balykchy. Sau da yawa muna gama rarraba buhuna biyu kafin wata ɗaya ya ƙare kuma mukan yi wa fasinjoji wa’azi a cikin jirgi daga Tokmok zuwa Balykchy.
An kafa ikilisiya a garin Balykchy a shekara ta 1995, bayan shekara takwas da muka fara ziyartar wurin. Kuɗin mota daga Tokmok zuwa Balykchy yana da tsada sosai a wannan lokacin. Amma, mene ne ya taimaka mana ko da yake mu talakawa ne? Wani ɗan’uwa yakan ba mu kuɗin mota a kai a kai don mu haɗa da namu. Jehobah ya ga cewa muna son mu yi wa’azi sosai kuma ya ‘buɗe mana sakatan sama.’ (Mal. 3:10) Hakika, babu abin da ya gagari Jehobah.
MUN SHAGALA DA RENON YARA DA KUMA YIN WA’AZI
Na zama dattijo a shekara ta 1992, kuma ni ne ɗan Kyrgyzstan na fari da ya zama dattijo. Ƙari ga haka, an soma samun fannonin dabam-dabam na yin hidima a ikilisiyarmu da ke Tokmok. Mun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ɗalibai da yawa da ke manyan makarantu. Ɗaya daga cikin waɗannan ɗaliban yanzu memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Shaidun Jehobah ne. Kuma biyu suna hidimar majagaba na musamman. Har ila, mun yi iya ƙoƙarinmu mu taimaka ma wasu a taronmu. A tsakanin 1990 zuwa 1993, ana wallafa littattafanmu a Rashanci kuma muna taro a yaren. Amma, ’yan’uwa da yawa a ikilisiyar suna Kyrgyzanci. Saboda haka, nakan yi fassara idan ana taro, kuma hakan ya taimaka musu su fahimci abin da ake koyarwa.
Ni da matata da yaranmu takwas a 1989
Ni da matata mun shagala da kula da iyalinmu da ke ƙaruwa. Mukan fita wa’azi tare da yaranmu kuma mu halarci taro da su. ’Yarmu mai suna Gulsayra ’yar shekara 12 a lokacin takan ji daɗin yi wa mutane a kan titi wa’azi kuma ta gaya musu game da Littafi Mai Tsarki. Ban da haka, suna son haddace ayoyin Littafi Mai Tsarki. Ta yin hakan, yaranmu da jikokinmu daga baya suna saka hannu sosai a ayyukan ikilisiya. Kuma cikin yaranmu 9 da jikokinmu 11 da suke da rai, 16 suna bauta wa Jehobah ko kuma halartan taro da iyayensu.
CANJE-CANJE NA MUSAMMAN
’Yan’uwa da suka soma wa’azi a yankinmu a 1956 za su yi mamaki sosai idan suka ga ci gaba da aka samu yanzu. Kuma tun daga 1990, mun soma samun ’yancin yin wa’azi da kuma halartan manyan taro.
Ni da matata muna wa’azi
A shekara ta 1991, ni da matata mun halarci taro na farko a Alma-Ata da yanzu ake kira Almaty a ƙasar Kazakhstan. Kuma a 1993, ’yan’uwa a Kyrgyzstan sun yi taron yanki na farko a Filin Wasan Spartak da ke birnin Bishkek. ’Yan’uwa sun yi mako guda suna share wannan filin wasan kafin a yi taron. Hakan ya burge darektan wannan filin sosai har bai karɓi kuɗi daga hannun mu ba.
Mun cim ma wani abu na musamman a shekara ta 1994. A wannan lokacin ne aka fara buga littattafanmu a Kyrgyzanci. Yanzu wani rukunin mafassara a ofishinmu da ke Bishkek suna fassara littattafanmu a Kyrgyzanci. Ƙari ga haka, a 1998, gwamnati ta ba Shaidun Jehobah ’yanci yin aikinsu a Kyrgyzstan. Mun samu ƙaruwa sosai a ƙasar, don yanzu muna da adadin masu shela fiye da 5,000. Ban da haka, muna da ikilisiyoyi 83 da rukunoni guda 25 da suke Cainanci da Ingilishi da Kyrgyzanci da Rashanci da yaren kurame na Rasha da Turkiyanci da yaren Uighur da kuma Uzbekisanci. Dukan waɗannan ’yan’uwa daga wurare dabam-dabam suna bauta wa Jehobah da haɗin kai. Jehobah ne ya sa aka cim ma dukan waɗannan abubuwan.
Jehobah ma ya gyara rayuwata. Mu talakawa ne kuma shekara biyar kawai na yi makaranta. Duk da haka, da taimakon Jehobah, na zama dattijo kuma na taimaka ma mutane da dama da suka fi ni ilimi su san Jehobah. Hakika, babu abin da ya gagari Jehobah. Abin da na shaida a rayuwa ya sa na ci gaba da wa’azi game da Jehobah, domin a wurinsa ‘dukan abu zai yiwu.’—Mat. 19:26.
a Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi, amma an daina buga shi.