Abin da Ke Ciki
MAKON 31 GA DISAMBA, 2018–6 GA JANAIRU, 2019
3 “Ka Sayi Gaskiya, Kada Ka Sayar” da Ita
MAKON 7-13 GA JANAIRU, 2019
8 Zan “Yi Tafiya Cikin” Gaskiyarka
Waɗannan talifofi biyu sun ƙarfafa mu mu nuna godiya don gaskiyar da Jehobah ya koya mana. Wannan gaskiyar da muka koya ta fi sadaukarwar da muka yi daraja. Talifofin sun kuma bayyana matakan da za mu ɗauka don mu ci gaba da daraja gaskiyar da Jehobah ya koya mana kuma kada mu sayar da ita.
MAKON 14-20 GA JANAIRU, 2019
13 Ka Dogara ga Jehobah Don Ka Rayu!
Littafin Habakkuk ya nuna yadda za mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah a lokacin da muke fuskantar matsaloli. Wannan talifin zai taimaka mana mu ga cewa ko da matsaloli da jarrabawar da muke fama da su sun ƙaru, Jehobah zai taimaka mana idan mun dogara gare shi.
MAKON 21-27 GA JANAIRU, 2019
18 Wane ne Yake Sarrafa Tunaninka?
MAKON 28 GA JANAIRU, 2019–3 GA FABRAIRU, 2019
23 Kana da Irin Ra’ayin Jehobah Kuwa?
Yayin da muke kusantar Jehobah, za mu fahimci cewa ra’ayinsa ya fi namu muhimmanci. Waɗannan talifofi biyu sun bayyana yadda za mu guji barin duniyar nan ta sarrafa tunaninmu da kuma yadda za mu riƙa bin ra’ayin Jehobah.
28 Nasiha—Halin da Muke Nunawa ta Furuci da Ayyuka