Ku Koyar da Yaranku Su Zama Masu Hidima
1. Mene ne Zabura 148:12, 13 ya tilasta wa matasa Kiristoci su yi?
1 Jehobah ya gayyaci matasa su yabe shi. (Zab. 148:12, 13) Saboda haka, ba gaskiyar Littafi Mai Tsarki da kuma dokokin Allah na ɗabi’a ba ne kawai ya kamata iyaye Kiristoci su koya wa yaransu. Suna kuma koyar da su su zama masu hidima ta bishara. Ta yaya za a iya yin hakan kuma a samu ci gaba?
2. Ta yaya misali mai kyau na mahaifi zai iya shafi yaransa?
2 Misali Mai Kyau: Alƙali Gidiyon ya gaya wa mutanensa 300: ‘Ku dube ni.’ (Alƙa. 7:17) Yara suna lura da kuma yin koyi da iyayensu. Wani mahaifi yana yin aikin dare, amma maimakon ya je ya yi barci sa’ad da ya dawo gida ranar Asabar da safe, sai ya fita hidima tare da yaransa ko da yake ya gaji sosai. Ba tare da faɗin kome ba, yana koya musu cewa hidima ta fi muhimmanci. (Mat. 6:33) Shin yaranku suna lura cewa kuna farin cikin saka hannu a fannoni dabam dabam na bauta, kamar su, yin addu’a, karatun Littafi Mai Tsarki, yin kalami, da kuma wa’azi? Hakika, ba za ku zama kamiltaccen misali ba. Amma yaranku za su fi bin ƙoƙarce-ƙoƙarcenku na koya musu su bauta wa Jehobah idan sun ga cewa kuna da ƙwazo wajen bauta masa.—K. Sha 6:6, 7; Rom. 2:21, 22.
3. Waɗanne maƙasudai na ruhaniya da ake samun ci gaba ya kamata iyaye su taimaka wa yaransu su kafa kuma su cim ma?
3 Maƙasudai Masu Sa a Samu Ci Gaba: Iyaye ba sa gajiya wajen koya wa yaransu su yi tafiya, su yi magana, su sa tufafi, da sauransu. Yayin da yara suka cim ma abubuwa masu muhimmanci sa’ad da suke girma, suna kasancewa da sababbin maƙasudai. Idan iyayen Kiristoci ne, za su kuma taimaka wa yaransu su kafa da kuma cim ma maƙasudai na ruhaniya daidai da shekarunsu da kuma iyawarsu. (1 Kor. 9:26) Kuna koya wa yaranku su yi kalami a nasu kalmomi kuma su shirya aikinsu a Makarantar Hidima ta Allah? (Zab. 35:18) Kuna koya musu su sa hannu a fannoni dabam dabam na hidima? Kuna kafa musu maƙasudin yin baftisma da kuma yin hidima ta cikakken lokaci? Kuna taimaka musu su yi cuɗanya da masu hidima da ƙwazo da za su ƙarfafa su?—Mis. 13:20.
4. Ta yaya yara masu iyaye da suka soma koyar da su a hidima tun suna ƙanana suke amfana?
4 Marubucin wannan zaburar ya ce: “Ya Allah, tun ina yaro kā koya mani; Har wa yau fa ina bayyana ayyukanka masu-ban al’ajibi.” (Zab. 71:17) Ku soma koyar da yaranku tun suna ƙanana su zama masu hidima. Babu shakka tushe na ruhaniya da kuka taimaka musu su kafa zai amfane su sa’ad da suka zama manya!—Mis. 22:6.