Tsarin Ayyuka na Makon 6 ga Fabrairu
MAKON 6 GA FABRAIRU
Waƙa ta 101 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafi na 131 zuwa 135 sakin layi na 18 (minti 25)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ishaya 47-51 (minti 10)
Na 1: Ishaya 51:1-11 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Ya Kamata Kiristoci Su Yi Amfani da Sunan Allah—td 23A (minti 5)
Na 3: Me Ya Sa Allah na Ƙauna Zai Halaka Kowane Ɗan Adam?—2 Tas.1:6-9 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 36
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Me Ya Kamata na Sani Game da Dandalin Yin Hira na Intane?—Sashe na 2. Jawabin da aka ɗauko daga Awake! na Agusta 2011, shafuffuka na 10-13 da Awake! na Fabrairu 2012, shafuffuka na 8-9. Ko kuma ku tattauna, Abubuwa Marasa Amfani da Ya Kamata Mu Guji. Jawabi daga Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 2010, shafuffuka na 21-22, sakin layi na 9-13.
Minti 10: Bukatun ikilisiya.
Minti 10: Yadda Za a Gabatar da Mujallu a Watan Fabrairu. Tattaunawa. Ka yi amfani da minti ɗaya ko biyu don bayyana wasu cikin talifofi da mutanen da ke yankinku za su so. Ta wajen yin amfani da bangon Hasumiyar Tsaro, ka sa masu sauraro su faɗi tambaya da za su yi da za ta jawo hankalin mutane da kuma nassin da za su karanta. Ka yi hakan da bangon Awake! kuma idan da lokaci ka yi amfani da wani talifi da ke cikin Hasumiyar Tsaro ko kuma Awake! Ka sa a gwada yadda za a ba da kowanne cikinsu.
Waƙa ta 96 da Addu’a