1-7 GA SATUMBA
KARIN MAGANA 29
Waƙa ta 28 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Ku Guji Koyarwa da Alꞌadu da Jehobah Ba Ya So
(minti 10)
Ku yi wa Jehobah biyayya don ku yi farin ciki a rayuwa (K. Ma 29:18; wp16.6 6, akwati)
Ku roƙi Jehobah ya ba ku hikima don ku san alꞌadun da ba su da kyau (K. Ma 29:3a; w19.04 17 sakin layi na 13)
Kada ku bar mutane su matsa muku ku bi alꞌadun da Jehobah ba ya so (K. Ma 29:25; w18.11 11 sakin layi na 12)
Yin bincike da tattaunawa da kyau zai taimake ka ka shawo kan matsin bin alꞌadun da Allah ba ya so
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
K. Ma 29:5—Mene ne zaƙin baki yake nufi, kuma ta yaya ‘wanda yake yi wa maƙwabcinsa zaƙin baki yake shimfiɗa wa ƙafarsa tarko’? (it-E “Flattery” sakin layi na 1)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) K. Ma 29:1-18 (th darasi na 5)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 3) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka gayyaci mutumin zuwa jawabi na musamman da za a yi. (lmd darasi na 2 batu na 3)
5. Fara Magana da Mutane
(minti 4) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka yi amfani da Hasumiyar Tsaro Na 1, 2025 wajen fara tattaunawa da mutumin. Idan mutumin ba ya marmarin batun da ka shirya tattaunawa da shi, ka canja zuwa batun da yake so. (lmd darasi na 3 batu na 3)
6. Fara Magana da Mutane
(minti 5) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka ba wani mutumin da ba ya jin daɗin yadda ake yaƙe-yaƙe Hasumiyar Tsaro Na 1, 2025. (lmd darasi na 3 batu na 4)
Waƙa ta 159
7. Bukatun Ikilisiya
(minti 15)
8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) lfb gabatarwar sashe na 4 da darasi na 14-15