8-14 GA SATUMBA
KARIN MAGANA 30
Waƙa ta 136 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. “Kada Ka Ba Ni Talauci Ko Dukiya”
(minti 10)
Za mu yi farin ciki na gaske idan muka dogara ga Jehobah, ba ga dukiya ba (K. Ma 30:8, 9; w18.01 24-25 sakin layi na 10-12)
Mai hadama ba ya gamsuwa (K. Ma 30:15, 16; w17.05 25 sakin layi na 15-17)
Ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka maka kada ka riƙa cin bashi ko ka riƙa shiga damuwa (K. Ma 30:24, 25; w11 7/1 10 sakin layi na 4)
ABIN DA ZA A IYA YI A IBADA TA IYALI: Ku tattauna raꞌayinku game da kuɗi a matsayin iyali.—w24.06 13 sakin layi na 18.
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
K. Ma 30:26—Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga dabbar nan, Rema? (w09 4/15 17 sakin layi na 11-13)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) K. Ma 30:1-14 (th darasi na 2)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 4) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka yi amfani da Hasumiyar Tsaro Na 1, 2025 wajen fara tattaunawa da mutumin. (lmd darasi na 1 batu na 3)
5. Komawa Ziyara
(minti 4) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. (lmd darasi na 9 batu na 3)
6. Ka Bayyana Imaninka
(minti 4) Jawabi. ijwbq talifi na 102—Jigo: Shin, Yin Caca Zunubi Ne? (th darasi na 7)
Waƙa ta 80
7. Kada Ku Bari A Rude Ku da Salama da Ba Ta Gaske Ba!—Chibisa Selemani
(minti 5) Tattaunawa.
Ku kalli BIDIYON. Sai ka tambayi masu sauraro:
Mene ne kuka koya daga labarin Ɗanꞌuwa Selemani game da tsai da shawarwari da za su taimaka muku ku sami gamsuwa da farin ciki?
8. Abubuwan da Ƙungiyarmu Ta Cim Ma na watan Satumba
(minti 10) Ku kalli BIDIYON.
9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) lfb darasi na 16-17