Ta Nazari
NUWAMBA 2023
TALIFOFIN NAZARI NA: 8 GA JANAIRU–4 GA FABRAIRU, 2024
© 2023 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
Wannan mujallar ba ta sayarwa ba ce. Sashe ce ta aikin ilimantarwa na Littafi Mai Tsarki a dukan duniya wadda ake tallafa wa da gudummawar da aka ba da da son rai. Don ba da gudummawa, ka shiga donate.jw.org.
An ɗauko Nassosin da aka yi amfani da su a nan ne daga Littafi Mai Tsarki: Juyi Mai Fitar da Maꞌana. A duk inda aka yi amfani da wani juyi dabam, za a ambata hakan a cikin talifin.
HOTON DA KE SHAFIN FARKO:
Ezra yana yin adduꞌa yana kuka a haikali don zunuban mutanen. Jamaꞌar ma suna kuka. Sai Shekaniya ya zo yana taꞌazantar da Ezra, yana cewa: “Akwai sauran sa zuciya domin Israꞌila. . . . Mu kuwa muna goyan bayanka.”—Ezra 10:2, 4 (Ka duba talifin nazari na 48, sakin layi na 17)